Sashe 31
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe biyu da rabi na samu na kammala komai har da gyaran gidan, da kuma wanka, a lokacin ne kuma na samu na yi azhur, zuwa lokacin kam na gaji likis, kamar wacce aka yi wa duka, abincin ma ji nake kamar in ci daga kwance.
Haka nan dai na daure na mike zuwa falon bayan na zira doguwar riga mara nauyi, kicibus muka yi da Bashir yana shigowa
"Ɗangurguna!" na yi maganar cikin tsokana
Shi ma cikin tsokanar ya ce "Matar Ɗangurgu, kina fushi ne in zo in sauke miki shi"
Cikin dariya na ce" a'a ba na yi"
"Amma kin yi kyau ai, bari in zo in biya kudin kwalliya"
"Ai ban yi kwalliyar ba ma, bare ka biya kudinta"
"Guduna fa kike yi Khadija" cikin alamun mamaki ya yi maganar
"Ba dole ba"
Duk muka yi dariya, lokaci daya kuma Ina ajiye mishi abincin da na zuba a gaban shi.
Sai da ya fara ci sannan ya ce "Rahma fa za ta kawo miki kayanki ne, saboda wadanda suka sayi gidan suna son shiga"
Shiru na yi, yayin da fuskata ta canja alamun rashin jin dadi. Kila ya lura da hakan ne shi ya sa ya ce "Ki yi addu'a, Sha Allah za a samu sama da shi"
"Allah Ya amince"
"Amin" ya amsa, ni kuma na ce "Kana nan dai ba za ka canja ba, yanzu ace kayan nawa za a kwaso daga Abuja zuwa nan shi ne ba za ka fada min ba. Sai bayan da suka shigo hanya, Allah Ya kyauta"
"Amin" ya kuma amsawa, kafin ya ce
"Ke ma kina nan, ba za ki yi canja komai sai kin yi korafi"
Murmushi na yi ina ci gaba da cin alaleta, Rahma ba ta iso ba sai 5pm,ba sai an tambayi gajiya ba kam, ta gaji kam, ta yi likis kamar fulawar bredi, ni kaina naga kokarinta
Isowarta ba da jimawa ba, su Khalil suka dawo, take gidan ya rude da ihun da ganinta, suna tambayarta su Farhan. Bayan sun natsa ne ta ce "Yaran nan sun yi girma sosai wlh, ko don ba na ganinsu"
"Ba mamaki, ni dai nan yadda na sansu haka nake ganinsu"
"Gaskiya sun yi girma, tun ba Khalil ba"
"Sai dai rashin ji ai" na fada ina dariya
"To ai shi ne ke sanya su girman."
Duk mu ka yi dariya.
Sai da suka dawo sallahr isha'i sannan suka ci abinci, bayan nan na karbi haddarsu, daga nan kuma na ce aje a kwanta saboda gobe.
Bayan tafiyarsu ne Rahma ta ce "Ma Sha Allah! Da alama makarantarsu Khalil ana karatu, kin ga Affan yadda ya dage, da kuwa ba ya son Islamiya"
"Gaskiya babu laifi, ana karatu, kin ga da shigarsu makarantar dai ina jin sun hada hizif biyar"
"Gaskiya kam akwai karatu, duka yaushe aka fara karatun"
"Ba jimawa kam, tun da har sun fara 2nd C.A"
Zamanta ta gyara sosai kafin ta ce "Allah Ya saka miki da mafificin alkairi Khadija, kin rike amanar yaran nan, Allah Ya biya ki da gidan aljanna, ya kuma jikan kawata"
"Amin" na amsa kafin na ce "Ni Sakeena ba ta yi min komai ba sai alkairi wlh, idan ma ta yi min ban sani ba na yafe mata. Kishiya irin Sakeena abun so ce ga ko wace mace. Har gobe ina jin kewarta, bayan mahaifina ita ce ta biyu da zan iya cewa a dawo min da ita duniya da ana yin hakan. Mutuniyar kirki ce. Koda ba na tare da Bashir, to tabbas zan yi wa su Khalil abun da uwa ke yi wa ƴaƴanta. Ina sonsu, ba son ganin ido ba"
Numfashi ta sauke a hankali kafin ta ce "Tabbas Sakeena mutum ce har da rabi, kawata ce but she's like sister to me, tana yi min abin yan'uwana ba su yi min. Har in mutu ba zan sake kawa kamar Sakeena ba."
"Gulma ta kuke yi ko?"
Duk muka juya kan kofar shigowa falo muna murmushi, shi ma ya karasa shigowa yana fadin "Ai halinku ne mata, da kun ci kun koshi, Sai ku fara gulma mazajenku"
A tare mu ka yi dariya da Rahma, kafin suka shiga gaisawa yana yi mata sannu da hanya, saboda lokacin da ta iso yana Batsari.
Bayan na ba shi abinci na basu wuri, saboda yanzu a wajen shawara Rahma ita ta haye kujerar Maman Khalil, idan ba ita ba mijinta, Sai ko Inna. Abin da na fahimta bayanin kayan Sakeena take yi mishi, ashe gidansu Sakeenar aka kai kayan, shi ya ce ba ya son ganin komai hankalinshi tashi zai yi
Sai wajen 10pm sannan Ja'afar kanen Sakeena ya zo ya dauke ta zuwa gidansu Sakeenar.
Washegari sai wajen goma ta leko, muka gaisa sama-sama sannan ta wuce family house nasu Bashir. Ni kuma ta turo min yan matan gidan, suka muka shiga gyaran gida, saboda kayan dakina nake son mayarwa na gaji da zama daki babu kujeru, Sai kwanciya a kan katifa
Ranar kam ba karamin aiki muka sha ba, komai bai koma normal ba sai wajen karfe biyar na yamma, amma fa sosai part din nawa ya yi kyau, shi kanshi Bashir da ya shigo sai cewa ya yi "Lallai gyara shi ne gida."
