Sashe 24
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da aka cika sati mai gyaran ya zo, cikin ikon Allah gyara ya yi, farin ciki guna ba a magana. Ba ni kadai ba duk wani masoyinshi ma. Kafar dai ba ta takuwa, Sai dai a kan keken nan, amma yana iya dagata da kanshi, har mikewa ma ya hau keken duk yana iyawa.
Ban san me ya faru ba, na ji dai an ce aje a share mana gidanmu, wai can zamu koma. Cikin kwana biyu kam aka gama gyare shi tsab muka koma. Sai na ji na fi sakewa, musamman wajen kulawa da shi. Saboda a can akwai idanun mutane, ba komai nake iya yi mishi ba.
Sosai na tattara hankalina a kanshi, duk wani abu da na san zai sanya shi farin ciki kokarin yi mishi nake yi.
Auran mijin mamaciya
akwai kalubale sosai, saboda kullum bakinshi a kan radadin yadda yake ji ne game da rashin matarshi, tun abun baya damuna har na rika jin babu dadi, daurewa kawai nake ba na nuna damuwata. Ni kaina ina kewarta, ballantana kuma shi.
Wani lokaci zan dage in yi masa abu, amma sai ya ce "Ina ma Sakeena na da rai na tsinci kaina a wannan halin, na san zan samu kulawa ta musamman"
Idan na ce ni bana kula da shi, sai ya ce wai shi ba haka yake nufi ba.
Kuma iyakar bakin kokarina ina yi, bana barinsa da datti. Yi mishi wanka, kai shi toilet, fitowa da shi, abincinsa, kasancewar ba komai yake ci ba.
Amma a hakan dai korafi yake. Ga ni dai yake da matarsa na da rai za ta fi kulawa da shi a kaina. Ga kafar tana yin wasu baroro kamar ya kone, wai sai aka ce daji ne, haka aka shiga karbo magunguna, amma ni ba na ganin wani ci gaba, kullum ciwon da sabon salo yake zuwa.
Yau Rahma da maigidanta za su kawo su Affan duba jikin Babansu. Shi ya sa tun safe nake ta lilo a tsakar gida, ba ni kitchen ba ni daki, ba na wajensa, ga Maama da rikici, idan ta fara kuka, kamar ana kwakule mata idanu. Ga kiwar tsiya, ba ta yarda da kowa, daga ni sai Jamila da Babanta, su din ma idan tana borinta basu isa su dagata ba.
Jamila na zuwa ta taya ni raino, don Zainab kanwata tuni ta koma gida.
Ina kitchen ina fama da aiki, ga Maama na ta kuka, ashe shi kuma yana kirana, zan kai shi toilet ban ji ba saboda kukan Maama.
Ban fita ba, har sai da na gama hada miya, dakinsa na nufa ba wai don na san yana kirana ba.
Sai don kawai in leka shi.
Ina shiga kuwa sanda tsakar ka.
Tun da na shiga yake bala'i kamar dama Jirana yake, ya hanani ma in yi magana.
Har sai da na jira ya kai aya sannan na ce "Ka yi hakuri, ban ji kiranka ba, Maama na kuka, kuma ina kitchen ba na son su Affan su iso ban kammala abinci ba."
"Ki yi min shiru, tun da Sakeena ta rasu na tabbata na yi rashin da ba zan iya cike gurbinsa ba, yarinya daya kawai amma kin kasa kula da ita, ki bar ta ta yi ta kuka, aiki ki kasa gamawa da wuri."
Daurewa kawai na yi kafin na ce mar "Ka yi hakuri don Allah, mu je in kai ka toilet din."
Da kyar na samu ya yarda na taimaka masa, sai da na tabbatar na yi mishi duk abin da ya dace sannan na koma kitchen, a lokacin kuwa miyata ta fara konewa.
Bayan na motsa miyar hade da rage gas, cigaba da zagaye kitchen din na yi da goyon Maama so nake ta yi bacci.
Yayin da a zuciyata nake jin wani irin zafi, ku san kullum Baban Khalil sai ya nuna gazawata a kan abu, kamar haushina yake ji, abu kadan sai fada, ya dauki alhakin mutuwar matarsa ya dora a kaina. Kamar ni ce na kashe ta. Bai san ni ma ina jin babu dadi a kan mutuwar tata ba
Komai na yi, bana burgesa, sai ya ga abun kushewa.
Ban da ina jin tsoron bakin mutane da na yi tafiyata na ba shi guri. Kar ya kai ni makura in fara tankawa.
Misalin karfe biyu na rana su Rahma suka iso, wannan ya tabbatar min da tun asuba suka dakko hanya.
Sosai na ji dadin zuwansu, bayan gaishe-gaishe, suka yi sallah, ni kuma na kai wa su Bashir abinci shi da mijin Rahma. Su Khalil kam tuni suna gidan kakanninsu.
Rahma zaune tana cin abinci ta ce "Aunty Ramla haka ƙafar Abbansu ta kara yi?"
Cikin jimami na ce "Wlh fa, an ce wai daji ne, ana ta magani, amma babu karayar yanzu"
"Yanzu wannan ciwon ana magani kenan? kalli fa yadda kafar ta zama"
Kai na jinjina alamar eh, saboda ni kaina ba na ganin wani ci gaba, kawai dai ana magani ne, amma kullum kafar kara caɓewa take yi, duk da wani farfashe. Ga shi ta kumbura sumtum, nan kashi nan fitsari.
