Sashe 4
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai yadda har yanzu da agogo ya nuna karfe bakwai na safe bai fito daga sashenta ba, kuma yana dawowa masallaci ya shiga bangaren nata. Yana kara tunzura min zuciya. Ni ba haka yake yi min ba. Yana shigowa ya dade 30mns.
Wani lokacin ma sai ya yi shirin office kafin ya leko ni
"Kai!!!" Na ji an fada a bayana, da sauri na saki cokalin da nake kwashe yam balls din cikin Mai, lokaci daya kuma na zabura bayan na saki siririyar kara
Da sauri ya rike ni yana dariya "Wallahi kin faye tsoro, to waye zai shigo har nan ya ba ki tsoro idan ba ni ba?"
"To dana san waye zai shigo din zan tsorata ne." Na ba shi amsa ina harararshi cikin fuskata mai nuna alamun shagwaba.
"Uhhhhhhh! Kamshin dadi" ya fada yana bubbude hancinshi
An yaba kaza mika, ta ce ga cinya
Sai na ji kaina ya yi fadi, kamar kitchen din ba zai daukeshi ba.
"Maman Khalil ta tashi ne?"
"Eh" ya ban amsa a lokacin da yake tsoma dunkulalliyar doya cikin kwai cike da kwarewa
"Ka iya girki fa"
"Maman Khalil ta koya min abinci da yawa ai, da ta tare muke shiga kitchen lokacin aiki bai yi min yawa ba"
"Ai fa" na fada a zuciyata a zahiri kuma cewa na yi "Ta kyauta"
"Zan dubo Affan ne, in bar ma kitchen din a hannunka?"
"Eh je ki dubo shi, zan kula da komai"
"Na gode"
A corridor muka hadu da ita, hannunta rike da lunch box guda biyu ta fito daga kitchen.
Sanye take cikin farar doguwar riga da aka yi mata a don duwatsu masu kyau.
Kamshinta mai dadi da kama jiki har yanzu yana manne da ko ina na dakin nata gami da jikinta
"Barka da safiya amarya, Allah ya sa ba hukuntani kika zo yi ba, jiya da yau duk na rike miki miji." Cikin murmushi take maganar lokaci daya kuma tana tafiya zuwa ainihin falonta
"Yarona na zo gani." Ni ma cikin dariyar karfin hali na yi maganar.
Yaran sanye cikin kayan makarantarsu gwanin sha'awa, dalilin da ya sa kenan ma na fitar da wayata na yi masu hotuna, don gaskiya sun burgeni tana kokari wajen gyara yaranta.
"Wai har Affan din ma makarantar zai je?"
Na yi tambayar ina kallonta
"To ya matsa sai ya je, shi ne Babanshi ya yi masu wanka ya shiryasu" Ta fada a lokacin da take ba Affan magani.
"Kenan tun dazu da ya shigo yaranshi yake shiryawa" na yi maganar a zuciyata, saboda ganin ba abin da nake zargi ba ne, duk lokacin da zai zauna a dakinta, kawai ji nake soyayya suke yi.
Tare muka fito da ita bayan ta gama shirinta da yaranta.
Hannuna daya na yi amfani da shi na bude wa yaran mota suka shiga
Bayan ta daidaita zamanta ne na dora mata Ramla a kan cinyarta.
Na dan ja kumatun yarinyar ina fadin "Ki yo min tsaraba."
ta wangale bakinta mai dauke da hakora hudu, kamar ta ji abin da na fada.
"Ki dauketa ta zauna da ke?" Cikin tsokana ta yi maganar
"Ashe zan biyo ki yau"
Mu ka yi dariya dukkanmu lokaci daya kuma ta murza kan mota cikin kwarewa ta yi hanyar fita.
Mamaki na yi sosai ganin yadda ya gyare kitchen din tsab kamar dai ni ce na gyara shi
Ina mamakin irin saukin kanshi, da kuma yadda yake yanke shekarunshi su daidaita da nawa idan muna tare.
Alhaji Bashir Balarabe Ruma, dan asalin jihar Katsina ne a karamar hukumar Batsari kuma a kauyen Ruma.
Mutum ne mai saukin hali, iya mu'amala da juriya a kan duk abin da ya sa gaba.
Yana da ilmi mai zurfi a ko wane bangaren sannan ya kan yi amfani da ilmin nashi ta hanyar da ta dace.
Yana aiki da ma'aikatar fansho ta kasa, sannan yana kasuwanci na sayi da sayarwa, bugu da kari babban manomi ne a kauyensu.
Shekarunshi zasu kai arba'in zuwa da daya in da yake da yara uku biyu maza sai mace daya wacce matarshi Sakeena ta haifa mishi.
Mace mai kokarin boye damuwarta, iya zama da mutane kawar da kai hade da kawaici.
Tana da ilmi sosai musamman na addini, don har yanzu Sakeena na zuwa Islamiya Asabar da kuma Lahadi, a ilmin zamani kuwa tana da degree ne a bangaren education, tana matsayin vice principal a Wata makarantar private da ke cikin garin Abuja.
Ita ma yar asalin garin Ruma ce, kila shi ya sa wani lokaci nake ganin kamar suna kama da mijinta.
Alhaji Bashir Ruma, dogo ne mai matsakaicin jiki, sannan yana da hasken fata da take nuna irin jin dadin da yake ciki, yana da matsakaicin gemu da saje wanda ya zagaye fuskarshi ya kuma kara mata kyau da cikar haiba
Tsagenshi na rumawa wato biyu-biyu a gefen kunnensa ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba.