Kowa ya zo kam sai ya yi sha'awa ya yaba, amma fa ranar hadda da homework din su Khalil Sai dai Babansu ya yi musu. Ni kam ina idar da sallahr isha'i sai bacci. Ko Rahma ta dawo gidan ma ban sani ba.
Misalin karfe biyu na dare wani matsanancin ciwon mara ya tashe ni, tun ina jin abun da wasa, har na kasa jurewa na tashi Bashir, daga ni har shi ba mu kawo haihuwa ba, ni na fi ganinta a irin juyin nan da ake cewa.
Zuwa karfe hudu kam na jigata, ga wani ruwa da yake zubo min. Yau ne na tantance haihuwa, saboda haihuwar fari ban san ya aka yi na yi ta ba, Sai dai na farka na ganni da Baby. Amma yau kam na gane Allah da girma yake.
Ban san ya aka yi ba, ni dai na ji murya Aunty Habi da Yaya Murja suna yi min sannu. Lokaci daya kuma suka kama ni zuwa waje. Ban san waye yake tukin ba. Ba na iya tantance komai sai azabar ciwa.
Ana dora ni saman gado yaro na fadowa, Sai a lokacin ne na ji lummm, jikina ya mutu lubus, sama-sama nake jin su Aunty Habi da nurse din suna cewa yaron bakwaini ne. Oho ni dai idan ma shidaini ne tun da ya fito sai a yi min barka. Ban san haka haihuwa take ba sai yau, azaba, iya azaba wayyo Allahna. Kai Allah Ya jikan iyaye mata. Amma haihuwa kam ba ta da mahadi a duk ciwurwukan duniya. Ita kadai ce.
Idan ka dauke rashin karfin jiki ba na jin komai, zuwa 5:30am an, gyare min jikina fes, taro kuma yana wani dakin daban a cikin wata kwalba.
6am asibiti ya fara cika da mutane, kun san kauye da kara, duk da babu tafiyar kirki tsakanin Batsari da Ruman amma yadda suke zuwa tawaga-tawaga yana ba ni mamaki.
Rahma ma da ta zo mamaki ta yi sosai na jin wai na haihu, a kai ta cewa aikin da na yi jiya ne. Daga asibitin Rahma ta wuce. Mu kam zaman asibiti ai sai ya kama mu, saboda yaron, ni dai lafiyata ƙalau. Yaron ne dai kam dan firit, don ma yana samun kulawar likitoci, amma wani lokacin idan na zo na ba shi nono, Sai in ga kamar ba zan sake dawowa in same shi da rai ba. Ba ni kadai ba, duk wanda ya samu damar ganinshi sai ya yi jimamin anya kuwa zai rayu. A haka dai aka yi mishi huduba da Abubakar Siddiq, muna kiranshi da Assidiq. Samira da Badiyya duk sun zo duba ni, haka ƴan'uwana mota biyu suka yi, da kayan gararsu, bayan an sauke kayan garar kuma suka nufo asibiti. To ai babu maganar taron suna.
Iyayen Sakeenar ba a bar su a baya ba, saboda duk abin uwa ke wa Ƴa shi Mahaifiyar Sakeena ke yi min, haka ma mahaifinta, ni ma ina kyautata musu da abin da nake da.
Wasa-wasa sai da mu ka yi sati biyar a asibiti sannan aka sallame mu, zuwa lokacin babu laifi ya yi girma, kuma siffarshi ta koma ta cikakke jariri, abin da duk ba mu yi zato ba.
A karo na uku Saratu ta zo duba ni a gida, saboda zuwanta biyu muna asibiti, yanzu kuma da muka dawo gida sai ga ta har da kayan jarirai masu kyau babu laifi.
Bayan ta tafi ne na kalli Shafa'atu tare da fadin "Wai wacece wannan? Ya kuke da ita?"
Wata irin dariya Shafa'atu ta yi kafin ta ce "Ni ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba"
Jamila da Lawisa suka yi dariya irin shakiyancin nan, yayin da ni kuma na ci gaba da magiya a kan su fada min wacece ita. Fir suka ƙi faɗa min, amma the way yadda seke manna min hauka, jikina bai ba ni ba, shi ya sa na aje mata bayar tambaya, na kuma kudiri niyyar canja mata, hade da taka mata burki a kan zuwa gidana.
Duk da na yi hutun makaranta, to su fa su Khalil suna zuwa, Sai dai yanzu suna tafiya karfe biyu ne a tashi shidda, sabanin baya da suke tafiya tun safe.
Kuma yanzu haka suna hutun 2nd term ne, kenan term daya ya rage musu su tafi js1. Bangaren karatun Kur'ani kam, suna da wajen hizif arba'in. Fatan da nike yi su sauke kafin su gama makarantar, ko basu yi hadda ba, hakan ma ya wadatar.
Misalin karfe takwas na dare Abban Khalil ya shigo, kamar kullum "Ina yaran nan?" shi ne abin da ya fara tambaya
"Suna cikin gida" na ba shi amsa, saboda yanzu tun da suka ga Maama na can kuma an yi hutu, su ma sai suka tare a can din.
Sai da na bari ya gama cin abinci, muna ta hira, sannan na sako abin ds ke damuna "Wai Abbansu Khalil wacece Saratu?"
"Me ya faru?" ya tambaye ni, cikin rashin ba wa zancen nawa muhimmanci.