Sashe 36
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda nake imagination din gidan sai ya wuce da tunanina, gida ne tangameme, mai dauke da katon farin gate, fentishi daga gaba white and ash ne, sosai ya haska hade da bayar da kala.
Kana shiga akwai dakin maigadi, wanda daga saman dakin ne, aka dora water tank Manya guɗa biyu, daga nan sai katuwar farfajiyar gida mai dauke da doguwar katanga wadanda madaidaitan fulawa suka zagaye saboda yanzu suka fara girma.
Daga can bangaren yamma wajen dakin maigadi akwai bishiyoyin mangoro, guava, cashew, umbrella, gwanda da kuma ayaba. Wadanda su ma basu gama girma ba.
Sai ka dan yi tafiya kadan sannan za ka iske part din farko, wanda yake bangaren gabas kofarshi tana kallon yamma, daga bangaren yamman kuma akwai wani part din, kofarshi na kallon gabas, wannan ya sa suke facing din juna.
Idan ka dan kara gaba, to a kawai wani part din daga bangaren kudu, kofar shi na kallon arewa, kenan part din can biyu su dan ba shi baya. Kuma duk ya fi su girma, saboda shi upstairs ne ma. Shi ma kuma a gaban entrance din akwai doguwar farfajiyar ko in ce tsakar gida, wacce za a iya parker motoci uku a tsaye ba a kwance ba.
Kuma nan Bashir ya ce mu shiga shi ne part dina.
Ban gama tsinkewa da lamarin ba, sai bayan da na shiga, an zuba komai na gyaran falo, very unique babu hayaniya, Irin cool falon nan dai na ƴan gayu. Kujeru leda ash colour mai haske, Sai stool da katuwar plasma. Idan ka dauke wannan babu komai a cikin a falon. Sai bangare daya da aka yi dinning area. Ta Kuma cikin dinning din ne kofar kitchen take.
Still a cikin falon daga kasan stairs din haurawa sama akwai corridor, wanda a nan ne dakin yara yake, dakuna ne guda biyu da aka zuba komai da yara ke bukata, na san daya na mata daya kuma na maza.
Upstairs kuma akwai wani room and falon guda biyu, daya nawa daya na Bashir, su ma an zuba komai na gyara.
Ban san lokacin da na fadi ina yi wa Allah sujuda ba, na fashe da kukan dadi, Murja ta dago ni tana fadin "Ikon Allah, abun murna sai kuka"
Su Yaya Habi suka shiga dariya suna "fadin kukan murna ne" tabbas kam kukan murna nake yi, a rayuwata ban taba koda mafarkin ina a irin wannan gidan ba. Bashir ya shigo ya same ni zaune ina ta kuka su Aunty Habi sun zagaye ni, yara ma sun yi cirko-cirko suna kallo na.
"Me ya faru?" ya yi tambayar fuskarshi na nuna damuwa
Cikin dariya Aunty Habi ta ce "Kukan murna take yi."
Siririn tsoki ya ja komai bai ce ba, Sai Assidiq da ya dauka, Aunty Habin ta dora da"Dole ta yi kukan murna. Bashir Allah Ya kara arziki, Ya sa ka fi haka, Allah Ya saka aminci a wannan gida, ya kare ku da dukkan sharrin abun ki, ya tsone idon makiya"
"Amin" duk suka amsa.
Yara kam bin bayanshi su ka yi suna murnar, wai nan gidan ya fi na Abuja kyau.
Ba jimawa aka shigo mana da katuwar kula, katon na ruwan gora da minerals.
Har da plate da spoon, Wai daga makotana.
Nan fa aka hau cin abinci aka yi sallahr azhur, kafin nan muka sauka kasa muka shiga zagaye gida.
Kowa na kara yabawa. Sai da muka yi sallahr la'asar sannan muka shiga makotana, na kusa sosai na yi musu introducing kaina. Sannan na yi godiya ga matar da ta kawo min abinci, ita ce muka hada katanga da ita a bangaren dama, ta ce min sunan ta Amina. Amma ana kiranta Maman Aiman
Ita kuma ta bangaren hagun ba ta nan, wai tana Amerika ita da mijinta.
Naso su Yaya Habi su kwana, amma suka ce ina tafiya za su yi. Misalin biyar na yamma kam suka bi motar da ta kawo mu.
Ni kam jina nake kamar sabuwar amarya, ashe dama haka sabon gida yake. Gidan na kara kalkalewa na kunna turaren wuta, yaran kam suna can rashin ji a tsakar gida.
Sai da aka yi sallahr isha'i Bashir ya dawo, hannunshi dauke da ledar take away, yaran ne suka tarbe shi, kusa da ni ya zauna yana fadin "Washhh Allahna!" a hankali
"Sorry!" na fada cikin nuna kulawa
"Thank you" ya amsa hade da kwantar da kanshi jikin kujera.
Yayin da ni kuma nake zaro robobin take away, na ba kowa daya-daya. "Yallaboi kai fa?" na yi maganar lokacin da nake aje mishi robar ta shi take away din a kusa da shi.
Mikewa ya yi daga kishingiden da yake yana fadin "Sosai na gaji ne."
"Sannu" na kuma fada lokaci daya kuma Ina bude robar take away din
Bayan na mika mishi ya fara ci ne ya ce "Khadija kin ga gida, ya yi kyau?"
"Sosai ma, ai ni ko bai yi wa kowa kyau ba ni ya yi min. Duk wani abu daga gare ka ai mai kyau ne, bare na wannan kowa ya yaba. Sai dai a yi fatan alkairi kawai"
Murmushin jin dadin maganar da na yi yake yi, yana tauna abincin a hankali ya ce "A cikin gidan menene bai yi miki ba?"