"Ya kamata a fitar da Abbansu waje Auntyn Ramla, wannan ciwon akwai daga hankali. Managarcin mutum ingarma kamar Abbansu, amma kalli yadda ya koma, komai sai yana zaune za a yi mishi. Gaskiya hankalina ya tashi. Idan kawata na da rai ba za ta amince ce ba. "
Komai ban ce ba, Sai hawaye da nake sharcewa. Ban san me ya sa mutane suke cewa idan Sakeena na da rai ba za ta yarda ba. To idan ba ta yarda ya za ta yi, ko za ta cire mishi ciwon ne? Ni ban san me zan yi ba kuma?
" Kalli ke ma duk kin rame kin yi baƙi?" cewar Rahma
A zuciyata na ce "Ba dole ba," ( wai arne ya tambayi pastor Idan ya mutu zai shiga aljanna? Pastor Ya ce ba dole ba, mutum da gidan uban shi) ai dole in yi rama, abubuwa da yawa ne a kirjina. Jimamin mutuwar Sakeena da Ramla, ga ciwon Bashir, ga jinya, ga tsotso, ga rigimar Maama. Ga ta Bashir da kullum nake zama mai laifi.
Haka muka rika hira da Rahma wata ta kwantar min da hankali, wata kuma ta tayar min da shi.
Da yamma na raka Rahma gidansu Sakeena, daga can muka wuce gidansu Bashir. A can na samu su Affan lan ci wasa da rashin ji an gaji. Sai magriba muka baro gidan. Inda duk zamanmu tattaunawar dai a kan ciwon Bashir ne.
Da safe ma haka aka dora, mijin Rahma ya dage lallai a fita da Bashir zuwa kasar waje
Wannan karon kam basu ki ba, amma sun ce wai a jira nan da sati biyu, akwai sabon mai maganin da aka samu, idan abun bai yi ba, Sai a fita wajen.
Haka su Rahma suka koma duk jiki a mace
*******
Bayan tafiyarsu Rahma kam ciwo sai dai godiyar Allah. Amma naman ƙafar Bashir zafkewa yake da kanshi yana faduwa. Fadin tashin hankali da muke ciki ba sai an fada ba. A haka aka kwashe shi zuwa babban asibitin Katsina.
Kwanansu daya mu ka bi bayansu.
Tun bayan da na isa asibitin mu ka gaisa komai ba kara cewa ba. Damuwa ta ishe ni, a shekaruna 23 abubuwa sun haye min. Na rasa da wanne zan ji. Yanzu kam da nake kallon Bashir kwance cikin jinya, ji nake kamar in ce ya ba ni in karbar mai ya dan huta.
Ga Maama ta ishe ni da fitina sai mu fita waje, haka na mike zuwa wajen, ina rarrashinta, bayan ta yi bacci ne na kuma dawowa ɗakin. Zuwa lokacin ne kuma su Aunty Habi suka rika fita yin alwalar la'asar. Ni kam dama ba sallahr nake yi ba.
Shi ya sa na koma kan tabarma na zauna, hade da yin shiru, jin muryar Bashir yana kiran sunana ne ya sanya ni saurin dagowa. Saboda na dauka bacci yake yi.
Da sauri na isa wurinshi ina fadin "Kana son wani abu ne? Sannu Allah Ya ba ka lafiya"
Maimakon ya amsa min, Sai ya zuba min ido yana kallo na, ganin ba zan iya jure kallon ba ne ya sanya ni janye idanuna.
Hannuna ya guda daya ya saka cikin na shi, a hankali ya ce "Allah Ya yi miki albarka Khadija, na gode da dawainiyarki a kaina"
Komai ban ce ba, hakan ya sa ya dora da "Ki daina tayar da hankalinki, kalli yadda kika koma Khadija"
Hawayen da nake ta kokarin dannewa suka gangaro min, cikin muryar kuka na ce "Hankalina ba zai kwanta ba Bashir muddin kana cikin wannan halin, idan na ce ma zai kwanta karya nake yi. Babban burina in ga ka samu lafiya koda kuwa haka yana nufin za a cire kafar nan. A hakan ma ina sonka"
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Kirjina yana zafi Khadija, ji nake ina ma ace ni ma na bi Sakeena, ga shi yanzu ina rayuwa cikin ba tare da ita ba. Na rasa wanne abu ya fi min zafi tsakanin jinyar nan da rashin Sakeena. Wani lokaci in ji kamar wasa, wani lokaci kuma in gasgata ba ta a duniya. Da ace ni ma na rasu da duk ba ki shiga wannan tashin hankalin ba. "
Hannunshi da ke cikin nawa na matsa a hankali kafin na ce" Ina bukatarka a raye, ba ni kadai ba, muna da yawa ka daina fadin haka. Mu yi addu'ar ka warke "
" Yaushe? Khadija yaushe zan warke kullum ciwon gaba yake kara yi"
"Bawa ba ya fitar da rai daga rahamar Allah Bashir, Sha Allah za ka warke, za ka samu lafiya"
Duk mu ka yi shiru, shi ne ya katse shirun namu da fadin "Na ce su yanke kafar nan, amma sun ce a'a, wai kashin bai mutu ba"
Sabbin hawayen da ke zubo min na dauke, kafin na ce "Allah Ya zaɓa abin da ya fi alkairi. Bamu da wata dabara"
"Miko min Sakeena" ya yi jin Maama na kananan kuka
Bayan na sauke ta kan cinyarshi ya dorata yana kallon ta. Ita ma shi din take kallo. Murmushi ya yi kadan kafin ya ce "Kin faye rigima Sakeena, takwararki ba haka take ba"