← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 44

Sashe 28

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba na ce ki daina yankewa yarinyar nan farce da reza ba, kar watarana ki yanke ta" ya yi maganar daidai yana jan burki a gabanmu

Shiru na yi kamar ba zan amsa ba, Sai kuma na ce "To" shi a kan yara to komai ba ka iya ba, zai ga kuma dai ba ka kula da su yadda ya dace. Ko a kan su Khalil dannewa kawai nake yi, amma kam da tuni mun yi babu daɗi. Zai iya shigowa ya iske su suna wasansu ya ce "Khadija kin ba yaran nan abinci?" sosai wannan tambayar ke ɓata min rai, ta ya zan dafa abinci in cinye kaf ba tare da na basu ba.

Har ya tuka keken zuwa gaba, Sai kuma ya dawo baya yana fadin "Khadija kin san kina da ciki kuwa?"

Wata irin faduwa gabana ya yi, yayin da na bude baki da idanu ina kallon shi, murmushi ya yi kafin ya ce "Cikin nan naki zai kai wata uku ko hudu"

Ni dai poster Kawai na ajiye yayin da shi kuma ya ja keken nashi zuwa gaba.

Idanuna na dauke daga kanshi na mayar kan Maama, wacce ba ta wuce watanni goma ba, Sai kuma na shafa cikina, kafin daga bisani na bi hannayena da kallo wadanda suka yi Fresh gwanin sha'awa

Bayan wannan fresh din da na yi ban ji wani canji mai kama da alamar ciki ba, musamman da ya kasance ba na period, kuma an ce idan mace na shayarwa wai ba ta period ba ta samun ciki.

"Tabbb!" na yi maganar hade da mikewa na bi bayanshi, idan har ya kasance da gaske ina da ciki aiko da Sai dai mu koma Abuja, ina zan iya da wannan abun kunyar ni Khadija. Mijin na fama a ganni da ciki kuma.

Zaune yake gaban wata loka yana duba wasu takardu, shigowata ce ta sanya shi dagowa yana kallo na

"Wai da gaske ina ciki?"

Sai da ya yi murmushi kafin ya ce "Idan ba ki yarda ba, gobe ki je asibiti"

Kama zan yi kuka na ce "aiko idan da gaske ina da ciki to gaskiya ka shirya mana komawa Abuja, ta ya zan fara kallon mutanen garin nan, kana fama da jinya ni kuma a ganni da ciki"

"Ciki kam ba nawa ba ne, me ye abun damuwa"

Fuska na kara narkewa kafin na ce "Kai nan ba ka komai ba, kana zaune kullum ace kuma Ina da ciki. Apart from that ma, duka fa Maama watanta goma"

Komai bai ce ba, Sai takardunshi da yake ta dubawa. Na shiga bubbuga kafa ina fadin "Kana ji na ka yi banza ko"

Takardun ya ajiye hade da janyo ni zuwa jikinshi kafin ya ce "Yanzu ina jin ki, me kike so?"

"Mu koma Abuja"

"Abuja kam Khadija sai dai ki kai ziyara, amma mun baro ta kenan, yanzu haka an sanya gidan a kasuwa"

Da matsanancin mamaki na tashi daga jikinshi ina kallon shi, kamar in ce wani abu sai kuma na fasa, saboda abin da zan fada din zai iya kawo sabani a tsakaninmu. Amma na tabbata da Maman Khalil na raye ba zai yanke wannan shawarar ba tare da sanin ta ba, amma ni idan ban da yanzu magana ta kama ba zai fada min ba.

Tashi na yi daga jikinshi tsam, saboda hayaniyarsu Khalil da na ji a tsakar gida.

A babban falo mu ka yi kicibus, dukkansu na raba su da jikina ina jin dadin dawowarsu, yayin da suka shiga kiciniyar dakkowa Maama tsaraba. Hakan yana tuna min da Ramla, saboda duk lokacin da suka dawo daga makaranta burki a dakina, wai za a ba Ramla tsaraba. Na dauka sun manta, ashe abun na ransu har yanzu, ga shi ana yi wa Maama.

Ruwan wanka na hada masu, kasancewar dukkansu sun girma, bana duk za su fita primary, na kwashe uniform din zuwa laundry basket, ina kitchen Affan ya shigo "Har an yi wankan?"

Kai ya jinjina alamar eh.

"To abinci fa?" na kuma tambayarshi

"Sai an jima zan ci."

Na juya kan Khalil da ya shigo ina tambayar "Kai ma abincin sai an jima?"

"Eh" ya amsa ni, kafin mu ka shiga labarin makaranta, yadda suke nuna suna jin dadin makarantar sosai yana sanya ni farin ciki. Kuma ni kaina ina ganin ci gaba sosai musamman bangaren addini.

Bashir ne ya tsaya kofar kitchen din, lokaci daya kuma yana dire Maama da ke kan cinyarshi tare da fadin "Yaran nan kin ba su abinci?"

Kamar in ce ban basu ba, Sai kuma na yi shiru, saboda Khalil ya riga ni amsa tambayar da fadin "Sai an jima za mu ci" shi ma bai kara cewa komai ba ya tuka kekenshi zuwa waje.

Wani abu na ɓacin rai ya tsaya min a wuya, dama da haushinshi na fito a kan zai sayar da gida ban sani ba. Ya kuma zuwa ya bata min rai da maganar ba yara abinci. Ban san me yake kallo na ba, ta ya zan yi abinci in hana yaran. A zuciyata Ina jin kaunar yaran tamkar ni ce na haife su, Sakeena ta fada min ga yaranta nan amana. A lokacin da take fada min wannan maganar, ba ta san za ta rasu ba, da wasa ta yi min ita, Sai ga ta ta zama gaskiya. Don haka na yi wa kaina alkawarin zan rike mata yara tamkar ita ce take raye kuma take rikon su.