Ita ma Sakeena haka yanayin jikinta yake, duk da yar kibarta mai ban sha'awa ta kan rage tsawon nata.
Yanayin hasken fatarsu daya da mijinta, zanen fuskarsu ma daya, bambancin kawai nata ya fi fita sosai da kuma yi mata kyau.
Ni kaina zanen nata burgeni ya ke sosai, yaranta uku babu wanda ba a yiwa zanen ba. Su ma sosai zanen ya yi musu kyau. Musamman Ramlah
Yau dai wannan ranar tawa ce don kuwa Bashir wunin ranar zuwa masallaci ne kawai ke fitar da shi, saboda koda su Maman Khalil suka dawo bai yi cikakken mintuna talatin tare da su ba. Ga shi yaran babu wanda ya zo part dina, har suka wuce Islamiya. . Maganar irin farin cikin dana tsinci kaina a wannan ranar ma ba zai misilti ba. Na rika jin, ina ma ace kullum hakan ne ke faruwa.
ina ma ni kawai ce da Bashir , lallai dana mori rayuwar amarcina, na aje tarihi mai yawa kuma mai dadin bayarwa.
Karfe takwas na dare na fito cikin kwalliyata dana tabbatar za ta ja hankalin mijina.
Riga ce mai laushi baka, ta wuce gwiwa kadan tana da siririn hannu, yau so nake in ba shi mamaki.
Sai da na tabbatar ko ina dake bangaren nawa ya yi fes ga kamshi mai dadi mara hawa kai.
Sai dai me? Yana dawowa masallaci ya zarce bangaren Gimbiyar tashi.
Yau ne, gobe ne har goman dare bai shigo ba, ɗan baccin ma da nake yi da, idan haka ta faru yau kam kwata-kwata na kasa yi, zuciyata tafasa kawai take yi, ina kuma shirya irin yadda zan nuna mishi bacin raina.
Matar J ✍🏻
[12/16, 12:06] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 4*
Duk yadda na kumbura fam ina jiran shi, lokacin da ya shigo sai na ka sa aiwatar da komai, idan ka dauke zumbure-zumburen baki da na rika yi. Kila shi ya sa komai bai ce ba, ya nemi makwancinsa. Hakan kuma ba karamin kara bata min rai ya yi ba. Shi ya na yi kuka mai yawa kafin bacci ya yi awon gaba da ni.
Da safe ma haka nan nai ta ayyuka rai babu dadi, ya kuma lura da hakan sai dai sam bai tambaye ni ba, ni ma kuma na shareshi
A haka muka gama kwanakinmu biyu tare da shi, ya koma dakin gimbiyarsa.
Ranar da ya koma ɗakinta, zaune nake a gaban TV da misalin karfe biyar na yamma , Sai dai hankalina sam baya gurin TV din.
Shawarar yadda zan bullo wa matsalata nake yi.
Kila wani zai ga ba abun damuwa ba ne, amma ni gaskiya ni yana ci min rai,, kamar kashin wuya haka ya tsaya min.
Yau da yake a dakinta yake, tun 10am da ya leko ni bana jin ma ya yi 10mns masu kyau ya fita har yanzu ko keyarsa ban kara gani ba. Kila ko don ya ga ina fushi ne oho. Idan ma haka ne ai kamata ya yi ya lallashe ni, ba wai ya yi banza da ni ba.
"Mtswww!" na ja dogon tsoki, lokacin da na tuna yadda yake sintiri ɗakinta, idan har yana dakina ne to ka'ida ne ya ziyarci matarshi sau uku a rana koma fiye.
Amma ni yau sau daya na samu ya leko ni.
"Gaskiya dole in yi mishi magana tun kafin matsalar ta girmama"
Na fada a zuciyata hade da gyara zamana. Lokaci daya kuma wayata na janyo hade da kiran Badiyya. Cikin sa a kuwa ta daga. Muka gaisa, sannan na shiga kora mata abun da ke damuna. Cikin rashin jin dadi na ce "Kawata kar ki ce na faye korafi, amma wlh auran nan ya fita a kaina. Haka auran mai mata yake ne? Daga wannan problems din sai wannan?"
Cikin salon kwantar da hankali Badiyya ta ce "Haka zaman aure ya gada Khadija, musamman mu masu abokiyar zama, don haka hakuri za ki yi, wadanda suke su kadai ma haka suke fama. Kuma na sha fada miki hakan ai."
Cikin dacin zuciya na ce "Nawa ya zo daban Badiyya, abin da na sani Amarya mai irin kwanakina bai kamata ace ta fara fuskantar irin abin da nake fuskanta ba, kiri-kiri fa yake nuna son matarshi a gabana. Ni na ma rasa dalilin da ya sa ya auro ni"
Yanzu kam gajeruwar dariya ta yi hade da fadin "Kauna mana ta sa ya auro ki"
"Gaskiya ban yarda ba, shi dai kawai ya auro ni don ya rika bata min rai" na ba ta amsa.
Kafin ta ce wani abu na kuma na cewa "Wai kin ga matarshi kuwa Badiyya, wlh kyakkyawa, wayayya ta sha boko ta koshi, Sai kin ganta komai na ta a can-a can"
Wata dariya ta kuma yi kafin ta ce "To da ya kike son ganin ta? Wata mummuna kucaka?"
"Ni dai abin da na dauka kawai shi ne amarya dole ta fi uwargida da wasu abubuwan, kuma miji ya fi son ta. Ba haka muke karantawa a littafi ba. Uwargida mai baƙin hali, Sai a auro amarya ta kwace gida?"