"Komai ya yi min Yallaboi, tsakanina da kai sai addu'a kawai, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi. Ummanmu na ta ma godiya kafin ta zo"
"Me kika ce mata?"
"Ka yi min gata mana."
Na ba shi amsa. Ya kuma murmusawa kafin ya ce "You deserve it. Na san fa kina da hak'uri. Ki kara hakuri da halina. Ko na yi niyyar kawar da kai a lamarin su Affan sai in ji na kasa. Ba wai don kina cutar dasu nake tambayarsu ko tambayarki wani abun game dasu ba. Kawai idan ban yi hakan ba ne ba na samun nutsuwa "
" Ba komai, na fahimta "
Na yi maganar a sanyaye, lokaci daya kuma na juya ina kallon Assidiq da yake kuka.
Kafin ma in yi magana har Affan ya kwaɗe Maama, kamar kiftawar ido shi ma Khalil ya kwaɗe shi, Sai fada ya kacame. Komai Bashir bai ce ba, ni ce na mike da sauri na shiga tsakaninsu kowa na ta huci "Me ya faru?" na yi tambayar ina kallon su.
Maimakon amsar Affan ne ya fashe da kuka, saboda shi idan abu ya ba shi haushi, ko idan yana da gaskiya ba ya magana sai kuka. Wannan ya sa na juya kan Khalil na ce "Me ya sa za ka duke shi?"
Sai da ya gama kumbura sannan ya ce "Shi ne fa ya duki Maama"
"Haba Khalil, kai babba ne, ka dinga hak'uri don Allah" na yi maganar ina shafa kanshi, Affan kam tuni ya fada kan kujera yana gursheƙin kuka, alamun dai ya hau jakar kuturu.
Hannunshi na kamo hade da dago shi daƙyar, saboda yadda yake dagewa na ce "Haba ɗanɗana, ka san yanzu da kai nake yi, tuni na yaye Khalil, ka yi shiru kar a ganmu a rana. Kuma ka sha kurumin ka, zan koma Ruma in dakko ma Maryam in kawo ta gidan nan ka rika kallon ta kullum kana farin ciki"
Ina zuwa wannan gaɓar, Sai ya fada kan jikina yana kunshe dariyarshi
"Ashe dai da gaske Affan son Maryam kake yi, lallai ya kamata in kai toshi," ina kai wa nan ya kwace daga jikina hade da rugawa a guje ya hau stairs yana dariya, Khalil din ma bin bayan shi ya yi yana dariya.
Duk budurin da muke komai Bashir bai ce mana ba, Sai abincin shi da yake ci a nutse. Sai bayan da suka haura ne ya ce" Wacece Maryam kuma? "
Cikin dariya na ce" Yarinyar Kawunshi Shamsu. Ya ce min kin ga Auntynmu idan na tashi aure Maryam zan aura, tana da kyau, ga gashi"
Baki bude Bashir ke kallo na, yana murmushi, kafin ya ce "Wai shi Affan din, dama yana magana haka, har ya san wani kyau?"
Dariya na saki kafin na ce "Har ga shi ma ya fada"
"Tabdijam! Allah Ya kawo mu zamani. Affan just 11-12years fa. Aiko zai ci uban shi"
Wata dariyar na kara yi, ina fadin "Kuma sai ka ga abin da ba mu yi tsammani ba ya faru. Yanzu fa duk yarinyar shekerarta biyu, ka ga ko lokacin da za ta isa aure ai Affan ya mika"
Kai ya jinjina kafin ya ce "Babu mamaki a lamarin ubangiji kam. Allah Ya rufa mana asiri"
"Amin" na amsa, ina kallon Assidiq da yake ta rashin jin shi, shi kadai, saboda Maama ma ta bi su.
"Affan idan yana fushi yana min kama da Mamanshi, idan ta yi fushi." ya yi maganar yana dan murmushi mai ma'anoni da yawa
Ni dai Allah Ya jikanta kawai na ce, hade da kawo batun da zai tafiyar da waccan hirar, saboda na tabbata hakan zai iya shafar abin da na yi mishi tanadi a daren yau.
Cikin ikon Allah kuwa na kawar da hirar, shi ya sa daren ya zame mana rayayye, kuma abun tunawa a gare mu ba ki daya.
Da safe babu wani wahala komai na kammala gyaran gida, da kuma hada break fast. Bayan mun karya ne Abban Khalil ya ce zai je wata makaranta ya siyowa su Affan form da Maama.
Bayan fitarshi da kaina, na zagaye gidan, ina ganin yadda aka kashe kudi ba na wasa ba, wurin gininshi. Su Khalil kuma ball suke yi a farfajiyar gidan.
Bayan na gama zagayen ne na koma kan entrance na zauna Ina kallon yadda suke buga ball din cike da Nishadi. Idanuna na dora a kan plat din nan guda biyu, wannan yana nufin akwai sauran mace guda biyu a kan hanya kenan.
Gabana ya bayar da wani irin rass, ina ta imagining yadda zan yi ranar da za a yi mini kishiya, dama-dama ma idan Sarai ce, amma jikina yana ba ni Bashir ba zai dakko Sarai ya aje ta a wannan kayataccen gidan ba. Kila wata mai degreen zai dakko ya zo ya hadamu in yi ta fama, idan haka ne kam, Sai in kwashe tarkacena in nufi Ruma, babu dalilin zama hankalina yana tashi.