Sashe 21
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Natsu Khadija! Ki natsu don Allah, rika ambaton Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un. Dukkanmu bamu isa mu ja da hukunci ubangiji ba. Allah ya bukaci abunsa, kuma sun karɓa kiransa,ki yi hakuri don Allah, mun san akwai damuwa da tashin hankali amma ki yi hakuri."kallonta nake yi ina tsiyayar da hawaye, ba zan ce ban fahimci abin da take fada ba. Amma na kasa gasgatawa.
Shigowar Ummata ne ya sanya ni rushewa da kuka mai sauti hade da kwacewa daga hannun yaya Habi zuwa wajen mahaifiyata, ita ma sai ta rungumeni tana kuka da alama zuwanta kenan ma, sai daki da falon ya kuma cika da koke-koke.
"Umma wai da gaske su Baban Khalil duk sun rasu? Don Allah ki ce min ba gaskiya ba ne, duka yaushe muka gama waya dasu, har yana fada min me zai sawo min sun kusa shigowa Abuja, amma to yaushe ya rasu?"
Umma ba ta ba ni amsa ba, wani kukan ta kuma fashewa da shi, wata Auntyn su Baban Khalil ce ta janyeni hade da yin waje da ni, can baya ta kai ni, mara yalwar jama'a.
Bayan mun tsaya ne har a lokacin kuka nake yi sosai.
" Ce Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un Khadija"
Na dade ban furta ba saboda kukan da ya ci karfina, da kyar na fada "Innalillahi.... Wa'inna.... Ilaihir.... Raji'unnn"
"Ci gaba da fada."
Ba musu kuwa na ci gaba da fada, tun muryata na yayyankewa har na fara fada daidai.
Har sai da ta gamsu natsuwata ta dan daidaita sannan ta dafa kafaduna ta ce
"Khadija ki yi hakuri, mutuwa a kan kowa take, idan ta zo ba tsumi ba dabara sai an tafi, akwai zafi da ciwo mun sani, amma ki yi hakuri don Allah, addu'a za ki rika yi masu."
Kallonta nake yi, hawaye masu dumi na bin kuncina.
"Yanzu suna ina?"
"Khadija an kai su gidansu na gaskiya tun jiya."
Ido na zuba mata kafin in ce "Cikin daren aka kai su? To ni ina na je, da ba za a kirani in gansu ba?"
"Ki yi hakuri yau kwana biyu da rasuwarsu ai, ke kuma kin riga kin shiga wani hali bai kamata a yi ta ajiyarsu ba."
Kenan idan na fahimceta kwana na biyu ban san inda kaina yake ba
"Kenan har da Bashir, shi ma ganin karshe na yi mishi. Wayyo Allahna ni Khadija." cikin sabon kuka na furta mata maganar
Jikinta ta janyo ni, muryarta ta yi rauni ta ce
"Yi hak'uri Basheer kam yana nan da ransa har yanzu yana dai bukatar addu'arki"
"Zo ki kai ni wurin shi " na yi maganar ne daidai ina tafiya ban damu da rashin takalmi da ke kafata ba.
Kafin ta ankara har na fara ratsawa cikin mazan da suka taru a harabar gidanmu tsallakasu kawai nake wasu kuma ina takasu, da katon cikina da na manta yana jikona
Rahma ce ta farkon wacce ta fara isowa wajena tana fadin
"Subhanallah! Ya akai aka bar ta ta fito?"
Ni kuwa kokarin kwacewa kawai nake daga rikon da ta yi min "Ni ki sake ni wajen mijina zan je, ki sake ni na ce."
Wajen mata biyar ne suka kama ni zuwa dakina.
Idona a bushe na kasa yin kukan ma, cewa nake kawai a kai ni in ga mijina.
Yadda na nace ne ya sa Rahma dole ta samo wanda zai kai ni babban asibitin Abuja inda Baban Khalil ke kwance, ni da yaya Habi da kuma kanwar Babana ne a motar.
Tun da muka shiga Kalamai masu laushi da kwantar da hankali suke fada min har zuwa lokacin da muka isa asibitin.
Kai tsaye dakin da yake kwance muka nufa, su Abdul ne kannensa a kofar dakin zaune.
Suna hangomu cikin sauri suka mike hade da tararmu.
"Ya mai jikin?" Aunty Habi ta fara tambaya
"Akwai sauki" Abdul ya fada cikin sanyin murya.
"Ya farka ne?" ta kuma tambaya, don ni kam yanzu idan akwai abun da ke mun wahala to magana ce.
" Eh ya farka."
"Ya yi magana?"
"Eh ya yi" wannan karon Hassan ne ya ba ta amsa.
A kuma daidai lokacin ne muka isa kofar dakin.
Kwance yake yayin da aka sanya mishi irin robar nan da take taimakawa wajen yin numfashi, kanshi nade da bandage, kafarsa ma akwai alamun gyaran karaya na asibiti.
Ido na zuba masa ina kallon yadda halittarsa ta canja lokaci daya, kamar ba shi ne mijina dan gayu mai son kwalliya ba, lallai dan Adam ba a bakin komai yake ba.
Fitowa na yi waje na zauna, har ga Allah na rasa kalar tunanin da zan yi.
Ni dai gani nan zaune kamar gunki, bayan mintuna talatin da fitowata sai ga sauran ma sun fito wai in tashi mu tafi.
Na kafe kam babu inda zan je ina nan, iya lallashinsu kin tafiya na yi, dole su ma suka hakura muka zauna tare.
Zaman makokin sai ya koma asibiti, saboda na ki tafiya gida.
