Sashe 27
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan na idar da sallahr na kara yi wa Rahma ta yin abinci a karo na ba adadi, saboda akwai flasks din abinci, wasu ma ko taba su ba mu yi ba. A karo na ba adadin ta kuma cewa "Ba na jin yunwa, Sai dai ko yaran za su ci idan sun dawo"
Su din ma kadan suka taba, wai sun koshi.
Dr Nura kam zarya ya rika yi tsakanin manya likitocin da ke asibitin, saboda Bashir ya matsa lallai sai a nemar mishi sallama, don wanke kafar da sayen magani za a rika yi ko yana gida ne.
Muna zaune a barandar ni da Rahma, Maman Hana ta iso, cikin sakin fuska suka gaisa da Rahma, kafin ta wuce ɗakin da Bashir yake, nan ma ba ta ji ma ba ta fito zuwa wurin mu
"Ashe ƴan Abuja suka iso?" ta yi maganar daidai tana zama gefenmu
"Ai kuwa, tun dazu" na amsa ta cikin murmushi, Rahma ma murmushin take yi, wata sabuwar gaisuwar suka shiga yi, kafin Maman Hana ta ce "Tubarakhallah yan maza zira gasu nan. Ya kuke fama da rashin ji?"
"Akwai kam. Dambe dai kamar filin boxing" cewar Rahma cikin dariya
"Na sani ai, ni ma mai guda uku fama nake bare biyar"
Daga haka suka shiga hirar rashin jin yara maza. Ni kam ma mikewa na yi zuwa wajen Abban Khalil, tun da ya ga shigowa ta ya mayar da hankalinshi a kaina har na karaso
"Khadija!" ya kira sunana cike da kulawa
Duk lokacin da ya yi hakan sai in ji jikina gabadaya ya mutu, tausayin kaina ya kama ni, in rinka jin kamar na zama wata abar tausayi, mai kuma neman taimako, Sai na yi da gaske nake iya matse hawayena, kamar yanzu ma da na rike hawayen da karfin tsiya
"Me ya sa kake son a sallame ka wai?"
"Saboda ke Khadija, sosai tausayi kike ba ni, kalli yadda kika koma kamar ke ce ba ki da lafiyar, kin je gidan wata kin zauna a raɓe, na tabbata dole ce ta sanya ki zaman gidan nan"
"Tabbas dole ce, amma ina jin dadin zama da Maman Hana, idan don ni ce, don Allah ka tsaya a kula da lafiyarka"
"A'a, ya kamata ki koma gida ke ma ki huta, ni kaina na gaji da zama a nan. Ya fi in koma gida, idan ma fita wajen za a yi sai mu fara shiri"
Shigowar Dr Nura da wasu likitoci ne ya sanya ni yin shiru, Sai ma kunnuwana da na raba a tsakaninsu, discussion din nasu kaf a kan file din Bashir ne. Kowannensu da abin da yake fada, wani lokaci kuma maganar tasu ta zo daidai. Kiran sallahr magriba ce ta fitar dasu. Ni ma alwala na yi wa Bashir, ni ma na yi na kabbara sallah.
Bayan na idar ina kan sallaya Affan ya shigo kusa da ni ya zauna idanunshi a kan Babanshi, har zuwa lokacin bai saki jiki ba.
Da kulawa na ce "Ko kana jin yunwa ne Affan?" kai ya girgiza alamar a'a, ban yi tsammanin zai yi magana ba, su kuma na ji ya ce "Yaushe za mu tafi gida?" a hankali ya yi maganar, saboda ni kadai ce na ji
"Ruma ko Abuja?
" Kauye"ya kuma amsawa a hankali.
"Kila zuwa gobe sha Allah"
"To shi fa Abbanmu"
"Muna jiran ya ji sauki Affan" na amsa shi a sanyaye
Hawaye ya shiga daukewa, a cikin kukan ya ce "Yaushe to zai ji Auntynmu?"
