← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ma kallonshi nake kafin in gano me yake nufi.

Mikewa na yi, na cire mishi babbar rigar da yar ciki, na aje a kan majinginar kujerar dinning.

Sannan na zuba mishi tuwon hade da fruit salad.

Rike hannuna da ya yi ne ina kokarin tashi ya sa na dakata ina kallonshi.

"Ina za ki je? Ba za ki ci abincin ba ne?"

"Zan ci" na amsa shi

"To Bismillah mana"

Na juya kan Khalil wanda hankalinshi kaf yana kan tv na ce "Khalil ba za ka ci tuwon ba kai?"

Kai ya jinjin alamar eh.

Yadda na ga Abbansu na dan murmushi, na fahimci ya ji dadin tayin da na yi wa Khalil din, haka muka rika ci tuwon a nutse hade da yin yar hira.

Shi ma dai cewa ya yi na yi mishi tuwon da ya fi so mai tauri.

Ban sani ba ko suna karfafa min gwiwa ne, ko kuma dai da gaske irin shi suke son oho.

Bayan ya idar bedroom ya shiga, ni kuma na shiga tattare kayan da muka ci abincin na shigar kitchen.

Daga nan kuma na bi bayan shi. Lokacin da na isa ya fito daga toilet da alama brush ya yi.

Dalilin da ya sa mu ka hadu a tsakiyar dakin

"Ina Khalil din?" ya fara tambaya ta

"Yana falo" na amsa shi.

"Ok" ya fada lokaci daya yana gyara hannun rigarshi

Tare mu ka juya zuwa falon, sai dai babu Khalil, da alama ya tafi wurin Mommynshi

"Ta shi mu je ki rakani wajen Auntynki in kara duba Ramla, in wuce ina da meeting karfe hudu"

"Ka je kawai" na amsa shi

"Me ya sa?"

"Ba komai"

"To idan ba komai tashi mu je"

"A'a fa" na ce ina gyara kwanciyata a kan 3sitter

"Ko ki tashi, ko in daga ki, wallahi sai a gabanta zan aje ki."

Ban motsa ba kamar yadda ban yi magana ba.

Ji kawai na yi ya yi sama da ni, hakan ya sa na fara dariya hade da kokarin sakkowa, amma ban samu damar yin hakan ba har zuwa lokacin da muka isa kofar sashinta.

Na dire kasa ina dariya, shi ma dariyar yake a haka muka kwankwasa kofar falon nata.

Khalil ne dai ya bude mana kofar, yayin da ita kuma Gimbiyar ke zaune a daya daga cikin kujerun falon

Wando da riga ne a jikinta masu kalar ja, wandon iyakarshi gwiwa kamar skin tight yake, sai kuma rigarshi mai hannun vest da kwalliyar fulawa mai kyau a jikin rigar, cif kan kwankwasonta rigar ta tsaya, kuma ba ta matseta da yawa ba.

A gabanta laptop din ta ce take daddanawa, ganinmu ne ya sanyata dagowa tana murmushi, idanuwanta a kan mijinta.

Lokaci daya ta mika mishi hannu tana murmushi.

Shi ma hannun ya mika mata fuskar shi dauke da murmushi, suka yi musabiha kamar dai wasu abokai.

"Ya jikin Ramla?" ya tambaya a lokacin da yake kallon Ramlan da ke zaune a kan kekenta na yara

"Da sauki sosai" Ta ba shi amsa ita ma tana kallon Ramlan.

Hancin yarinyar ya ja, ita kuma ta wangale mishi baki.

"Zan wuce office, ina da meeting karfe hudu, akwai wani abu ne?"

"Babu, amma me kake so da dare?"

"Abu mara nauyi, don kanwarki ta cika min ciki da tuwo"

Murmushi ta yi "Ta kyauta kuwa"

"Zan tafi. Waye zai raka ni?"

"Wacce ta rakoka nan" Ta yi saurin fada, babu alamar wata damuwa a kan fuskarta.

Gardama sosai muka shiga yi, daga karshe dai na mike hade da bin bayanshi.

Bayan ya daidaita a mazauni ne ya kalleni idanuwanshi a kankance

"A ba ni bye- bye"

Na janye fuskata a kan tashi ina siririn murmushi

"Sarkin kunya." ya fada

Ban yi magana ba, sai dai na mayar da kallona kanshi, a lokacin da na ji ya kama hannuna yana murzawa

"Ba zan daina fada miki ba Khadija, ina sonki, akwai abubuwa masu nagarta da yawa a tare da ke, na san ke ba ki sansu ba, amma ni na san da su"

Shiru na yi ina mamakin bakin ganga irin nashi, kullum yabon matarshi yake, sau tari ma idan na yi abu sai ya ce wance ba haka take yi ba.

"To idan haka ne me ye nawa yake burgeshi, kodai ya fada ne kawai don ya ji dadi? Ni wani lokaci ma rikita ni suke yi shi da matarshi, in rasa ina ne gabansu"
A zuciyata na yi maganar a zahiri kuma kallonshi kawai nake yi, ba tare da na yi niyyar magana ba

Juya hannun nawa ya yi, yana kallon bayan hannun kamar mai son gano wani abu.

Ganin ina niyyar janyewa ne ya sa shi kai hannun nawa a bakinshi ya sum bata a hankali.

Tare muka lumshe idanu, ya saki hannu hade da murza key din da ke jikin motar.

Na ja baya a hankali hade da rufe mishi kofar, sai da ya fice na dawo dakina, zama na yi zuciyata cike da sake-sake.

