Sashe 32
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nothing, kawai ina son sanin yadda kuke ne, dazu ta kawo ma Assidiq kaya"
Ido ya waro alamun mamaki kafin ya ce "Da gaske, mu gan su"
Assidiq na ajiye saman kujera, hade da shiga dakin na dakko mishi kayan na kawo mishi.
Ya shiga budasu yana yabawa, har yabon ya fi kayan yawa. Wannan ya sa na tabbatar da abin da nake zargi. Don haka na ce "Yarinyar nan sonka take yi ko?" na tambaya kai tsaye
Maimakon ya amsa min sai ya yi dariya mai da sauti, hade da ajiye kayan a kan kujera.
Ku san halina da kishi, don haka take ya taso min na ce "ka mayar mata da kayanta ni ba na so. Sannan ka fada mata, wlh kar kafarta ta kara takowa gidan nan"
"Sannu maigida" ya yi maganar hankalinshi a kan kiran da yake shigowa wayarshi.
Yadda ya yi receiving called din ya fahimtar min da masu aikin gidanshi a Katsina yake magana, kuma da alama aiki ya yi nisa, na ji ana zancen fenti.
Bayan ya dire wayar ne ya ce "Ko kina da zabin kalar fentin da kike so?"
"Ba ni da shi" na amsa, duk da kuwa ina da zabin
"To shi kenan" ya mike hade da jan kafarshi zuwa bedroom, saboda yanzu yana iya tafiya ko ba crochet, amma fa da alama kafar ta tsaya a haka. Ba za ta taku ba, irin da.
Na gama cika da batsewa ta, na bi shi zuwa bedroom din, na kwanta hade da sanya Assidiq a tsakiyarmu, ina addu'ar Allah Ya sa kar ya ce zai taba ni, cikin ikon Allah kuma bai yi hakan ba.
Matar J ✍🏻
[12/22, 21:19] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 26*
Safiyar Monday 8am Bashir ya tashi daga bacci, abun da ya ba ni mamaki sosai musamman lokacin da na zo na same shirye tsab cikin manyan kaya.
Cike da mamaki na kalle shi, kamar zan yi magana sai kuma na fasa na ce "Dama zan kai Assidiq rigakafi ne?"
Hankalinshi a kan laptop din gabanshi ya ce "Break dina fa?"
"a kawo ma nan ne ko, a bar shi a dinning din?"
"Bar shi a can"
"Ok" na fada hade da juya da zummar fita
"Khadija!" ya kira sunana
Wannan ya sa na juyo duk da ban amsa ba
"Zan fara zuwa aiki yau"
"Ma Sha Allah! Wannan ai labari ne mai dadin ji. Allah Ya sa aje lafiya a kuma dawo lafiya, Ya kara ba ka lafiya"
"Amin Ya Rabbb, na gode sosai"
Komai ban ce ba, na kuma juyawa da zummar fita ya ce "Zo nan mana"
Ba musu na dawo baya, hade da tsayawa ina kallon shi.
Hannuna ya janyo har ya zaunar da ni kusa da shi kafin ya ce "Sarkin fushi. Menene kuma yanzu"
Na danne yadda nake ji na ce "babu komai, ba fushi nake yi ba"
"Na ji" ya fada lokaci daya kuma yana plying wani video. Na ranar sunan Ramla ne, Maman Khalil sanye cikin lace purple, ta yi mugun kyau, sosai sai murmushi take yi, hannunta rungume da Ramla, ya jima yana kallon videon kafin ya danna pause hade da sauke ajiyar zuciya ya ce "idan na tafi ina sai ranar Alhamis ko Friday"
Duk da na ji ba dadi amma ban nuna ba, na ce "Allah Ya kai mu"
"Amin."ya amsa
Jin bai kara cewa komai ya sanya ni mikewa" Ki duba kitchen din, idan akwai abin da kuke bukata let me know "
" Ok"na amsa shi. Kai tsaye kuma na fita zuwa kitchen din, zuciyata na min babu dadi, saboda na san ba yau ne aka shirya komawarshi aikin ba, yau dai din ne ni na sani.
Na dawo mishi da abubuwan da muke bukata a rubuce, bayan ya gama dubawa ya ce "Shi kenan Sagir zai kawo miki"
"To mun gode"
Daki na koma hade da karasa shirina na zuwa asibiti, na saba Assidiq sama kafadata, ina rufe kofar bedroom na ji fitowarshi.
Wannan ya sa muka hadu a falo, hannunshi rike da karamar jaka. Yadda yake shagida kafar sai na ga kamar jakar ta yi mishi nauyi, shi ya sa na mika hannu na karba ina fadin "Har ka yi break din"
"Kunun kawai na sha. Ya isa haka"
Tare muka jera har zuwa wurin da aka wanke mishi motarshi tas, ta fito kamar sabuwa,.
"Shiga sai in ajiye ki a asibitin"
A, hanya muke taba hira, a nan ne ma yake shaida min ya nemi transfer zuwa Katsina. Na yi mishi fatan alkairi.
A kofar asibitin ya ajiye ni, ya juya ya wuce, ban wani jima sosai ba, aka yi wa Assidiq allurar na taho gida
Kai tsaye kuma na wuce family house din su Bashir.
Sashen Murja na fara shiga, saboda muna ɗasawa da ita.
Da Maama na fara cin karo, ta rugo da gudu hade da makale ni tana fadin "Oyoyo Auntynmu" haka take kirana ita ma.
Na ɗan daga ta sama, kasancewar akwai Assidiq a bayana sai na dire ta, lokaci daya kuma muka shiga dakin Murja.