Ka cinyata na kwantar da shi a hankali na ce "Affan yi hak'uri ka daina kuka, kana dagawa Abbanku hankali. Sha Allah zai ci sauki soon. Ku dai ku rika yi mishi addu'a"
"Ai muna yi kullum, har ma da Mommynmu da Ramla, Mommynsu Farhan ta ce mu rika yi musu addu'a"
Idanuna na lumshe a hankali, wani abu mara dadi yana min yawo a kirji.
"Me same shi?" sautin Bashir ya katse min tunanin da nake son fara yi.
"Babu komai, ya gaji ne" na ba shi amsa, hankalina na a kan Khalil da yake shigowa dauke da Maamah.
Abun mamaki sai ta ki yarda in dauke ta, wannan drama ita ce abin da ya sanya mu dariya yau, cikin dariya Abban Khalil ya ce "Kawo ta nan mu gani ko za ta yarda, Sai ka huta"
Ya nufe shi da ita, cikin sa a sai ta yarda, muka kuma yin dariya, Abban Khalil ya ce "Wato yaro ma ya san na shi, kalli kiwa irin ta Maamah fa, amma wai ba ta ƙin ƴan 'uwanta"
"Abba kafar na yi ma zafi?" Khalil ya katse mana dariyar da muke da ta tambayarshi idanunshi a kan ƙafar
"Ba sosai ba Khalil, ku dai rika yi min addu'a kun ji" ya ba shi amsa shi ma yana kallon kafar.
Su Rahma ne suka shigo da Maman Hana, a nan Bashir ke fadawa Rahma Maman Hana matar Bashir Sandamu ce. Cike da mamaki Rahma ta ce "Wacce ke ta bamu wahala kenan, kin ki zaman Abuja, kuma kin hana mijinmu ya zauna"
Cikin dariya Fatima ta ce "Mijinku dai bai yi niyyar zama ba, amma ni ina ruwana" duk mu ka yi dariya.
"Rahma ya kamata ku tafi masauki, yaran nan sun gaji" cewar Bashir yana kallon yaran daya bayan daya
"Gaskiya kam, tun ba Haidar ba, kamar kaza yake, ga shi an sha tafiya."
Daga haka mu ka shiga shirin tafiya, Rahma dai mu ta bi. Dr kuma ya tafi hotel.
Matar J ✍🏻
[12/22, 15:44] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 22*
Lokacin da muka isa Umaima ta shirya abinci, shi ya sa sallah kawai mu ka yi, aka shiga cin abincin da kuma hira, wani irin shauƙi da farin ciki nake ji, wanda na rabu da jin shi, saboda yadda mutane suka hadu ana ta hira gami da nishadi.
Sai after 10pm muka kwanta, kuma 5am mun tashi, bayan sallahr asuba muka shiga kitchen taya Maman Hana abincin breakfast.
Misalin 9am muka bar gidan zuwa asibiti, a can muka samu Dr Nura, sun dora daga inda suka tsaya.
Ni dai breakfast na haɗawa Abbansu Khalil, ya dan taba ya ce ya koshi.
Tabarma muka baza a kofar dakin muka zauna, muna taba hira gami da ganin yadda ma'aikata ke ta shige da fice.
Karfe daya Dr Nura ke sanar damu an bamu sallama, amma za mu rika zuwa ganin likita duk Monday.
Maman Hana na kira hade da shaida mata, ba jimawa kuwa ta zo ta dauke ni zuwa gidanta na tattaro kayana, na asibitin kuma na bar Rahma da tattarewa.
Ba dai mu bar garin Katsina ba sai wajen karfe uku,
A hanya ma dai hirar ciwon Bashir aka fi yi, da irin matakin da ya kamata a dauka, kai tsaye gidanmu muka nufa, a maimakon gidansu, hakan kuma ya yi min dadi, ko babu komai na fi sakewa a nan.
