Sashe 40
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata dariyar na kuma yi, ko ba komai sai na ji wani kaso na damuwata ya ragu, duk da ba maganin abun Maman Aiman ta yi min ba.
Har Uwani ta dawo hirar kishiya muke yi, irin zaman da ta yi da tata, ni ma ina fada mata irin zaman da na yi da Maman Khalil, zama mai dadi da tsafta.
Matar J✍🏻
[12/23, 14:12] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 32*
Maman Aiman ce ta ba ni kwarin gwiwar faɗawa ƴan'uwana, Abban Khalil zai yi aure, kowa dai hak'uri yake ba ni, da kuma fada min in kawar da kai, hatta kawayena Samira da Badiyya abin da suka fada min kenan, Sai kuma alkawarin da suka yi min na za su zo biki. Ummata ma da Yusrah kwantar min da hankali suka yi, hade jaddada min in yi ta hak'uri. Wannan ya sa wani kaso na damuwata ya kara raguwa.
Saboda na fahimci dole sai na yi hak'urin,wani lokaci Sarai ba ta tashi kiran Bashir sai yana gida, kila kuma coincidence ne oho. Shi kuma baya jin nauyin dagawa, Sai dai ni idan abun ya ishe ni in tashi in bar wurin. Tursasa kaina kawai nake yi, a kan danne kishina, amma abun ya ci tura, kullum jikina nunawa yake yi. Is not easy handling din wannan situation din. Akwai matukar wahala wajen jiran shigowar kishiya. A lokacin na san lallai Maman Khalil ba karamin hak'uri ta yi ba. Ai koda wannan fargabar a ka bar mutum na jiran shigowar kishiya ya ishi mutum. Abin da na fahimta kawai kishiya, kishiya ce, ba ta da gaba bare baya. Ba ta a farko kuma ba ta a karshe.
Idan ke ce farkon za a karo miki wata sai kin ji babu dadi, idan taraswa za ki yi nan ma dai hakan ne. Babu abu mai sauki.
Ana saura sati hudu biki Bashir ya fada min wai a cikin satin Saratu za ta zo ganin gida. To kawai na ce. Maman Aiman kawai na fadamawa, ta ce eh ana yin haka, Sai na dan rage damuwa.
Ranar Asabar ta zaba a matsayin ranar da za ta zo, tun juma'a Abban Khalil ke maganar, safiyar Asabar din ma, bai bar ni na huta ba, haka ya dame ni fa zuwan Saratu har su Khalil ya fadamawa, wai sabuwar Auntynsu za ta zo. Son barka ba su yi maraba da abun ba, tun ba Affan ba, gara ma Khalil ya na ce da tambayar wacece. Bare Maama da ba ta ma fahimci ina zancen ya dosa ba.
Abban Khalil bai tsaya iya nan ba, har Uwani ya fadamawa da ta zo aiki da safe, wai a yi abinci special akwai baki. Wannan abu ba karamin kona min rai ya yi ba. Saran kamar wata queen Elizabeth.
Bayan ya fita ne Uwani ta ce "Auntynmu me za a girka, na ji yallaboi ya ce akwai baki"
"Tuwo" kai tsaye na amsa mata
"Wane iri?" ta kuma tambaya, na dan yi shiru kafin na ce "Ayi na shinkafa miyar ganye"
"Dole sai an je kasuwa ai, lokaci bai kure?"
Na kuma yin shiru kafin na ce "To a yi miyar wake, tun da akwai ganyen ugu a gida."
Da to ta amsa. Komai ban taya Uwanin ba, na haye sama da Haidar na kyale ta. Sabanin baya da muke girki a tare.
Misalin 1pm Bashir ya kira ni, wai a bude musu gate gasu nan. Ban amsa ba kawai na yanke kiran, Sai da na ji horn din motarshi, sannan na sakko kasa na cewa Uwani ta bude musu kofa.
Cikin falo na zauna, saitin windown da ke hango min farfajiyar gidan.
Ina daga zaune na ga fitowar Sarai, cikin wani lace coffee color, dinkin riga da zane, ta yafa gyale golden jaka da takalmin ma duk golden ne, ba dressing dinta kawai ne ya ban mamaki ba, har da yadda ta yi wani haske hade da yin kina mai kyau, kasancewarta gajera ba ta faye tsawo ba, hips din nan ya fito sosai.
A zuciyata na ce "Dole Bashir ya rude, yana kallon wannan cikar, lallai ba zai zauna lafiya ba, amma yaushe yarinyar nan ta yi wannan kibar, da wannan uban hips din, ga wani haske. Tabbb! Ikon Allah kenan" na karashe maganar zucin hade da rike habata alamun mamaki
Ban san me suke cewa ba, amma dai na ga Bashir ya koma cikin mota ya dakko key hade da bude mata gudan part din nan mai kallon yamma.
Bayan shigarsu ciki ne, na sake labulen hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya ina fadin "Wayyyo Allahna ni Khadija. Ashe haka Maman Khalil ta ji da za a kawo mata ni, har nake cewa da ma ni ce ta taras. Baiwar Allah ashe ba karamin hadiya ta yi ba. Don Allah Sakeena ki yafe min?" na yi maganar hawaye na son taruwa a idanuna. Da sauri na mayar da su ina fadin" No! No!! No!!! Khadija kada ki yi kuka, waccan yarinyar ba ta kai matsayin da za ki yi mata kuka ba."
