Sashe 25
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon shi kawai take yi, kallon shi ya mayar kaina kafin ya ce "Khadija kodai akwai abin da ke damun yarinyar nan ne ba mu sani ba. Ko a, gargajiyance haka? Rigimarta ta yi yawa."
"To ni dai ban sani ba. Amma Maama kam ai tun aka haife ta haka take"
Kai ya jinjina hade da fadin "An ce yara idan suna ganin mutuwar waninsu. Kodai ta fahimci mutuwa zan yi ne?"
"Haba Abban Khalil! Me ya sa kullum kake son kashe min jiki, maimakon karfafa min gwiwa?ka san me mutuwarka kake nufi a wajena? To ni kaina ban sani ba. Amma na san shi ne karshen tashin hankalina"
Kafin ya ba ni amsa aka turo kofar, su Abdallah suka shigo, wannan ya sa ya mayar da hankalinshi kansu.
Matar J✍🏻
[12/22, 15:41] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 20*
Duk yadda su Aunty Habi suka so in koma gida tare da su ki na yi. Ji nake ina juya baya abu mara dadi zai faru da Bashir. Hankalina ma ba zai taba kwanciya ina gida shi yana asibiti ba.
Ba don sun so ba, suka bar ni, amma sai aka ce zan zauna gidan wata matar abokinshi Mustapha, gidanta yana kusa da asibitin ne. Ni dai ba haka na so ba, na so ace a nan nake kwana kuma nake tashi.
Amma hakan ma ya yi min, ko ba komai dai zan rika kallon shi kullum.
Yanzu zaune nake a kan kujerar da ke fuskantarshi, Maama na shan nono, lokaci daya kuma ina yi mishi fifita a kafar, duk da lokacin karfe shidda da rabi na yamma.
"Su Affan sun kusa yin hutu Khadija, ina jin ya kamata su dawo gida, a nema musu makaranta, mun bar wa su Rahma dawainiya"
Kai na jinjina a hankali cike da rashin jin dadi, saboda school din su Khalil tana da kyau sosai, ba na jin za a samu kamarta ko a Katsina ba ma a Ruma ba.
"Gaskiya ne, amma kam ba na son a cire su a makarantar can, ka ga a Ruma babu makaranta mai kyan wacce suke yi"
"To ya za a yi, su ma wannan din kaddararsu ce, zan yi waya da Dr Nura, ya karbo min transfer latter yaran da school clearance na makarantar"
Ban kai ga ba shi amsa ba, wata mata doguwa, mai matsakaicin jiki ta shigo, sanye take da abaya blue, ta rolling ɗankwalin abayar. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci akwai wayewa ta ilmi a tare da ita.
Cikin fara'a suka gaisa da Bashir ta yi mishi ya jiki, shi kuma ya amsata hade da yi mata godiya a kan dawainiyar da suke yi da shi. Kaina ta juyo cikin sakin fuska ta ce "Madam barka da yamma ya mai jiki?"
Murmusawa na yi kadan kafin na ce "Jiki Alhamdulillah, mun gode da dawainiya Allah Ya saka da alkairi"
"Babu komai. Ita ce za mu je tare" ta yi maganar hankalinta a kanshi
"Eh. Ta ki yarda ta bi su"
Yanzu kam ni ta kalla hade da murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tana fadin "Tana da gaskiya ai. Ko ta koma hankalinta ba zai kwanta ba, gara tana kusa da kai. Allah dai ya kara afuwa"
"Amin" muka hada baki a tare, kafin ya ce, "Ta shi ku je"
Ba musu na mike hade da saɓa Maama a kafaɗata na ce "Sai da safe, Allah Ya ba ka lafiya"
"Amin, na gode"
Na juya kan matar da take amsa waya, a haka ta yi wa Abbansu Khalil sallama muka fita tare.
Wata farar mota mai kyau na ga ta tunkara, har zuwa lokacin kuma waya take yi.
Da kanta ta bude min front seat na zauna, ita kuma ta zagaya driver seat ta zauna daidai tana gama amsa kiran.
"Baby ya sunanki?" ta yi tambayar hade da yi wa Maama wasa
"Sakeena, amma muna kiranta Maama"
"Ma Sha Allah! Bari mu je ta hadu da wata Maaman mai rikici"
"Ita ma wannan ai tana taɓawa" na yi maganar cikin murmushi. Daidai lokacin ne kuma take fita daga asibitin
"To ko duk haka Maama suke?"
"Ba mamaki" na amsata, lokaci daya kuma mu ka yi dariya.
Haka ta rika ja na da hira har zuwa lokacin da ta yi horn a kofar wani kyakkyawan gida, ba jimawa, wani yaro ya bude kofar gate. Muka silala. Dandanan yaran suka zagaye motar, suna mana sannu da zuwa cike da nutsuwa. Sosai na ji sun burge ni, na ji Ina ma ace ni ce, zagaye da yarana cikin kwanciyar hankali. Ko yaushe zan ga wannan ranar ni ma oho.
Da wannan tunanin mu ka shiga cool parlor nata, komai unique cikin tsari, babu wasu tarkace, take na ji wata nutsuwa na shiga ta.
Wani daki ta nuna min, ta ce in shiga in huta.
Dakin madaidaici ne, akwai katuwar katifa, net, ac. Wardrobe Mai biyu, Sai karamin TV. Toilet din ma madaidaici ne, amma sosai yake a tsabtace.
Maama na kwantar hade da dauro alwala, ina sallah yara suka kawo min abinci.
Kamshinshi da miyar ke yi, ya sanya ni cin tuwon duk da rashin son cin abincina.
