← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 44

Sashe 19

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina mika mata ta fice, duk da bai yi magana ba, amma na san tabbas shigar Maman Khalil ta tafi da shi.

Wando ne baki mai kama jiki ta sanya, tsawonsa bai wuce gwiwa ba, jar riga wacce hannunta ya tsaya rabin cinyar hannu, ba ta kamata ba sosai amma kuma ta fito mata da dirinta, bakar hular da ta dora a kanta ma ta kawata mata kwalliyarta.

Sam bana son ganin giccinta idan ina tare da mijina, don muddin za ta gitta muna tare da shi ta kan janye hankalinsa zuwa wajenta gabadaya.

Shiru ya ratsa wajen bayan tafiyarta.

"Kin ki fada min laifina ko?" ya katse shirun namu
A yanzu dai ba zan iya fada ba, Maman Khalil ta kuma dagula min komai.

Ganin ban yi magana ba, ya sa ya kwantar da Ramla da ta yi bacci, sannan ya ce "To mu kwana lafiya."

"Allah ya sa" na fada a lokacin da yake fita

Kamar ransa a bace, amma ban damu ba, matar Sonshi za ta wanke mishi shi tas.

Matar J✍🏻
[12/22, 14:42] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 16*

Karfe hudun asuba, na tashi Ramla na yi mata wanka, lallen hannun ya yi kyau sosai, fulawar ta fita radau ba ta dame ba, saboda na yi ta kula da hannun.

Tea na ba ta bayan na shiryata, cikin riga da wando masu kyau a irin tsarabar Rahma ne.

Wandon na jeans fari mai taushi, sai pink din riga ita ma mai laushi, sosai ta yi kyau musamman dana dora mata pink din takalmi a kafarta.

Duk da akwai alamun bacci bai saketa ba, hakan bai hana na yi mata hotuna ba.

Sannan na goyata a bayana don ta koma bacci. Ina cikin jijjigata na ji alamun an shigo, a kofar shigowa bedroom din muka hadu.

Ta dan ja baya tana dariya "Wallahi na dauka ba ku tashi ba."

Ni ma dariyar na yi "Haba tun 4am mu ka tashi."

Miko min bowl din hannunta ta yi mai dauke da cin-cin "Ga na ki nan, na tsaraba ne da na yi."

Na karba hade da godiya mai yawa

"Wai yanzu da wannan katon cikin kike goya yarinyar nan? Don Allah ki sauketa kar ta nane mana hancin yaro."

Murmushi na yi kafin in ce "To sai me idan ta nane, ni dai ga amanarta nan a hannunki."

"Ni!! Allah ban karba ba, ba zan iya wannan kicimillen ba, wai daka da miji goye."

"To Allah zan hanata zuwa."

"Dama ni na ce zan je da ita, ke ma kin san idan ni ce da yarana zan tafi, wa zai dauki wannan rigimar. Kuma ga amanar yarana nan a hannunki, idan kika ci Allah sai ya tambayeki"

"Guda kika bari guda za ki taras, ni ma kuma da gaske ki kula min da yarinyata."

"Ni gaskiya ba zan iya ba"

"amma kuma ni na karbi ta ki amanar?"

"Yarana ai ba kamar yarinyarki ba ne, yauwa Baban Khalil..." ta yi saurin kiran sunansa dalilin shigowarsa

"Ka shaida na bawa Khadija amanar yarana, kar in ji kar in gani, amma kuma ni ban karbi tata amanar yarinyar ba."

Dariya duk mu ka yi, ni kuma na nufi kitchen hade da dakko mata flask din da na zuba tsarabata, na mika mata "Ki kai wa Inna, sannan ki ce ina mata sannu." na kuma mika mata ƙaramin food flask na ce "Wannan kuma ku ci a hanya"

"Kai madalla, An gode kuma sha Allah za ta ji."

Bayan ta fita ne ya zuba min ido

"Ba na ce ki daina goya yarinyar nan ba wai?"

Ban yi magana ba

"Je ki sauketa." Babu alamun wasa akan fuskarsa.

Ban yi magana ba, na dai zumbura bakina hade kawar da kaina gefe alamun bana son yin abin da ya fada.

"Ba ki ji ba ne?"

Na kuma turo baki ina kallonsa, yanayin da na gani a fuskarsa ne ya sa na shige bedroom na kwantar da ita ba don naso ba.

A in da yake tsaye nan na same shi.

Key ya je ya sanyawa kofar falon, sannan yan janyoni jikinsa, ya rungume hade da shafa bayana.

"Na san fushin da kike yi, a kan maganar Inna ne ko? I'm sorry, ni ma a shekaranjiyan na
ji maganar, kuma sai na shafa'a ban fada miki ba, sai can dare abun ya fado min, kuma a lokacin kina bacci. Da safe kuma hankalina ya tafi office sai da Maman Khalil ta yi maganar na tuna. Please sorry Kar in tafi kina fushi. "

Har yanzu kwance nake a kirjinsa, ban yi magana ba.

Dago fuskata ya yi" say something please . "

" Ba komai na fahimta."

"Thanks" ya fada hade da kissing din goshina.

"Zan yi kewarki sosai, Inna ce ta ce kar aje da ke cikinki ya yi nauyi."

Na danyi murmushi mai alamar kunya

"I love you" cikin wata irin murya ya yi maganar.

Jikina ya mutu likis.

Ya kuma dago fuskata da na boye a kirjinsa.

"Do you love me?"

