Sashe 22
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baby ne me kyau a ciki zan haifo miki, ki samu abokiyar wasa yadda su Affan ba zasu kara korarki ba idan kin je wurin wasansu."
Wangale baki ta yi sosai alamun ta ji dadi, a lokaci daya kuma ta kai hannu tana shafa cikin.
Ni ma fadada fara'ata na yi, hade da janyota zuwa jikina.
Tun daga wannan ranar ko me ta samo sai ta kawo min wai a ba Baby, ku kuma ta bude cikina ta dora abun wai Baby ta dauka.
Na so ace Ramla na raye na haihu, in ga wace irin murna za ta yi? Za Ta bari a dauki Babyn ko ba za ta bari ba?. Tun ina kukan a hankali, har na bude murya sosai na shiga rera shi.
Kowa a dakin hakuri yake ba ni da fada min magana mai dadi.
Da sauri na mayar da hankali kan Abbansu Khalil da aka turo cikin keken marasa lafiya.
Matar J ✍🏻
[12/22, 15:04] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 18*
Kasa janye idanuna na yi a kanshi, har zuwa lokacin da Abdullahi ya tsayar da kujerar a gaban gadona, yayin da mutanen cikin dakin suka shiga jero mishi sannu.
Bayan mutanen sun watse ne, ya zaro littafi ya yi rubutu hade da miko min.
Hawayen kan fuskata na dauke, hade da karbar littafin na shiga karanta abin da ya rubuta.
_"Bana iya magana Deejah sakamakon aikin da aka yi min a muka-muki, amma kuma na damu da sanin halin da kike ciki tun da aka ce kin haihu."_
Abun da ya rubuta kenan, ni ma sai na mayar mishi da amsa.
_"Ina lafiya Alhamdulillahi, amma na fi damuwa da halin da kake ciki Abban Khalil, yanzu me ye ya fi damuna? "_
_"Kafata ce ta fi damuna da alama yanketa za a yi, ban san ya rayuwa za ta juya min ba kuma."_
Ba tare da na share hawayen da ke diga a kan littafin ba na shiga ba shi amsa
_"a ko wane irin yanayi ina sonka Bashir, zan kuma ci gaba da sonka har karshen numfashina, bare ma sha Allah za ka warware, ni bukatata kawai shi ne ka rayu, koda babu kafa zan yi ma komai, zan kula da kai"_
Silent murmushi ya yi, a lokacin da ya karasa karatun, kafin ya yi rubutu ya miko min
_"Ya kika ga Babynki, kyakkyawa kamar Affan ko? "_
Bayan na karanta na dan yi gajeren murmushin da na manta ranar da na yi irinsa, na san ya canja salon hirar ne, dalilin da ya sa kenan na zuba ma yarinyar ido.
Gaske yake yi, tamkar Affan ne ya koma jariri yake kwance.
_"Basu yi kama ba, fuskar Ramla ce."_
Murmushi ya yi, lokaci daya kuma ya shiga ba ni amsa
_"Don ba ki san Affan yana yaro ba shi ya sa, amma da Maman Khalil na kusa abin da na fada na san ita ma shi za ta fada._
Shiru na dan yi bayan na karanta sakon, shirun da na rasa me ma na tuna.
_" Yanzu me suka ce game da kafar taka?"_
Ni ma na canja salon tawa hirar, ba na son abin da zai tayar mishi da hankali
_"Basu ce komai ba, kawai dai da an gyara ne, sai gyaran ya baci"_
_"Ko zamu gwada na gargajiya"_
Wannan karon dago fuskarsa kumburarra ya yi yana kallona.
Yayin da ni ma na zuba mishi ido cike da tausayawa, ya yi baki, ya rame, fuskarsa ba sajen nan da yake shan gyara duk an askeshi, haka ma gashin kansa.
Kuma a yanzu ne na fahimci karfin hali kawai yake yi, amma yana jin jiki.
"Bashir!" na kira sunanshi cikin sanyin murya, bayan na matso daf da shi, hade da kama hannunsa.
"Ina sonka a ko wane irin yanayi, fatana ka samu lafiya, don Allah ka rage damuwa, idan har kana son mu bar asibitin nan da wuri. Ba ni kawai ce ke bukatarka ba, hatta Sakeena da Ramla suna bukatarka a raye , saboda kullum za ka nuna kulawarka garesu ta hanyar yi masu addu'a."
Na dan tsagaita hade da kallonsa, shi ma ni yake kallo.
"Sannan ga su Khalil da Affan, su ma suna bukatarka, idan ka tafi maraici sai ya fi masu yawa."
Wannan karon hawayen da nake boyewa sai da suka samu damar gangarowa.
Hannu ya sanya yana share min hawayen, yayin da shi ma na shi hawayen ke sauka kamar ruwa.
Ban san ko tsawon mintuna nawa muka kwashe a haka ba, kuma a haka Aunty Habi ta shigo ta same mu, ita ce ke shaida min zuwan Yusrah kanwata. Kuma ita ce ta kira Abdullahi ya tura Abbansu Khalil zuwa dakinshi.
Zuwan Yusrah ba karamin kewa ya kara debe min ba, Idan tana yi min hirar ƴan'uwa da gida sai in rinka jin dadi sosai.
Haka rayuwarmu ta kasance a asibiti, kodai ni in tafi wajen Baban Khalil, ko shi a kawosa wajena.
Matsala daya shi ne baya iya magana, cikin sati littafai uku muka cika dam da magana, mun bude na hudu ne aka ba ni sallama.
Shi ma zuwa lokacin sosai akwai sauki, idan ka dauke rashin maganar da kuma kafarsa.
