Sashe 2
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To me ya faru?" ta tambaya.
"To duk ba haka tsarin gidan da abincin gidan yake ba. Shi ya sa ma ban gwada zan yi ba. Gara ma ranar can dana gidan ba kowa na gwada yin wani abu, na manta ma sunanshi ban iya ci ba wallahi, na faki ido na zuba a bola. Ko ban iya ba ne, ko kuwa dai haka yake ba dadi oho?"
Wata dariyar ta kuma saki, hade da fadin "Amma ke ba sai ki zo da na ki sabon salon ba"
"Ina jin tsoro Badiyya, in yi bai yi dadi ba, kin ga ai na fado kenan."
"Wlh kam. Ga shi ba ke kadai ba, zama da kishiya akwai kalubale Khadija. Gara ma ke, abincinki kike yi ke kadai. Amma mu masu gabadaya muke tantancewa. Yau yara su ce kin yi basu koshi ba, jibi su ce babu dadi. Citta su ce ba ki gama da wuri ba. Kullum da sabuwar tsirfa."
Haba na rike kamar tana kallo na, kafin na ce" Wato tukunyar dai tare ta tafasa? "
" Wlh kam. Don yanzu haka raina bace yake, kiranki ne ma ya dan warware ni. Yaron can Abbah sarkin gadara, shi ne yake yi min abin da ba na jin dadi, kai tsaye ki ji shi a kitchen dina yana min bincike, kuma ba damar in yi magana, Sai ace wai yaro ne in yi hak'uri zai bari"
Cikin sigar lallashi na ce "ki yi hak'urin to, komai zai wuce sha Allah."
"Allahu Ya sha" ta amsa, kafin mu ka yi sallama. Duk jikina a mace, ashe haka aure yake, ko wanne da irin kalubalenshi, ba masu kishiyar ba, ba wadanda suke su kadai ba. Kanwata Yusrah da take ita kadai ma a gidan miji, ita ma da tata matsalar.
Haka na ci gaba da tattauna kalubalen da zuciyata, lokaci daya kuma Ina aikin tuwona.
Matar J
[12/16, 11:29] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 2*
*MATAR J*
Tun da na gama miyar shiga goma fita goma zan yi a kitchen din sai na bude tukunya na dauki ludayin na dangwala a hannuna na lashe, abun ka da ban taba gwada yi ba so dai nake in tantance, kar Ogan ya ci ya raina min.
Tuwon ne dai ya yi tauri da yawa ba kamar yadda mamana take yi ba, shi ba mai tauri ba, kuma ba mai taushi ba, yana nan a tsakiya dadin ci.
Amma ni nawa aka jefi kato ba abin da zai hana bai ji ciwo ba.
"To me ya sa?" Na tambayi kaina.
Kiran layin Ummata na yi
" Ummah!" na fada bayan na yi sallama hade da gaishe ta
"Na'am" ta amsa
"Tuwon shinkafa na yi, ya yi tauri bai yi irin naki ba" Na ta fi kai tsaye akan abin da nake so
"To ba sai ki dakko littafin da kike rubuta kalolin girki ba, ki duba yadda za ki gyara"
Shiru na yi, ina tuna yadda take jin haushin littafin koyon girkin can nawa, lokaci daya kuma Ina tuno yadda take fada
"Aikin banza da wofi, kullum kina like da TV wai koyon girki, idan za ki tsaya ki koyi abu a zahirance ki tsaya ki koya, wannan rubutun ba inda zai kai ki ba, ni dai kika sanya aka zageni a kan ba ki iya girki ba, sai Allah ya saka min."
Haka take cewa duk lokacin da nake rubuta yadda ake wani girkin a TV ko a media
" Kai Umma, yanzu fa kin san ba kamar da ba ne, idan ban iya wannan abinci zamanin ba akwai matsala wallah, mazan yanzu yan zamani ne ba Yan gargajiya ba" Haka nake ba ta amsa.
"Wane namiji ne zai siya miki kayan girkin da kike rubutawa? Wani ma bai ko taba jin sunansu ba, sannan wane namiji ne zai rika siya miki kaza kina rarike cikinta kina tura dankalin turawa da su hanta da koda? Wane namiji zai tsaya siya miki kwai kina dafawa kina dode duwawun kaza? Sannan wane namiji zai fita tun safe ya dawo da yamma ki aje mishi cake ko wani burodi can da danyen tumaturi? "
A duk lokacin da ta fadi haka dariya nake yi, a zuciyata ina fadin "Ba ganewa za ta yi ba."
Ashe dai ni ce ba zan gane ba.
"Kin ji me na fada dai ko?" ta katse min tunanina
"Eh"
"Yauwa" Ta yanke kiran
Fita batun tuwo na yi, na gyare kitchen dina fes kamar ban yi aiki a ciki ba.
Wanka na shiga, bayan na fito na shimfida sallaya don sallahr azahar.
Bacci ne cike da idona, don haka a kan sallayar na kwanta bayan idar da sallahr.
Bacci kuma ya yi awon gaba da ni.
Cikin baccin ne na ji kwankwasa kofa.
A firgice na tashi na nufi kofar
Khalil ne tsaye cikin kayan shan iska na yara, kamshin turarensu na yara da turaren mamarshi tuni ya cika kofar tawa.
"Khalil, kun dawo ne? Me ya faru?" cikin muryar bacci na jero mishi tambayoyin.