Hannayena biyu na sanya a kan fuskata ina murmushi.

"Sarkin kunya" ya fada a daidai lokacin da yake fita

"Ki kawo Ramlan tafiya za mu yi." ya yi maganar ne a kofar daki.

Sabota na yi a kafadata daya hannun kuma rike da flask, don kayanta tun jiya na ba wa mamanta.

A kan cinyar Maman Khalil na dorata.

Har yanzu bacci take yi, na mika mata ƙaramin flask din ina fadin" Ku kula min da yarinyata don Allah."

Zuwa lokacin zuciyata ta gama karyewa, hawayen da nake kokarin boyewa suka gangaro a kan kumatuna.

" Ikon Allah!"

Abun da Maman Khalil kawai ta iya cewa kenan tana kallona.

Baban Khalil ne ya mayar da ni daki yana rarrashi, har zuwa lokacin da yake ganin zuciyata ta yi taushi.

Ina jin fitarsu daga gidan, sai na ji jikina ya kuma mutuwa, zuciyata ta yi kunci, komai nawa ya tsaya

Haka nan na yunkura zuwa bangaren Maman Khalil in duba su Affan ko sun tashi, har lokacin bacci suke yi.

Tashinsu na yi muka dawo sashena, su ka yi alwalla da brush, ni kuma na shige kitchen don nema mana abun kari.

Lallai sabo ake wa kuka ba mutuwa ba, mutum rahama ne, ji nake kamar ni kawai ce na rage a duniya ba kowa, gidan duk ya min fadi.

Duk da Ramla ba mai yawan surutu ba ce, amma zirga-zirgarta da rigimarta ta kan debe min kewa.

Idan kuwa na gaji da zaman shiru wajen Maman Khalil nake tafiya sai ta debe min kewa.

Ga mai gayya mai aiki wato mijina, idan har yana kusa da ni to tabbas sai na yi dariya, ya kan mantar da ni da yawan damuwata.

Duk da ba na ganin yan gida, idan yana kusa ba na kewar rashin ganinsu.

Wani lokaci yana bata min rai sosai in ji kamar in yi ta bugunsa, amma kuma dai sonshi da kaunarsa na nan daram a zuciyata.

Kiran da ya shigo ne a wayata ya katse min tunani, Maman Khalil ce, cikin sauri na dauka.

"Kin kirani, wayar na a cikin jaka kuma a silent?"

"Dama so nake in tambayeki yarinyata ta tashi?"

Ina jin sautin dariyarta kafin ta ce "Ta tashi yanzu?"

"Tana kuka na yi saurin tambaya?"

"To wa za ta yi ma wa? Dama ai don ganinki ne ya sa take wannan tabarar."

Tausayin Ramla ya kama ni , ji nake kamar in yi tsuntsuwa in bi su, don na san duk a takure take, kuma na san tana son ganina.

"Don Allah ki kula min da ita" wannan karon cikin sanyin murya na yi maganar

"Yanzu kam kin ba ni tausayi, zan kula miki da ita sosai kamar kina wurin "

Na dan yi murmushi mai sauti "Allah ya kiyaye hanya" na fada hade da yanke kiran.

Sosai na ja su Affan jikina suka saki jiki mu ka yi break fast, sannan na yi masu wanka, suka shirya cikin kaya marasa nauyi.

Cartoons suke kallo a tashar St kids ni ma ina taya su, duk da dai hankalina yana kan masu tafiya.

Misalin sha daya na safe sai ga Rahma wai ta zo daukarsu Affan.

Mamaki ya kama ni, don ni ba mu yi haka da uwarsu ba.

Ganin hakan ne ya sa ta ce "Su Farhan ne za su yi birthday shi ne za su je taya su murna, amma bayan haka ba komai wlh"

Duk da ban ji dadi ba, haka nan na hakura saboda Oga ya sa baki. Ina gani Rahma ta kwashesu zuwa gidanta.

Sai gidan ya kuma yi min fadi na zama kamar wata mayya.

Shirun duk ya min yawa,, har ji na yi ban lafiya, waya kuwa minti-minti nake kira, ga Ramla za ka shekara dari kana mata magana a waya ba ta amsawa, sai dai ta yi kasake kamar wacce ake yi wa susar kunne.

Haka nai ta yawo kamar macen da aka saki da sauran so, ba ni ɗaka ba ni waje.

Da yamma kuwa kifa hajabina na yi, na mike layin unguwa na yi ta tafiya, har sai da na ji na gaji sannan na dawo.

Dalilin da ya sa kenan na kwanta da wuri bacci mai nauyi ya dauke ni.

A firgice na farka sakamakon wani mafarki da na yi, jikina sharkaf da gumi duk kuwa da saitin fanka nake.

Kirjina harbawa yake yi da karfi kamar yadda yake harbawa a mafarkin.

Waya na janyo, na fara laluben lambar Rahma sai na tuna ashe ma ban da lambar.

Wata shida baya na taba wani mafarki, wai an yankewa Affan hukuncin kisa ta hanyar rajamu (jefewa) amma wai an ce a jira sai ya kara girma, don haka aka debi wasu shekaru da ake ganin zuwa lokacin ya kara girman.

A cikin mafarkin ni ban damu ba, dariya ma abun ya rika ba ni , saboda gani nake ba za su jefeshi ba, kawai ana tsoratashi ne, koma kafin lokacin da aka diba din mutanen sun manta.

Amma fa wasu har da kuka suke ta yi, ni kam ko a jikina.
Chapter 19 · 0% Book details