Kwance take saman kujera 3sitter da waya a hannunta
Cikin tabe baki na ce "ana sana'ar ne"
Murmushi ta yi hade da mikewa zaune tana fadin "Ki bari kawai, wani novel na samu mai shege zaƙi"
"Haka dai, daga Monday har sati" na ba ta amsa ina zama kusa da ita
"Daga ina kike?"
"Asibiti, Assidiq na kai allura"
"Ki ce yau akwai kuka"
"Ki bari fa, ga shi Babansu ba ya nan, bare ya taya ni rarrashi."
"Har ya fara zuwa aikin ne?"
Kai na daga a hankali, kafin na ce "gulma na zo mu yi"
Cikin dariya ta ce "Ina jin ki"
"Don Allah wai wacece Saratun nan ne? Na ga ranar can kuna ta raina min hankali. Amma yanzu na fahimci akwai wani abu tsakaninta da Abban yaran nan"
"To ba dai ruwanki, na ki ido" ta yi min maganar da alamun kashedi
"Dama ni ina ruwana, ni fa so nake kawai ki fada min wacece ita"
"Auho! Bazawara ce, mijinta ya rasu bai dai yi shekara da mutuwa ba"
Cike da mamaki nake kallon Murja, mijin nata bai yi shekara da mutuwa ba, amma har ta fara barbarar wani. Kodayake Ai duk ɗaya ita Abbansu Khalil din.
Mun jima muna hira, kafin na shiga part din Inna.
"Tun dazu Maama ta fada min kin shigo, kuma sai na ji ki shiru" cewar Inna bayan ta amsa sallamata
Assidiq na sauke, a lokacin da nake kokarin zama saman kujera sannan na ce "Na shiga Sashen Maman Abida ne"
"Shi ya sa"
Cike da girmamawa na gaishe ta, sannan mu ka shiga labarin duniya.
Da kaina na shiga kitchen na girka mana abinci, har da wanda zan diba zuwa gida
Assidiq kam sai karfe daya allura ta fara tabashi, inda Allah Ya taimake ni na gama abinci, kuma gida da yawa wannan ya dauka wannan ya dauka, Sai 4pm aka samu ya yi bacci. Ni ma na samu damar yin sallahr la'asar.
Muryar da na ji tana rangaɗa sallama ba karamin kayar min da gaba ta yi ba. Na yi tsum ina tambayar kaina, me ya kawo ta gidan kuma, tun yaushe take zuwa?
Juyowa na yi sosai, wannan ya ba kwayoyin idanmu damar haduwa, yau kuma sanye take da riga da zane na atamfa, ta saka madaidaicin hijab.
Kasa ta tsugunna, suka shiga gaisawa da Inna wacce take goye da Assidiq.
Kafin daga bisani ni ma ta miƙo min gaisuwar na amsa ba yabo ba fallasa.
Sannan ta shiga kiran Maama wacce ke zaune saman kujera ta na cin abinci, amma mirsisi ta ƙi zuwa ko ta amsa ta. Kamar ma ba da ita take ba.
Omo da subalai ta ajiye Inna, sannan ta mike tana fadin "Dama zuwa na yi in gaishe ku"
"To an gode Allah Ya saka da alkairi, ki gaishe da Innar taku"
Ta amsa da to hade da ficewa daga dakin zuwa tsakar gida.
Idanuna na janye daga kanta hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya. A raina na ce "Iska na wahalar da mai kayan kara"
Saboda a jikina nake jin Bashir ya wuce da ajin Sarai, irin yaran nan ne girman talla, da alama ba ta yi karatu mai tsawo ba.
"Ki tashi kar yaran nan su dawo kina nan" Inna ta katse min tunanina
Na mike daga zaunen da nake, kafin in yi magana ta kuma cewa "Ki bar Assidiq din a nan, idan ya tashi a kawo miki shi, tun da an samu ya yi bacci"
Sosai na ji dadin maganar, saboda dama Ina ta jimamin yadda za mu kaya idan an tashe shi
Maama kuma ta kafe sai ta bi ni, na fito hannunta cikin nawa, daya hannun kuma rike da foodflask.
A tsakar gidan na hadu da Murja, ta ce "Wai har za ki tafi, na dauka na za a kawo su Affan din"
"Ai ban fadawa mai mashin din su ya kawo su nan ba."
"Sai ki ga mutuniyar ki"
Wani abu ya daki kirjina kafin na ce "Dama tana zuwa ne?"
"Wannan shi ne zuwanta na uku ina jin dai"
Gabana ya kuma faduwa tsoro ya kama ni, amma ban nuna a fuska ba na ce "Hu'umm"
"Sosai son yayanmu take yi, idan da alkairi Allah Ya tabbatar"
Sai na kasa cewa amin, Sai yake da na yi hade da nufar kofa ina fadin "Idan kin samu lokaci ki zo ki sanya min salataf zan yi kunshi"
"To" ta amsa min, kafin in yi magana kuma kiran Abbansu Khalil ya shigo wannan ya sa na daga
Bayan ya amsa sallama ta ya ce "Har yanzu kina fushin ne, na ji ba ki kira ni ba, ko irin ya hanyar nan"
"Kai din ma ai ba ka kira ba"
"Ni aiki ne ya min yawa, kin san sabon wuri"
"Ni kuma Assidiq ne ya rufa ni da kuka"
"Amma ya yi shiru ai"
"to ga shi nan dai bacci yake yi. Yanzu na hadu da bazawararka" duk yadda na so in rike abun na kasa
"Wacece?" ya tambaye ni
"Kenan suna da yawa?" ni ma na tambaye shi cike da kishi
Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce "Khadija tawa"