Sashe 38
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da safe tare da shi mu ka shiga kitchen, yayin da su Affan ke ta shirin makaranta, su suka shirya Maama wacce ke ta rigima wai ta ba za ta je ba. Around 7:30am mai kekensu ya zo, bayan sun tafi ya rage gidan daga ni sai shi.
kuma a lokacin ne na zauna ina cakular abincin, saboda Sam ba na jin dadin komai, ina zaune a wurin ya sakko cikin shirin fita office, kai tsaye dining din ya tunkara, dalilin da ya sanya ni hada mishi komai, da Bismillah ya fara kurbar tea din kafin ya ce "jikin ne?"
Kai na girgiza a hankali kafin na ce "Kawai bakina ne babu dadi and it seems like kana fushi" na yi maganar cikin langabar da kai gefe
"Ta ya ba zan yi fushi ba, a gabana fa kike kukan hada zuriya da ni Khadija, ba kya son jinina kenan"
Tea cup din na ajiye hade da kallon shi kafin na ce "Haba yallaboi, ya za ka juya min magana, wlh ba haka nake nufi ba, kawai dai na ga cikin ne ya yi wuri, ya kamata in dan huta, shekara hudu da aure yara uku"
"Me suka rasa?" ya yi tambayar idanunshi a kaina
"Ba komai" na ba shi amsa
"To babu ruwan ki, kawai ki yi ta haifa min, Allah ba zai hana ni abin daukar dawainiyarsu"
"To ka yi hakuri don Allah, Allah Ya bamu masu albarka"
"Amin, haka ya kamata ki ce. And cikin wata uku ne, an ce babu yawan zirga-zirga ko aiki mai nauyi, saboda har yanzu bai zauna daidai ba."
Kai na jinjina alamar fahimta, kila wannan dalilin shi ya sa jiya da dare bai kusance ni ba kenan, don shiga kitchen ba bakon abu ba ne a wurin shi.
A nutse ya yi break din shi muna taɓa yar hira, Sai bayan da ya gama ne zai tafi ya ce" Khadija please take good care of my baby, ba na son komai ya samu cikin nan I'm telling you. Abinci ki yi mai sauki"
"In Sha Allah" da haka na rako shi wurin mota, hade da bude mishi gate ya fita.
Bayan fitarshi aikin hada turarena na shiga yi, ina tsaka da aikin ne Maman Aiman ta shigo, don haka mu ka ci gaba da yi tare da ita muna hirar duniya.
Akwai humra, da kuma su roll on kananu masu taushin kamshi da kuma masu karfi irin na maza. Sosai Maman Aiman ta rika yabawa da turarurukan, ita ce ma ta dauki hotunansu ta daddora a status tana min talla.
Tun kafin ta fita na ga mutane na ta tambayarta nawa, kuma a ina za su samu. Abun ya yi min dadi, na rika addu'ar Allah dai ya sanya min albarka a abun.
Ragowar abincin break fast din mu na ci, na yi sallahr azhur na kwanta bacci, Sai la'asar na farka, shi ma Assidiq ne ya tashe ni, ruwan zafi na fara dorawa, sannan na yi wanka hade da yin alwala na yi sallahr la'asar, bayan na idar na yi azkhar dina, na yi wa Assidiq wanka, na shirya mu gabadaya, zuwa lokacin kam har farar taliyar da na dora ta dahu, na yi mana souce din cabbage. Na shirya a dining, saboda na san nan da 30mns, da maigidan da yaran gidan duk sun dawo.
Bashir dai 5:30pm ya dawo, su Affan ne sai 6pm,saboda makarantar hade take da Islamiya.
Haka dai rayuwa ta ci gaba da juyawa cike da farin ciki, saboda zamana a sabon gidan nan, farin cikin da nake samu da kulawar da nake samu, ban same ta lokacin da nake amarci ba.
Shi ya sa lokaci kankane na yi haske hade da yin ƴar ƙiba, musamman da ya kasance akwai yaron cikin. Bangaren sana'a kam, a hankali Maman Aiman ke kawo min customer na cikin unguwa da wajen unguwa, ni ma kuma Ina samun nawa, haka na matsa sai da Maman Hana ta rika yi min talla a wurin aikinsu, nandanan idan na hada turare ya kare, tun ina sawo kayan hadi kadan, har na fara sawo da yawa. Bashir ma yana dibar na maza ya tafi dasu wurin aikinshi, kuma sosai saye ake yi, wani lokaci har nema ake yi.
Kila dalilin hakan ne ya sanya shi ba ni jarin miliyan daya, wai in gwada saro atamfofi da rigunan yaran mu gani, idan komai normal sai ya kara min.
Ranar farin ciki hana ni bacci ya yi, da safe kam na kira Ummata na fada mata, ta ce za ta hada ni da wani mai irin sana'ar a kwari.
Aiko a waya muka gama komai, ya turo min kaya latest, ni kuma na tura mishi kudi, yanzu din ma dai Maman Aiman, Maman Hana, Bashir sune ƴan tallata, atamfofi da rigunan yaran basu tafi kamar turare ba, don sai da suka yi sati jibge babu wanda ya saya, har na fara karaya, na fadawa Ummata da Bashir. Sune suka rika karfafa min gwiwa a kan kar in damu za a saya.