"Momyna ce ta ce idan kin rage abinci wai ki san mana kafin ta girka mana"
Hannu na kai cikin sauri na murje idanuna don gasgata mafarki nake yi, kodai gaske
Tuwona mai taurin can zan ba ta? Matar da ko ruwan zafi ta dafa sai ya yi dadi. Shi ya sa bana son ba ta abincina, ina jin tsoro ta rika min kallon ban iya girki ba
"Zo ka zauna, sai in daukar ma kada ka baras ko" na yi maganar hade da jawo hannunshi zuwa cikin falon sosai. Komai bai ce ba, ya biyo ni.
Babban tire mai kyau na dakko, na jera abincin da gorar ruwa daya, sai fruit salad mai sanyi.
"Mu je ko" Na fada a daidai lokacin da na zo wurinshi
Wannan karon ma bai yi magana ba
"Wannan yaron tun wuri miskili ne" Na fada a zuciyata ina kare mai kallo, cikin mulmulallan jikinshi da ke nuna yana samun kulawa a ko wane fanni.
"Assalamu Alaikum" na yi sallama a falonta hannuna rike da tiren abincin.
"Amarya shigo mana, na fito wanka ne" Daga cikin bedroom nata ta yi maganar bayan amsa sallamar tawa.
Daure take da towel iya gwiwa, jikin nan kamar na tarwada, iya inda na gani ban ga kurji ko alamar tabo ba.
Haka kalar fatarta mai wahalar fassarawa ta fita sosai gwanin sha'awa. Don ita dai ba za a ce mata fara ba, kuma ba baka ba.
Kamshin nan da kullum yake like da dakinta yana nan, na rasa wane irin turare take amfani da shi kamar maye.
Ni kaina yanzu dana shiga dakin nata sai in yi awa daya kamshin bai bar ni ba
Idan kuwa ta taba kudi, ko mijina ya kwana a dakinta ya dawo dakina, to har ya bar dakina kayan da ya shigo dasu ba zasu bar kamshinta ba.
"Tuwo fa na yi miyar kuka" na fada ina murmushi
"Ai shi yaran nan suka fi so ma, haka Babansu ma" ita ma cikin murmushin ta yi maganar
"Je ka dakko min plate a kitchen Khalil" Ta fada tana kallonshi
"Bar shi ya huta bari in kawo miki" Na fada hade da mikewa. Ta yi saurin riko ni
"Wayyoh! Rufa min asiri, wallahi ban isa ba, ke da Khalil din duk zauna na hutashassheku"
Kafin in yi magana tuni ta fice cikin sauri daga dakin. Na bi bayanta da kallo, wanda yake dauke da faffadan kwankwaso.
A zuciyata na ce "Ko yaushe nawa kwankwason zai bude kamar na ta oho"
"Wallahi Ramla ce ba lafiya, na biya asibiti shi ya sa ban dawo da wuri ba. Na ce Baban yaran nan yau ma ya shiga kwanonki" .
Maganarta ta katse min tunanina.
Murmushi kawai na yi, ba tare da na ce komai ba, lokaci daya kuma Ina kallon yadda take warware tuwan daga cikin leda zuwa kan tsabtataccen plate din gabanta
Hankali kwance take cin tuwon har da santinta wai ta fi son tuwo ya yi tauri haka.
A zuciyata na ce koma ba ki so ya kika iya haka nan za ki sassakeshi.
Na mike tsaye hade da taba jikin Ramla da ke bacci
"Zazzabin ma ya sauka, Allah ya sawake, bari in je daki"
"Amin, na gode amarya na hadaki da aiki,"
"A'a ba komai wallahi, sau nawa ni kina shan wahalar aikinki ki zubo min in cinye."
Dukkanmu muka yi karamar da dariya a daidai lokacin da nake fita daga dakin.
"Wannan mata wane kalar mai da sabulu take wanka da shi ni Khadija?"
Na fada a daidai lokacin da nake ficewa daga bangaren nata
"Ga inda ya kamata in bata lokacina nan, wajen koyon sabulu da turare na je na bata shi a koyon girkin kasashen waje."
A zuciyata na yi maganar hade da jan tsoki ina jin haushin kaina.
Saman kujera na fada raina yana min babu dadi,
Horn din da na ji ne ya sanya ni mikewa da sauri na nufi bedroom don na san maigidan ne ya dawo.
Kuma fuskata ko mai ban shafa ba, bare ta kai ni ga kwalliya, shi ya sa faka-faka na yi kwalliyar hade da shiryawa cikin riga da siket na atamfa.
Ina tsaka da Fess turare na ji knocking kofa a hankali, wannan ya tabbatar min da shi ne.
Na fito cikin yauƙi, a zuciyata ina kiyasta yadda zan tare shi, irin tarar da kullum yake korafin ban yi mishi, yau dai ita zan yi mishi.
Ganin hannunshi rike da Khalil ya sanya ni ja baya kadan, saboda na san ba zai so in rungume shi gaban yaron ba.
Da murmushi a kan fuskarshi ya ce
"Wata biyu da aure amma har yanzu kin kasa sakin jiki da ni, to sai yaushe?"
Ban yi magana ba, illa kokarin danne kunyar da take taso min da na yi hade da fadin "sannu da zuwa"
"Ban amsa ba ni wallahi"
Ya fada cikin muryar shagwaba, hade da kankace idanunshi a kaina.
Ba zan iya jurar kallon ba, dalilin da ya sa kenan na raba shi na wuce zuwa dinning table
"Ki sauke min abincin a kasa"
A kasan na aje mishi, na koma na zauna a kujerar da ke fuskantarshi.
Ya daga hannayenshi sama yana kallona.