Amma ciwukan da ke jikinsa da yawansu sun warke.
Ranar da zan tafi gida, da kuka muka rabu, na so su bar ni har zuwa lokacin da za a cirewa Baban Khalil karfen da ke bakinsa, su bamu sallama tare, saboda za a koma Ruma da shi don yi mishi aikin gargajiya. Amma suka ki, wai suna bukatar gadon. Ban hak'ura ba, kullum sai na zo asibitin, saboda na fahimci yana jin dadin hakan.
Sannan Abdallah ya sawo waya ya ba shi, ni ma kuma wayata tana nan, Sai mu rika yin chat koda ban je asibitin ba. Kullum cikin lallabashi nake yi. Ba bukatar bayyana ya damu da rashin matarshi da kuma yarshi, ko bai bude baki ya fada ba ni na san yana jin zafi.
A tare da ni a gida akwai kanwar Abbansu Khalil budurwa mai suna Jamila, ni ma kuma akwai kanwata Maryam, saboda Yusrah kwananta uku ta koma gida. Sakamakon rashin lafiyar yarinyarta. Sai kuma Aunty Habi, wacce ke kula da ni sosai a bangaren jego.
Rahma kullum sai ta zo, kuma har zuwa lokacin ba ta maido yaran ba. Ni ma kuma ban yi maganarsu ba. makotana ma, suna dan yawan shigowa, ba kamar baya ba, don ban ma sansu sosai ba.
Gidan dai kullum sai an yi baki.
Amma kuma hakan bai debe min kewar Ramla da Sakeena ba, kullum cikin tunaninsu nake da tuna rayuwar da mu ka yi. Sai in ji kamar zan ji tashin motarta ta fita ko ta dawo. Idan na kalli motar lullube ba na sanin lokacin da hawaye ke zubo min.
Kamar mafarki Sakeena ta zo, ta kuma ta fi.
Ashe dama rayuwar zamanmu da ita ba mai tsawo ba ce.
To yanzu da ta zauna da ni da mugun hali, ta cutar da ni kamar yadda wasu ke yi wa abokan zamansu da shi kenan yanzu ta tafi ta girbi abun da ta shuka, tun da ko gafarata ba ta samu damar nema ba.
Ni ma ga shi ban nemi tata gafarar ba, kuma ba san na yi mata abubuwa marasa dadi.
Abu ma fi a'ala shi ne ka zama mutumin kirki sannan ka jira mutuwa, saboda a ko wane lokaci tana iya riskarka, ba ruwanta da kana aikata mai kyau ko akasinshi.
Shigowar Affan ce ta katse min tunanina
Na rika bin shi da kallo ina tuna mafarkin da na yi a kanshi. Abun ka da yara babu ruwansu, komai bai canja nasu ba
"Kai da wa kuka zo?"
Don na san idan ba ya canja ba, ko zamu shekara a haka, daga sallamar da ya yi da kuma gaishe ni ba zai kara komai a kai ba.
Kafin ma ya ban amsa Rahma ta shigo rike da manyan ledoji guda uku, Khalil na bin ta a baya.
Shi kam kan jikina ya fada cike da murnar ganina, rungume shi na yi tsam, lokaci daya kuma Ina ta kokawa da hawayen da ke son zubo min.
Kan stool din mirror Rahma tan zauna, lokacin daya kuma muna gaisawa.
"Affan ya dauki Babyn?"
Ta yi tambayar hade da kallona.
"Bai dauka ba, kin san halinsa ai ba ya magana."
"Kuma a can ya dame ni, in kai shi wurin Abbanshi da kuma Babynsu yana son ya dauketa."
Na dan yi murmushi, lokaci daya kuma ina kallon irin ramar da Rahma ta yi, lokaci daya ta zube, sai ta kara haske fayau, har ba kyau.
Samun kawa kamar Rahma a wannan lokacin abu ne mai wahala, tana da rikon amana.
Karbar yarinyar na yi a hannun Khalil ina fadin "to zo ka dauke ta "
Ba musu ya zauna aka dora masa ita, Rahma ta rika mishi hotuna, ni ma sai na rika daukarsa.
"Wadannan kayan Sakeena ce ta saya da hannayenta, ta bar su a wajena ta ce idan kin haihu sai in kawo mata ta ba ki. Dama jira nake abubuwa su yi sauki in kawo miki."
Ta karashe maganar hade da turo min ledojin.
Jiki a mace na rika budasu, latest kayan baby ne masu kyau da tsada, overrall, da unique sex masu kyau, sannan akwai na mata yankanti masu kyau sosai da takalma, zanen daukar baby da na goyo, socks, feeding bottles, pampers, maya-mayai na Baby, turare, kai tarkace ne cike leda biyu.
Dayar ledar kuma, less, atamfa, da kuma shadda ne masu kyau, sai ta kalmi gyale, turaren Wuta, na kaya da kuma na jiki.
Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, maimakon Rahma ta lallasheni ita ma sai ta fashe da kukan.
"Aunty kayan da Momy ta saya miki ne ba kya so?" cewar Khalil bayan ya dafa kafadata.
Girgiza kai na yi alamar a'a.
"Aunty wai Mamana da Ramla sun mutu?" cewar Affan yana kallona
Nan ma girgiza kan na kuma yi.
"To suna ina, Abbanmu ba shi da lafiya, amma su ban gansu ba?" ya kuma tambayata
"Suna Ruma" Na ba shi amsa hade da share hawayena
"Amma Aunty mutane sai cewa suke sun rasu, yanzu shi kenan ba mu da Mama." cewar Khalil yana kallona.