← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ban san me zan ce ba, yadda za ki fahimta" Na yi maganar hade da rufe bakina dalilin hammar da na yi.

"Ki fada min komai zan fahimta." ta amsa ni

Na ɗan ja siririn tsaki "Ni lafiya lau muke zaune da ita, tsawon wata uku da mu ka yi tare ko mugun kallo ba ta taɓa yi min ba."

"To shi fa mijin naki?" Umma ta yi saurin tambaya

"Shi ma haka"

Na ba ta amsa

"To me ye damuwarki?" Ta yi tambayar hankalinta a kaina

"Umma dama haka auran mai mata yake?" ni ma na tambayeta ina kallonta

Ita ma kallona take, ba ta yi alamar magana ba, wanda hakan ya nuna min tana neman karin bayani a gurina ne

"Ki gode Allah da ba ki auri mai mata ba Umma wallahi duk yadda kike ganin kina da matsaloli a gidan auranki ke kadai to basu kai ace kina da kishiya ba. Ni kam na yi danasanin auran mai mata "

"Ni ki fada min matsalar, ba zagaye-zagaye ba"

"Umma sam ba ni da ƴancinkaina, sai abin da matarsa ta ce, ba a shawara da ni sai dai in ga ana yi, ke ko wani abu zai min sai ya biyo ta hannun matarsa, yana tare da ni amma hankalinsa na gurin matarsa da yaransa, ke kam dai na zama kamar wata tunkiya a garken awaki. Ko dama haka ake yi? " Na rufe maganar da tambayar ta, lokaci daya kuma ina tabe bakina.

Umma ta ɗan murmusa kadan, murmushi dana kasa gane dalilishi

Kafin ta ce "Ki yi duk yadda za ki iya ki zama kamar ita, sannan ki yi hakuri, ba da gaggawa ake taka matsayi mai girma ba, kafin ta zama haka sai da ta kwashe tsawon shekaru, kin ga kuwa ke da kike da kika zo jiya, ba ki isa ki zama kamar ita ba. Ki bi komai a hankali "

" Kin ga Umma hatta danginshi sai abin da ta ce, wurin bikin nan duk shawara da ita ake yi"

Ta kalle ni da alamun damuwa kafin ta ce "Duk wannan kar ya dame ki, a hankali za ki iya zuwa matakin da take, kila ma ki wuce ta. Abin da kike bukata kawai shi ne kyautatawa, girmama na gaba da ke. Sannan girmama kowa. Da tsayawa matsayinki, ba ruwanki da yawan tsegumi ko gulma. Babu girman kai, Sai girmama kai. "

Shiru na yi hade da nazarin maganganun Ummana, tabbas wadannan sune abubuwan da Maman Khalil ta rike, babu dadi babu kari. Saboda kowa bai raina ta ba, kuma ba ta raina kowa ba.

Haka muka rika tattaunawa, har bacci ya dauke ni.

Cikin bacci na rika jin hayaniya da karar taɓa abubuwa.

A hankali na bude idona, wanda bacci bai isa ba, kasancewar jiya bacci bai dauke ni ba sai wajen uku saura na dare.

Saboda hirar da mu ka rika yi da Umma. Ko bayan hakan ma na dade ina nazarin duk wasu maganganu da ta fada min

Duk abin da Hasashena ya ba ni, sabanin haka na taras, yayin da Umma ta kara tabbatar min da cewa Hasashen nawa gaibu ne, ba lallai abin da na Hasaso ya kasance gaskiya ba, kamar yanzu ma.

Ni abin da na dauka shi ne, a matsayina amarya, to zai kasance hankalin mijina yana kaina, zai tarairayeni, zai ji da ni, kamar dai yadda na sha fada tun farko.

Amma me ya sa ban samu wannan ba?

Kodai ni ce ban iya tarairayar miji ba?

"Wannan ba gaskiya ba ne." na ba kaina amsa, hade da yunkurawa na tashi zaune a kan katifar.

"Me ye bana mishi? Ina mishi komai, bana barin kazanta ko datti a ko ina.
Ina kiyaye ganinshi da jin shi. Girki ma na dage sosai nake kokari, duk da dai ni kaina na san ban kamo kafar Maman Khalil ba a nan bangaren"

Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, a bayyane na fadi

"Mata ce kamar mayya, komai ta iya, ni ban taba ganin mace irinta ba"

Jin almar za a shigo dakin ne ya sa na yi saurin yunkurawa na daga net din ina kokarin fita.

Maryam ce kanwata

"Aunty ashe ma kin tashi, dama Ummanmu ce wai in zo in tashe ki"

"Na tashi" na ba ta amsa, lokaci daya kuma muka fita tare

Bayan na idar da sallah, daukar tsintsiya na yi, na, share gidan fes, sannan na shiga kitchen inda Umma ke saka danwake

"Tsawon wata uku kenan ban ci danwake ba Umma ba" Na fada hade da janyo karamar kujera na zauna gefenta, tare da fara saka danwaken a cikin tukunya.

"To me ya sa, ba kwa yi ne?"

"Ni dai ban taba yi ba, ban sani ba ko Maman Khalil ta na yi"

"Oh kowa girkinsa yake yi"

Kai na jijjiga alamar Eh.

"Kina ji na?" Umma ta yi maganar hade da dakatawa daga saka danwaken alamar maganar na da muhimmanci.

"Allah ya hada ki da kishiya mai wayo, wacce ta san kanta"

Na yi saurin kallonta alamun ina neman karin bayani.

"Magana ta gaskiya, shi ne akwai aiki a gabanki, kafin ki taka matsayin da kishiyarki take kai yanzu."