Tare muka gama aikin kitchen din, su Affan suka yi alwala zuwa masallacin magriba, ni ma na shiga dakin don yin tawa alwalar, lokaci daya kuma Ina lallashin Maama da ke kukan dole sai ta bi su masallaci.

Bayan na idar da sallahr magribar, ina zaune kan sallaya ina ba Maama nono da take son yin bacci, maganar ciki ta fado min, take na yi sake da ni, jikina ya mutu likis,

Yarinya wata goma ciki wata hudu, kenan tana da 6month na samu cikin

"Wayyyo Allahna!" na fada cike da jin kunyar yadda zan rika hada ido da mutane, Bashir na zaune cikin keke ni ina kayan ciki turtsi-turtsi.

"Allah Ya sanya ma ba cikin ba ne" na fada a sanyaye, lokaci daya kuma Ina jin lallai gobe in je asibiti domin tabbatarwa.

Jin Maama ta yi bacci, na zare daga jikina a hankali, na kwantar da ita saman katifa, kafin na dawo na kabbara sallahr isha'i.

Ina idarwa su Khalil suka shigo, Sai muka runguda zuwa falo, na sanya mana abinci mu ka ci, mu ka yi home work, sannan na karbi haddarsu hade da yi musu gyararraki, Affan kam ana gama karbar haddar ya yi bacci. Shi ma Khalil ina tattare falo ya yi bacci. Sai da na kintsa ko ina, kafin na shiga tashinsu zuwa dakinsu.

Ina tsaka da tashin Affan Bashir ya shigo, ya zuba mana ido yana kallon yadda nake fama da Affan, saboda akwai lafiyar magagin bacci, dakyar na samu ya tashi. So hannayensu na rike zuwa dakinsu, daidai zan shiga dakin ya ce "Yaran nan sun ci abinci kuwa za su kwanta?"

"Sai dai yanzu da ka zo ka ba su" na amsa shi ba tare da na tauna maganar ba. Ko ta dace ko ba ta dace ba, ni dai na sako ta. Babu halin kuma mayar da ita.

Matar J ✍🏻
[12/22, 21:12] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 23*

A falon na dawo na same shi, kamar in yi banza da shi a kan maganar na shi abincin, Sai kuma na shige kitchen na hado mishi komai da komai na kawo mishi.

Na wuce dakina, yau gabadaya duk bata min rai yake yi, sosai raina yana baci a kan yadda baya sakani cikin ko wacce sabga ta shi, Sai dai kawai in ga ana yi, ko in ji an yi, sabanin Sakeena, da komai da shawararta yake yi.

Aiki gonarshi na bana ban san ko me ya samu ba, zakka da ya fitar ma ban san yadda ya fitar da ita ba, amma lokacin Maman Khalil na raye duk wadannan abubuwan da yake yin su. Ni kuma ina ta wahala a kanshi da yaranshi baya gani. Jin alamun shigowarshi ne ya sanya ni juya baya kamar ina bacci.

Yadda na ji kamshin turarurrukan kwanciyarshi ya cika dakin, na tabbatar har ya yi wanka.

Ina jin lokacin da ya sauka saman keken, ya hau gadona amma ban motsa ba.

Without anything ya shiga shafa ni, na ji kamar in buge hannun, takaicinshi ya kara kama ni.

Wannan dabi'ar tashi na masifar bata min rai, ta yadda bai dauki fushina a bakin komai ba, zai fahimci ina fushi, amma sai ya share kawai ya shiga harkokinshi, ga ni ni ba Sakeena ba, da ta iya danne abu, idan ban magantu ba; ban jin dadi.

Shi ya yi kidanshi, na kuma ya yi rawarshi, hakan kuma bai sanya ya damu ba, Sai ma kawai ya shiga baccinshi, kamar a duniya babu abin da ke damunshi.

Toilet na shiga hade da gyara jikina, na yi raka'a biyu hade da shafa'i da wutri, kafin na kwanta amma sai da na sanya Maama a tsakiyarmu, asubar fari kuma na shiga kitchen don yi wa su Khalil abinci breakfast da wanda za su tafi da shi school.

Shi kuma ya je ya hada kansu suka tafi masallaci, bayan ya dawo daga masallacin baccinshi ya koma, ni kuma na shiga taya su Affan shiryawa, ga Maama ta tashi ita ma, duk na zama busy.

Koda suka tafi ma ban huta ba, gyara kitchen Wanke-wanke, da gyaran gidan. Sai wajen 8:30am na kammala, sannan na zauna don yin break, bayan na gama kuma na shiga shirin zuwa asibiti.

Gefen gadon na zauna bayan na shirya, ina jin wani zafi a zuciyata, da ace ina da kudi kawai zan yi tafiyata ne ba ma sai na tambaye shi, amma ko don kudin asibitin dole ya sani.

Zaman nan na ba kwandalar da take shigo maka sosai yana damuna.

A hankali ya bude idanunshi hade da zube su a kaina, fuska na kara hadewa, shi kuma ya lumshe idon a hankali kafin ya yi doguwar mika, cikin muryar bacci ya ce "Me ya faru?"

"Asibiti nake son zuwa" na amsa murya a cunkushe.

"Yin me?"
Chapter 28 · 0% Book details