Tun muka isa mutane ke zarya, lallai na yarda Katsinawa akwai kara, tun ba kauye ba. Wajen satinmu uku a Katsina amma kullum sai sama da mutane ashirin sun shigo asibitin nan wajen Bashir, wasu ƴan'uwa wasu kuma abokan arziki.
Gidan bai yanke da mutane ba sai wajen goma, zuwa lokacin kuwa ba kowa a gidan daga ni sai shi, saboda Rahma gidansu Sakeena ta tafi ita da yaranta.
Dr Nura kuma yana part din baƙi.
Dakin na shiga da sallama, cikin alamun bacci ya amsa min
"Wai har ka fara bacci?" na yi tambayar ganin Abdullahi bai jima da fita ba.
"Wlh kam, sosai na gaji ne"
Gefen shi na zauna ina kallon kafar sannan na ce "Sannu, Allah Ya kara sauki"
"Amin Ya Rabbb." ya amsa hade da janyo ni gefen jikinshi.
Saman kirjinshi ya kwantar da ni, lokaci daya kuma yana shafa gashina da yake a tsefe.
"Kin watsar da komai, kalli yadda gashinki ya cunkushe hade da yin karfi"
Sosai na kara kwantar da kaina a kirjinshi, ina jin yadda kasusuwan kirjin suke a jere, sabanin da can baya da tsoka ta lullubesu.
"Ba ki ji ba?" ya yi maganar da wata irin muryar da na rabu da ji. Dalilin da ya sanya ni lumshe ido, kafin na ce "Ba ta gyaran kai nake yi ba, kai zan gyaramawa kuma ga ka kwance"
"Ki, gyara min gobe idan Allah Ya kai mu ina so"
Kai na jinjina alamar to, saboda ba zan iya ba shi amsa ba, abin da ban yi tsammani ba shi ne ya faru, ni kaina ba na ce ga ta yadda komai ya faru ba, sai dai bayan faruwar komai din ni ce na taimaka mishi wajen gyara kanshi, yayin da muka sha jinya cikin dare, saboda mun tsokano kafar.
Safe su Rahma suka fara shirin komawa, babu laifi sun sha tsarabar kauye kam, yayin da Abbansu Khalil ya sha shawarwari wajen Dr Nura na yadda zai kula da kafarshi.
Yanzu kam gida ya koma daga mu sai mu, Sai ƴan dubiya dasu Abdullahi ƴan jinya, yara kuma rabi suna wurina, rabi gidan kakanninsu na bangaren uwa ko na bangaren Baba. Ba ni da case da su.
Bashir kam kullum dare za mu sha soyayyarmu, mu dawo muna jinya da safe, wani lokaci har sabon ciwo muke jiwa kafar.
Inda Allah Ya taimakemu ma kafar na sauki ba laifi, saboda magunguna da yawa aka hada, a yi na gargajiya, a yi na asibiti har da na Islamic.
Lokacin da hutu ya kare Saminu kanen Abbansu Khalil shi ne ya yi hidimar samarwa su Khalil makaranta a Batsari mai hade da boko da Islamiya , tun safe idan suka tafi sai yamma ake dakko su.
Yayin da ake kai Bashir ganin likita ko wace ranar Litinin. Kuma Alhamdulillah a cikin wata biyu sosai kafar ta yi sauki, taka ta ne kawai ba ya yi, amma yana iya mikewa tsaye da kanshi, zai iya canjawa kafar position daga wani wuri zuwa wani. Kuma ta daina ɗiwa, wani wuri ne kawai bai gama warkewa ba.
Kasancewar an fara zafi zaune nake saman tabarma da misalin karfe 5pm ina yankewa Maama farce, Bashir ya shigo gidan saman kekenshi, babu wanda zai ganshi a haka ya ce ba shi da lafiya, saboda ya yi fes abun shi, har wata ƴar ƙiba yake yi.