Ta dan tsagaita, yayin da ni kuma nake bubbuga kumfar danwaken da ta taso.

"Natsuwa za ki yi, ki gano a ina gazawarta take, sannan ban da kwaikwayo, ya zama ke ma kin zo da naki sabon salon da zai zama bako a gurin mijinki. Wannan shi ne kawai"

"Me kike nufi da haka?" Na yi tambayar a lokacin da nake tsame danwaken

"To me kuma kike son in fada miki, komai sai an yi miki dalla-dalla ne?"

"Haka ya kamata a rika yi, musamman a kan macen da za a kai gidan kishiya."

Na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma murmushi na yi, ina yaba alkunya irin ta iyayenmu, wato komai sai su bamu shi a dunkule, yayin da muka warware za mu samu abubuwa da yawa masu muhimmanci. Duk da wani lokaci mu kan warware abun ba daidai ba, ya fi ace an warware mana shi ta yadda za mu fahimta.

Ni na raba danwaken na sanyawa kowa, ni ma na ja na wa, ci nake amma kuma bitar maganar Umma nake yi.

Zuwa karfe takwas gidan shiru sai ni, kanwata Maryam da take zana min lalle, Sai kuma Umma da ke ta faman hada min tsaraba.

Hira muke da Maryam a hankali wacce da yawan hirar a kan kannenmu ne, Sai kuma Yusrah, daya kanwar tawa da take aure a Kaduna.

Ita kam ta jima da aure, saboda ta ma riga ni auran, tun mahaifinmu na da rai aka yi mata aure, ni kuma sai da na kammala NCE.

Zuwa karfe biyu, na fita shar da ni, kamar yau ne za a kai ni gidan miji, kunshina ya yi kyau, haka ma kitson da Umma ta yi min zanen kwance, ya fito da fuskata fayau.

Doguwar riga mai ruwan madara na saka, na zagaye fuskata da dankwalin rigar ina jiran zuwan Abbansu Khalil

Ba jimawa kuwa ya iso, bayan sun gaisa da Umma ya yi mata ihsani, mu ka yi sallama, sai Airport.

Matar j
[12/16, 20:12] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 7*

Karon farko da na fara shiga jirgi a rayuwata, amma kuma ba na ɗoki, murna ko farin ciki. Hasali ma raina a bace yake, komai baya min dadi, ji nake kamar in ce a tsaya in sauka.

Shi kanshi na ga ya fahimci hakan, duk da komai bai ce ba, idan ka dauke hannuna da yake cikin na shi yana murzawa a hankali.

Duk bacin ran nawa, na san baya rasa nasaba da yadda nake tunanin yau Maman Khalil za ta amshe min miji, na san yau za ta fanshe duk wasu kwanaki da ya yi a wajena.

Gaskiyar Ummanmu ne, Maman Khalil mace ce mai matukar wayo, iya mu'amala da zaunawa a rai.

Ta san yadda ake tafiyar da miji, da yi mishi abin da zai tsaya mishi a kwakwalwa da zuciyarshi.

Sosai nake tausayin kaina, idan na tuna irin kalubalen da ke gabana.

"Tea or coffee?" Ma'aikaciyar jirgin ta yi min magana cikin wani irin turanci da take yi ma Tajweedi

Shiru na yi, na kasa gane me ta fada a kalmarta ta biyu, ta fari dai na san tea ne, kuma ai kullum ma sai na sha shi.

Don haka sai na yi saurin cewa "Coffee" da irin sallon da ta furta.

Cikin yan dakikai, aka kawo mana abin da muka bukata

Tea mai kauri na ga an mikawa Abbansu Khalil,, yayin da ni kuma aka mika min abu baki.

Na kurba a hankali, hade da kallon Abbansu Khalil, shi ma ni yake kallo, da alama yana son ganin reaction dina ne

Idanuna na dauke daga kan fuskarshi, zuwa wani bangaren, na rufe idanuna gam sannan na hidiye abin da na kurba.

Gudun kar in yi abun kunya na rika sipping abun kamar magani.

Da kyar na sha rabi, na aje sauran. Ina danasanin rashin cewa a ba ni tea dan gida.

Misalin biyar muka sauka Abuja

Saukar mu ke da wuya na hango Maman Khalil sanye cikin wani hadadden leshi mai ruwan goro

Dinkin riga da siket ne, ya zauna jikinta das, ta sha sarka da yan kunne masu kyau da tsada.

Eye glass din da ta sanya ya kara mata kyau sosai, idan dai kwalliya ce to Maman Khalil kam ta iya sai madalla.

Yaran ma fes dasu cikinsu kaya masu kyau da tsada

Tun daga inda take tsaye take aikawa mijinta sakon murmushi.

Shi ma hankalinshi duk yana kanta, kamar ya ture mutanen da ke gabanmu ya isa gareta

Tuni kishi ya turnekeni, zuciyata ta yi kunci, raina ya dagule, ji nake kamar in dora hannu a kai, in yi ta zumduma ihu.

Gaskiya babu abin tashin hankali a gurin mata irin ka ga mijinka da wata, kuma ace mallakinsa ce,, musamman irin su Maman Khalil,, kishi da irinsu ma bala'i ne.

Yaransa ne suka fara isa gareshi a guje cike da tsantsar farin ciki, shi ma cikin farin ciki yake dagasu, hade da yi masu tambayoyi, har zuwa lokacin da ya isa gurin Maman Khalil da ke tsaye ta na murmushi.
Chapter 7 · 0% Book details