Ina zaune a wurin Bashir ya shigo, kallo daya na yi mishi na kawar da kai, shi ne ya ce min" Khadija baƙi sun iso"
"Eh na ji su, sannunsu da zuwa"
Baki ya washe kafin ya ce "Ba za ki je ku gaisa ba"
Da sauri na mayar da kallo na kanshi, kafin na ce, ban gane in je mu gaisa ba? Kamar ya in je mu gaisa, ba sune suka same ni a nan ba, ai kamata ya yi su fara zuwa nan kafin su shiga ko ina"
Dan shiru ya yi kafin ya ce "Kuma fa haka ne, to ina zuwa." Ni dai komai ban ce ba, ya ja shagidaddar kafarshi ya fita.
Ina jin shi yana cewa Uwani ta kai musu abinci.
Kamar mintuna biyar Uwani ta shigo, kallon ta na yi, ina fadin "Kin kai musu abincin?"
Cike da girmamawa ta ce "Eh"
Har za ta fita kuma, sai ta dawo ta ce "Auntynmu kar ki ce zan yi gulma fa"
Kallon ta na yi ba tare da na yi magana ba, hakan ya sa ta ce "Wai ita waccan din wacece, na ji Alhaji na ta fama da ita, ta zo ku gaisa, amma wai ta ce ke ya kamata ki je ku gaisa, tun da su baƙinki ne"
"Kan bala'i! Haka ta ce?" na yi saurin katse Uwani
Kai Uwani ta gyaɗa alamar eh.
Wani murmushin takaici na yi kafin na ce "Aiko koda ubanta take yawo a zariyar wando, wlh ba zan je in gaishe ta ba. Yau za ta ga sarautar uwargida. Ai idan dai amarya ba ta hau doki ba, to kuwa bai kamata a dora mata kaya ba"
Kallo na kawai Uwani ke yi, jin tahowar Bashir ya sa ta nufi kofar fita. Ni kuma na hade fuska ina tattaba wayata, yadda ya yi tsaye cikin rashin sanin abun yi ne ya sa na ce "An kai musu abincin?"
"Eh" ya amsa min, kafin ya zauna kujerar da ke fuskantata ya ce "Saratu ta zabi wancan part din"
"Shagalinta" na fada cikin ko in kula, kuma har zuwa lokacin ban kalle shi ba.
Ya kuma cewa "Khadija bakonka Annabinka, ki je ku gaisa da yaran nan, wai su kunyarki suke ji"
Wani kallo na yi mishi kafin na ce "Kunya! Wace irin kunya kuma? Sai yau ne suke jin kunyata, a Ruma sau nawa suna zuwa wajena, ni ba na son gulma da munafurci."
"Haba me ye kuma ya kawo wannan furucin?" ya yi saurin tara ta
"Ga abin da ya kawo shi nan, dama fa ba wurina suka zo ba, idan sun yi abin da ya kawo su kawai su tafi, ni ba ni da case da su. Basu ji kunyar zuwa gidan ba, Sai kunyar zuwa gaishe ni." na karasa maganar da jan siririn tsoki
"To tsokin na waye?" ya tambaye ni yana dan hade fuska.
Maimakon in amsa mishi, mikewa na yi, kawai na nufi stairs, don Ina jin kila ma Haidar ya tashi.
Ban san lokacin da ya bar falon ba, kuma tun da na hau saman ba sakko ba, Sai da Uwani ta sanar min sun tafi kafin na dawo falon. A zuciyata nake fadin "Ka ji min kilbabbar yarinya, yau wata gulma ce ta tashi, da ni ce zan je in, gaishe ta, ai uban kuturu ma ya yi kadan bare na makaho. In ji yara" haka nan sai raina yay ta baci, abincin ma kasa ci na yi. Sai da yara suka dawo sannan na dan warware. Shi kam bai dawo ba sai bayan sallahr isha'i. Na hade fuska kam, don ma Kar ya ce zai min wani sharhi. Saboda a sama nake ya hancin gauta, yana taba ni, zan fado kanshi.
Ana saura sati biyu biki na zabar mana shadda mai kyau, mu dukkanmu iri daya, sannan na zabi lace, atamfa kala biyu lace ma kala biyu, wa mu matan bayan shaddar.
Mazan ma na kara mu shadda kala daya, da yadi masu kyau kala biyu. Sannan na sawo musu yan kanti, da takalma kafa hurhudu da huluna.
Sosai na kashe mana kudi, kuma babu wanda na nunawa Bashir, shi din ma bai tambaya ba, harkar bikinshi kawai yake yi, abun da yake bata min rai kenan.
saura sati daya aka, zo aka kara fente gidan tas, har da part dina, abun mamaki sai Bashir ya ce a kwashe kujeruna, wai canja min za a yi.
Saura kwana uku daurin aure sai ga kujeru, masu kyau da tsada yan waje, aka kara canja min tv wacce ta fi waccan girma, da kuma labulaye. Ni kaina dakin ya yi min kyau sosai, duk da zuciyata babu dadi.
Ana saura kwana biyu daurin aure muka fara karbar baki, part din nan daya aka bude yan Ruma da dangina, kasancewar akwai dakuna da yawa a ciki, kuma akwai toilet a ciki.
Makotana ma suna da lekowa don ganin ko akwai ayyukan yi.
Bangarena kam, ba zan iya misilta yadda zuciyata take ciki ba, komai baya min dadi, musamman idan na kalli Bashir yana ta rawar kafa, in ji kamar in rufe shi da duka