Ina cin abincin ne ta kuma lekowa tana fadin "Zan ɗan kaiwa Abban Khalil abinci asibiti, mai kai mishi abincin ba ya kusa"
"Ba damuwa" na amsa ta.
Sai da na yi sallahr isha'i sannan na yi wanka, na canjawa Maama kaya zuwa marasa nauyi.
Duk surutan da ke tashi a falo ban leka ba. Haka na yi zamana a cikin dakina. Muna chat da Bashir
A chat din ne yake fada min matar da na zo gidanta sunanta Fatima, amma Maman Hana ake kiranta, matar Mustapha Sandamu ce. Na san Mustapha Sandamun, Sai dai iya wannan kawai na sani, ban san wani abu da ya shafe shi ba bayan wannan.
Sosai muka sha hira da dare da Bashir, hirar da ta sanya ni yin bacci mai dadi. Dakyar na tashi na yi sallahr asuba ina kan sallayata, na rika jin ɓuruntun matar gidan a kitchen, wata zuciyar na fada min in je wurinta, wata kuma na hanani.
Daga karshe dai na mike zuwa waje, sound din na rika bi har na gano inda take. Gani na ya sanya fadada fuskarta da murmushi ta ce "Amarya har kin tashi"
Kai na jinjina a hankali kafin na ce "Ina kwana?"
"Lafiya kalau, ya bakunta ya kuma Maama, sarkin rikici?"
Wani murmushin na yi kafin na ce "Tana bacci ba ta tashi ba. Akwai abin da zan taya ki"
"Babu komai wlh, ki koma ki huta"
Nan fa muka shiga jayayya, ta dage lallai sai in tafi in huta, ni ma na dage lallai sai na taya ta. Haka ta hak'ura ta bar min soya doya. Ina muna hira, abin da na fahimta tana da faran-faran sosai. A shekaru kuma za ta yi tsarar Maman Khalil.
Misalin bakwai muka kammala komai har da gyara kitchen din, zuwa lokacin kuma tuna yaranta suna ta shirin tafiya makaranta. Kominsu cikin tsari gwanin sha'awa, saboda ita ma ce min ta yi za ta je ta yi shirin tafiya aiki.
A falon na zauna ina kallon yaran su bakwai, dukkansu kama suke da juna, duk da na fahimci akwai tagwaye a cikinsu.
Ina zaune a wurin na ji kukan Maama, wannan ya sanya ni mikewa zuwa dakin, Sai da na, gyara mata jiki sannan muka fito, a lokacin kuma yaran break fast suke yi, wacce ake kira da Ihsan ce ta mike hade da nufo mu tana fadin "See Beautiful baby Ya Zeeyad" wanda aka kira da Ziyad din ya waigo yana kallon Ihsan da ke ta kokarin daukar Maama amma ta ƙi yarda
Kamar za ta yi kuka ta ce "Tana ƙin mutane ne?"
Kai na jinjina mata alamar eh ina murmushi
"Oh my God! I like her"
Kan dinning din muka karasa, da kanta ta haɗawa Maama tea ta shiga ba ta, wannan kam tana amsa, amma a kan jikina. Sai da ta koshi sannan ta kyale ta.
Daidai nan Mamansu ta fito cikin shirinta, doguwar rigar atamfa irin dinkin Hajiyoyin nan ya sha stone, dauri mai kyau, fuskarta farar powder ce kawai da lipstick, Sai kamshi Mai dadi. Kafardarta sagale da blue mayafi wanda ya dace da atamfar
"Kina nan dama?" ta yi saurin tambayata
"Eh" na amsa hade da murmushi
Hannu ta mikawa Maama tana fadin "Beauty zo mana"
Yadda ta makale hannun ne ya sanya dukkanmu yin dariya, ita kuma ta dora da "Daga yau ga Beauty nan, daga yau Beauty ba sunan ki Beauty ba"
Duk suka kalli wacce ake maganar a kanta suna dariya
"idan za ki je asibitin yanzu, ki shirya kafin in kai yaran nan school in dawo"
"To" na amsa. Haka suka fice gwanin sha'awa, ni kuma na shiga ciki don yin wanka, duk da ba ni da kayan canjawa.
Ina yin break kuwa ta dawo, Sai da ta jira na gama, sannan muka fita zuwa asibitin, a can ma ba ta jima ba ta baro asibitin.
Ni kam ina zuwa na iske su Abdullahi na kokarin kar Bashir toilet, bayan sun kai shin, na ce su bari kawai zan yi mishi duk abin da yake so.
A kan toilet din ya zauna hade da dora kafarshi mara lafiyar a kan wani dan stool, a haka na yi mishi wanka, ya yi brush, na sawo shaving stick na yi mishi shaving,kafin na karbo wasu kayan na canja mishi. Su kuma suka dauke shi zuwa gadonshi. Abincin da Maman Hana ta kawo na hada mishi ya ci kam babu laifi, sannan ya shiga tambayata ya wurin Fatiman akwai dadin zama kodai a canja min.
Zuwa lokacin dai ban ga wata matsala ba, don haka na ce a yanzu dai babu. Haka na ci gaba da debe mishi kewa, yayin da ƴan dubiyarshi basu yankewa a asibitin.
Duk wani abu da ya shafe shi, idan har zan iya ni ce ke yi.
Haka na ci gaba da zaman jinyanshi, kullum safe Maman Hana za ta kawo ni, yamma ta zo ta dauke ni, ba mu da matsalar abinci, har ragewa muke yi.
Sosai nake hidima da Bashir, bana barin shi da kazanta, ina kokarin kwantar mishi da hankali.