Ni dai ba zan ce bama zaman lafiya ba, amma na san abubuwa ba su zo mun yadda na tsara ko nake hasashe ba.

Kodayake yanzu aka fara tafiyar, kila rawar ta canja a gaba.

Matar J✍🏻
[12/16, 11:56] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 3*

A tsarin gidan shi ne, ranar da miji zai bar ɗakinki, ke za ki yi abincin dare, sai ya ci sannan ya baro dakin. Don haka yau Maman Khalil za ta miko min Abbansu Khalil, shi ya sa tun da na idar da sallahr isha'i na shirya cikin (English wears) da suka yi matukar karbar jikina. Ni ma yau so nike in burgeshi, in nuna mishi ni ma fa duk abin da matarshi ta iya na iya kuma zan iya.

Riga da wando ne, masu kalar ruwan madara, wandon dogo ne har kasa bai kamani sosai ba, rigar guntuwa mai siririn hannu da ta zauna kan kwankwaso na.

Na kama gashina na matse da ribbon mai kalar far. Na dawo falo na kame ina jiran dawowarshi. Ba jimawa kuwa na ji horn din shi, Ina jin lokacin da maigadi ya bude mishi, shi ya sa na yaye labulen windown falona ina kallon shi, har shige part din matarshi.

Zaunawa na yi, zaman jiran tsammani, na san dai ba zai wuce awa daya a can ba.
Sai dai sama da awa biyu, ban ji duriyarshi ba.

Duk yadda na so danne zuciyata abun ya ci tura.

Saboda yadda ya dade din, bai taba dadewa haka ba, bayan kuma ba aikinta ba ne.

Haka kuma idan aikin ta ne ba ya jimawa a wurina yake fita,
Sometimes ma Idan ya dawo Sai ya leka bangarenta, sannan ya taho nawa, koda kuwa
a dakinta zai kwana.

Amma ni yanzu ga shi har goma saura bai shigo ba turare sai fesawa nake da gyara powder amma shiru har na gaji.
Ba abun haushi irin ka yi abu don mutum kuma bai gani ba.

"Allah ma ya kara min! Da na auri saurayi babu abin da zai hada ni da wannan takaicin. Duk inda yake da abin da yake yi hankalinsa dai yana kaina. Amma yanzu yaransa sune farko sai uwar yaransa kafin ni in biyo baya."

Kai karshen tunanina ya yi daidai da jin karar bude gate, Sai kuma na ji tashin motarshi, wannan ya tabbatar min da fita suka yi.

Na ja tsoki hade da mikewa zuwa doguwar kujera na kwanta. Raina a matukar ɓace

Tun ina tuna banza da wofi har bacci ya dauke ni.

A cikin bacci na ji kamar ana jan kafata, dalilin da ya sa kenan na bude idanuwana a hankali cikin yanayin bacci na zubasu a kanshi.

" Da ace ɗana ne, da kawai mari masu zafi zan wanke fuskarshi da su" A zuciyata nake saka wannan amma a zahiri, kuma lumshe idanuna na yi.

"Bacci kike yi?"

"A'a rawa nake yi" a zuciyata na kuma yin maganar.

Amma a zahiri ko idona ma ban bude ba, bare ya yi tunanin zan ba shi amsa.

Ina jin shi ya wuce wurin abincin da na shirya mishi, na yi amfani da damar wajen kallon agogon da ke falona, karfe shadaya saura.

Wani gululu ya tsaya min a kirji duk kwalliyar da na yi, ta tafi a banza kenan bai gani ba.

Mikewa na yi cikin yanayin bacci na nufi bedroom

"Daga karshe dai na ga kwalliyar" ya fada a daidai lokacin da ya mike tare da nufo inda nake

Da sauri na shige bedroom, amma sai da ya cimma ni

"Ba za ki cire wannan kwalliyar ba, kin yi kyau kuma na yaba, na gode sosai"

"Ba za ki ce komai ba?" ya tambaya ganin ba ni da niyyar magana

"To me zan ce?"

"Abin da ke ranki."

"Ai babu komai" ina kokarin zama gefen gado na yi maganar.

Shi ma zaman ya yi kusa da ni "Ki yi hakuri, wallahi Affan ne ba lafiya muka kai shi asibiti"

Ai dama na san tatsuniyar gizo ba ta wuce koki. Kullum cikin hidimar yaranshi da ta matarshi yake. Ni kuma ko oho. Ko yaushe ma Affan din ya dawo oho. Saboda tun last week ya je hutu gidan kawar Mamanshi, daga can ake kai shi makaranta, a kuma dakko shi

"Allah ya ba shi lafiya" Na yi maganar daidai lokacin da nake kwanciya. Don gaskiya na kasa dannewa.

A yanayinsa na ga kamar bai ji dadin yadda na karbi abun ba, ta hanyar nuna halin ko in kula, amma ni bai dame ni ba, don gaskiya na fara gajiya da yadda yaranshi da kuma matarsa ke shiga lokacina.

Bayi ya shiga, ya yi wanka, na dauka ba zai neme ni ba, sai kuma na ga ya yi hakan, duk da ni ban bayar da hadin kai dari bisa dari ba. Don har zuwa lokacin zuciyata zafi take yi.

Ni ce na tashe shi zuwa masallaci sallahr asuba.

Ni ma kitchen na shiga bayan na idar da sallah, doya na fere, yam balls nake son yi.

A nutse nake yin aikina duk da dai bana jin dadin zuciyata

Don ma Bashir mutum ne da ya san mace, sosai ya tafiyar da kashi saba'in cikin dari na damuwata a daren jiya.
Chapter 3 · 0% Book details