Sai da kayan nan suka yi sati biyu, sannan na fara ciniki, shi din ma bashi, wai karshen wata, abu kamar wasa, kasuwancin atamfofin ya koma za a dauka amma sai karshen wata kudin . Cikin sati biyu komai babu, har ana nema, haka Bashir ya kara min 500k na karo, cikin sati su ma suka kare, inda Allah Ya taimake ni satin karshen wata ne. Na zauna zaman jiran tsammani. Sai dai karshen wata na yi na fara jin alert, wadanda suka dauka kadan take suke biyana, wadanda suka yi siyayyar 150k,sune ke ba ni rabi, ko 100k,wasu kuma duk suke biyana, cikin sati da salary kudin dakko wasu kayan suka hadu. Wani irin farin ciki nake ji babu misultuwa.
Daga lokacin kasuwancin atamfofi ya koma na ƴan albashi. Za a dauka, wata a hada min kudi, turaren ma ana daga kafar sati.
Na yadda, idan mutum na taba kudi, ba komai ne ke ɓata mishi rai ba. Kamar ni yanzu ba komai ke ɓata min rai ba. Duk tunanina a kan yadda zan inganta kasuwancina ne. Kuma Alhamdulillah kullum gaba nake ci ba baya ba.
Assidiq dole na yaye shi da shekara daya, saboda ciki ya fito sosai, yana neman wata takwas. Na sha rigima sosai, ko in ce ina kan sha, don ma su Affan na hutu, suna janye min shi.
Matar J ✍🏻
[12/23, 12:55] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 31*
Yau kam Murja na turawa kaya zuwa Ruma ta hanyar Bashir da ya shirya zuwa shi da yara wai weekend hatta Assidiq ba a bar min ba. Gidan shiru ba kowa, bayan duk na gama ayyukana, na shiga gidan Maman Aiman, a can na samu Maman Hisham, daya makociyar tawa, aiko mu ka zauna hira, Sai 6pm na baro gidan ganin magriba ta yi. Ina isowa gida na yi alwala don yin sallahr magriba. Ina raka'ar karshe na ji cikina ya yi wani irin juyi, kamar an sanya hannu a juya shi da karfin tsiya. Kafin daga bisani na ji marata ta daure gam, dakyar na dago, ba zan iya cewa ga abin da na karanta atahiyar nan ba. Ni dai kawai na farka, na ganni kwance saman sallaya, kafin kuma in kara yin wani yunkuri wani ciwon ya kuma tashi. Wani zufa ya rika lullubeni, yayin da wani ruwa ke bin kafafuna, cikin 5mns na ji kukan jariri, ganin abun nake kamar mafarki, wai na haihu cikin 30mns.
Daga kwancen da nake na janyo wayata da ke saman gado, na kira Maman Aiman na ce ta zo na haihu. Yadda take dariya na san ba ta yarda ba, ga shi na rufe gate, babu yadda za ta iya shigowa ni kuma ban iya fita, saboda uwa ba ta biyo, ba ta kara gasgata na haihun ba, Sai da ta nemo namiji ya duro gidan ya bude mata kofa.
Mamakin haihuwar take yi ba kadan ba, Maman Hisham ta kira, suka gyara yaro da ni, da tsakar ɗakin, bayan an rage kazantar jikinta. Sai da komai ya zama normal sannan na kira Bashir na fada mishi cewa na haihu, na samu Baby boy. Shi din ma bai yarda ba, Sai da na tura mishi hoton Baby, haka na rika kiran mutane ina shaida musu na haihu. Ummata murna ba a magana, haka Yusrah da su Badiyya kawayena.
Karfe biyu kam na safiyar Asabar Bashir na a gate din, tare ya taho da Jamila kanwarshi, yara tsalle, da murna sun yi kane, Maama kam fushi take yi, wai mace take so. Ni kaina macen na so, ina son in samu Ramla. Yarinyar na raina.
Haka na rika amsar yan barka, musamman customers dina, Ana gobe suna yan Kano suka iso da yan Ruma, gida ya cika taf, musamman ranar suna, ban taba haihuwar da na tara mutane gami da samun abun arziki ba kamar haihuwar Aliyu Haidar. Tabbas ya zo min da goshi, Sai godiya kawai.
Raguna biyu Bashir ya yanka min, washegari aka suya hade da rabawa makota, da duk wanda yake da rabo, ranar lahadin gidan ya koma namu, saboda a ranar Jamila da Yusra kanwata suka tafi, yayin da Bashir ya dakko min wata yarinyar mace, za ta 45 years, sunanta Uwani, wai mijinta ne ya rasu, ya bar ta da yara hudu, ita ce ke taimaka min da aikin gida, za ta zo safe, ta tafi bayan magariba. Duk wata muke biyan ta.
Ina jin dadin zama da Uwani sosai, mace mai kawaici, mara kiwa ga tsabta da taka-tsan-tsan. Ga hak'uri da yara, ba ta da saurin hasala.
Har kayan siyarwa ta take dauka zuwa unguwarsu, idan ta siyar in sammata wani abu, aikin hada turare duk tare muke yi.