← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 44

Sashe 44

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan Uwani ta yi breakfast, kan entrance muka dawo, domin hada turaren wuta, na kamshi, humra da kuma roofreshener, aikin da ya dauke mu har 12pm. Kuma har zuwa lokacin Saratu ba ta fito ba, sosai abun ya ba ni mamaki, ni dai ban kai mata abinci ba, kuma ban ga Bashir ya sawo mata ba. Na fita batunta muka shiga hidimar girkin rana.

Sai dai misalin karfe 1pm sai ga Bashir da take away, kai tsaye kuma ya wuce bangarenta, after like 20mins ya fito, a kitchen ya same mu ya ce an gama abincin rana, na ce yana hanya dai, daga haka ya wuce abin sa, wai ya koma wurin aiki.

Sosai takeaway din Nan ya taɓa min zuciya, kun san kishi dai, bare ni mai nawa a kusa. Sai dai haka na danne ban tanka ba.

Abu kamar wasa, har na fita girki Sarai ba ta taba ko shiga kitchen din ba, bare ta dora abinci, take away ake yi mata.
Na zuba ido in ga Ikon Allah tun da girki ya dawo kanta.

Da dare Bashir ya koma ɗakinta, haka na rarrashi kaina dakyar na yi bacci. Karfe hudun asuba alert dina ya tashe ni, alwala na yi, hade da yin sallah raka'a biyu, bayan na idar na yi lazumi hade da karatun alkur'ani, ban tashi ba dai sai da na yi sallahr asuba na nufi kitchen.

Abun mamaki a rufe gam, tun ina tunanin datsewa ya yi har na fahimci an rufe kitchen din ta waje ne. Ga shi ba ni da extra key, haka na koma kitchen dina na ciki na yi tsaye, babu wani abu da zan sarrafa a ci, komai yana kitchen din waje.

Fadin takaici da bacin ran da na ji bata lokaci ne, musamman da na ga rana ta fito, ga yara har sun gama shirin makaranta. Khalil ne ya ce "Auntynmu ko mu je mu yi wa Abbanmu magana ya bamu wani key din?"

"Kyale shi kawai Khalil, dakko min jakar da nake ajiye kudi, ku sawo bread da kwai, da mai, Sai kuma Maggi."
Na yi maganar zuciyata babu dadi.

Affan ne ya dakko jakar, ya ciri kudi, suka tafi tare da Khalil. Basu jima ba suka dawo, don haka na soya musu kwan, suka hada da bread suka karya, ni dai ɓacin rai hanani cin komai ya yi. Juice kawai da biscuits suka tafi da shi school, Sai na hada musu da kudi, koda ba a kawo musu abincin rana ba.

Haka na zauna zuciyata na ta min daci, gyaran dakin ma na kasa, Sai da Uwani ta zo, ta gyara ko ina.

Sai 10am Bashir ya fito cikin shirin fita aiki, lokacin ina sama, ina ta aikin lallashin zuciyata.

Sanye yake cikin royal blue din yadi da aka yi wa ɗinkin zamani. Sosai ya yi kyau, jikin lukui bai boye jin dadin da yake samu ba.

Daga kwancen da nake na ce "Ina kwana?"

Ya amsa min, lokaci daya yana zama kusa da ni, hannuna ya saka cikin na shi kafin ya ce "I'm sorry, na so leko ki da Asuba, Sai Nana ta tashi da ciwon ciki"

Ba tare da na kalle shi ba, na ce "ba komai"

"Me kika dafa da safen?"

Kamar in fada mishi abin da ke min zafi sai kuma na fasa na ce "Ban yi da yawa ba, ni ma da ciwon kai na tashi"
Hannunshi ya kai saman goshina kafin ya ce "Kodai ba ki yi bacci ba?"

Karon farko da na kalle shi muka hada ido na ce "Me zai hana ni bacci?"

Maganar ya kawar da fadin "Zan tafi aiki, akwai abin da kuke bukata ne?"

Kai na girgiza alamar a'a

Ya mike daga zaunen da yake lokaci daya yana daukar Haidar da yake wasa, ya ce "My lion, za a yi min rakiya?"
Ni dai yi na yi kamar ba na jin su.

Ya gama surutanshi ya aje min Haidar din ya fita.

Misalin 11am na sakko kasa, Uwani zaune tana kallo a falo. Ganina ya sa ta gyara zamanta hade da kara gaishe ni. Kafin ta ce "Dama Ina ta addu'ar Allah Ya sa ku tashi da wuri, na ji kitchen a rufe"

Sai da na zauna saman kujera, sannan na ce "Je ki wurin Amarya ki amso mana key din"

Komai ba ta ce ba, ta mike, yayin da ni kuma na zauna zaman jiran dawowarta.

Ko minti biyu lafiyayyu ba ta hada ba, ta dawo min da amsar wai ta ce ita ce da kitchen yau.

Wani kullutu, da wani mulmulallan baƙin ciki, suka taso min zuwa zuciyata suka dunkule wuri daya, wannan ya sa na shiga kokawa da su,. Tsabar ɓacin rai bishi-bishi ma nake ganin Uwani.

Matar J ✍🏻
Chapter 44 · 0% Book details