Idan ka dauke ido babu wani abu a jikina da yake aikinsa yadda ya kamata, bana iya magana, idon ma ya bushe babu hawaye, zuciyata ba ta iya wani tunani mai zurfi.
Abinci ma sai surukata ta sani a gaba da Mamata sannan nake iya ci.
Yayin da Baban Khalil ke kwance kamar gawa.
Saboda komai sai an yi mishi.
Lokaci daya kuwa na zube, na yi baƙi, har da wasu kurajen tashin hankali suka fito min. idan ka dauke cikin jikina babu wani abu mai kauri.
Tsawon sati amma babu wani cigaba, kullum jiya iyau, har an fara tunanin fita da shi waje, da taimakon Rahma da kuma mijinta. Yanzu kam idan ka dauke ni, Inna (mahaifiyar Abban su Khalil,) Aunty Habi, Abdullahi, Hassan, Ni da kuma Maryam kanwata, to ba kowa. Sai Rahma da ba ta taba gajiyawa wajen kawo mana abinci ba. Su Affan ma duk suna wajen ta. Daga can ake kai su school a kuma dakko su.
Yau ma zaune muke a dakin, masu hira na yi, ni dai dama zan iya wuni ban yi magana ba, ni ban san ma me zan rika cewa ba. Abin da yake damuna kadai ya ishe ni. Wuni nake kuka, ga na kewar Maman Khalil, ga na rashin lafiyar mijina.
Ina lura da yadda Inna ta kafe ɗanta da ido tun bayan da suka shigo dakin.
Dalilin da ya sa kenan ni ma na mayar da hankalina a kanta, duk kuwa da kukan da nake yi.
Abdullah ta ja zuwa waje, jimawa kadan sai gasu da likita.
Maganar da likitan ya fada ba ƙaramin daga min hankali ta yi ba, sannan ta yi sanadiyyar yankewar duk wani network da yake jikina.
Saboda cewa ya yi, wai numfashi ya yi nisa da gangar jikin Basheer.
Kwance bisa gadon marasa lafiya na ganni bayan na farka.
A hankali kuma komai ya rika dawo min har zuwa furucin likitan, a hanzarce na yunkura da niyyar tashi.
Amma na ji an mayar da ni, Aunty Habi ta ce
"Kwanta, jikinki akwai ciwo."
"Aunty Basheer fa." na yi saurin tambayarta ba tare da na koma na kwanta din ba.
"Aunty da gaske shi ma ya rasu?" na kuma tambayarta a karo na biyu.
"Kwanta na ce miki, Basheer yana nan bai rasu ba, doguwar suma ya yi."
Na dan lumshe ido cike da jin dadin abin da ta fada min. Koda ba gaskiya ba ne, tabbas na ji sanyi.
Sai a lokacin na ji zafi a kasan cikina.
"Me ye wannan?" na yi tambayar hade da shafa wajen.
"an yi miki aiki ne an cire abin da ke cikinki"
A lokacin ne na kuma na shafa cikina don gasgata abun da ta fada lokaci daya kuma ina tuno wata maganarmu da Maman Khalil.
Bacci nake yi sosai bayan na idar sallahr magriba, ban san ma ya daukeni ba, a cikin baccin na ji tana tashina.
Firgigit! Na bude ido hade da dorasu a kanta.
"Me ya faru?" na yi maganar cikin yanayin bacci hade da mikewa zaune
"Haihuwa kika yi." ta yi maganar cikin murmushin da baya bacewa a kan fuskarta.
Ni ma a lokacin murmushin na yi tare da fadin "Ace ko haka ake yi, ai da kila kullum mutum sai ya haihu."
Tare mu ka yi dariya kafin ta ce "Ke kam haka haihuwarki za ta kasance ba za ki san kin haihu ba. Sai dai a ba ki labarin haihuwa kika yi"
Har zuwa lokacin dariya nake yi, bayan da na karbi plate din da ke hannunta mai dauke da wainar Fulawa da yajin da ya sha garlic.
"na gode" na fada a daidai lokacin da da take ficewa.
Na share hawayen da suka gangaro kan fuskata, ban san ranar da zan daina kukan rabuwa da Maman Khalil ba, na yarda mutum ko namanka yake yanka, idan ka rasashi sai ka ji babu dadi. Barrantana ita da ko bakar magana ba ta taba shiga tsakaninmu ba.
"Sannu! Akwai ciwo ne?"
Aunty Habi ta tambaya hade da zuba min ido
Kai na girgiza alamar a'a sannan na ce "Ina son ganin Bashir Aunty ."
"To jira in je wurin Doctor tukun."
Fitarta ke da wuya sauran 'yan' uwa da ke waje suka rika shigowa suna min sannu, wasu kai kawai nake iya daga masu.
Nurse din da suka shigo da Aunty ne ta taimakeni na ta shi zaune, sannan ta dora min Babyn a kan cinyata hade da bude mata fuska, cikin murmushi take fadin "Ya kika ga Babynki, lafiyayya kuma kyakkyawa ga gashi tamkar ba'Indiya."
Na zubawa yarinyar ido ina kallonta, abin da duk nurse din ta fada gaskiya ne, amma zuciyata babu dadi sam da zan ji dadin kalamanta.
Hasalima hawaye ne suka gangaro kan kumatuna bayan na jingina kaina jikin bango.
Ramla nake tunawa, watarana tana danna cikina, na ce "Ke bari Baby ne a ciki"
Ta zuba min ido, kafin ta ce "Baby?"
"Eh." na amsa cikin murmushi.
Ba tare da ta dauke idanunta akan cikin ba, ta shiga murmusawa na san akwai maganganu sosai a bakinta amma ba hausar da za ta yi su, hakan ne ya sa na kara mata haske.