← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 44

Sashe 16

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganganu masu karfafa gwiwa ya ci gaba da fada min har zuwa lokacin da ya ja min kofa ya fice.

Lumshe idanuna na yi cike da jin dadi, ni ma dai yau na rama abun da Maman Khalil ke min, na rike min miji bayan a dakina yake, ban taba tunanin irin wannan ranar ni ma za ta zo ba, ashe dama can sauri nake yi.

"Ko ya zuciyarta yanzu?" na yi tambayar a zahiri hade da tashi zaune ina murmushin mugunta.

Ya zama dole in karo wasu hanyoyin kissa domin ni ma ya zama mijina ya na yi da ni ba ita kadai ba

"Yes!" Na fada da karfi hade da wurga hannayena irin celebration din nan.

Koda gari ya waye ma ban ga keyarta ba, ni ma kuma ban leka ba, har zuwa lokacin da Ogan gidan ya zo gaisheni.

A lokacin na yi simple kwalliya cikin riga da zane na atamfa, na yi daurin ture ka ga tsiya ina zaune kan kujera ina kallon shirin *Morning to you Nigeria*

Kusa da ni ya zauna tamkar zai shige jikina, wannan kuma ita ce dabi'arsa

"Ta shi in ga kwalliyar?" abun da ya fara fada kenan bayan na amsa sallamarsa.

"Ba ga shi ka gani ba"

"Allah sai kin tashi"

Na yi kamar ban ji ba

Sai ya fara min cakulkuli, dariya nake sosai a lokacin da na zame daga kujerar zuwa kasa, amma bai bar ni ba, har sai da na mike tsaye ina fadin "Sorry na mike ai"

Shi ma dariya yake yi sosai a lokacin.

"Kin yi kyau, ina masifar son in ga mace ta sanya atamfa ta daura zane, normal zane irin wannan kuma a yi dace ta iya, kai tana tafiya da ni sosai" gama fadin hakan ke da wuya, na ji ya janyo Ni ta baya, hade da dora hannayenshi duk biyun a kan cikina.

"Ina sonki!" ya fada daidai saitin kunnena, ban kai ga amsawa ba, ya juyo ni muna fuskantar juna, hannayenshi ya yi amfani da su wajen tallafe fuskata, kafin ya hada bakina da na shi.

A daidai lokacin kuma Ramla ta fito daga bedroom cikin yanayin bacci ta zuba mana ido.

Da sauri na kwace kaina, hade da nufar inda take. Lokaci daya kuma na daga ta zuwa jikina ina fadin "Yarinyena! Kin tashi"

Hankalinta a kan Babanta har na shige da ita bedroom, ina yi mata wanka ya shigo, gefen gado ya zauna hade taɓa wayarshi

"Zan je Ruma, ki shirya mu je" ya yi maganar lokacin da nake fitowa daga toilet rungume da Ramla

Cike da doki na ce "Aiko na gode, dama Ina ta kewar garin"

"Irin kin zauna din nan sosai"

Murmushi na yi kafin na ce "Ban zauna ba, amma abubuwa masu dadi sun zauna a kwalkwalwata"

Idanunshi ya saka cikin nawa, na yi saurin janye nawa din ina murmushi

"Menene abubuwa masu dadi?"

"Sirrina ne" na amsa har zuwa lokacin murmushi nike yi

"Allah sai kin fada" ya yi maganar hade da kawo min cafka, na yi saurin tashi dauke da Ramla a jikina ina dariya, kai tsaye kan dining na zarce, tea na shiga hada mata.

Daidai lokacin ya fito, kai tsaye kuma kofa ya nufa, wayar shi akan kunnenshi, da alama kira yake amsawa.

Matar J✍🏻
[12/18, 06:52] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 14*

Yau ma Maman Khalil ba ta yi min sallama ba ta wuce wurin aiki.
Na rika hasashen tana jin irin zafin da nake ji ne, ko kuma dai ta yi latti, zan jira ta dawo domin tantance zargina.

Mu ka sha baccinmu da Ramla, sai 12pm na shiga kitchen, jalouf din taliya na yi mana da ta ji busasshen kifi da ganyen ogu, Ramla na fara sanya ma wa, kafin na watsa ruwa hade da yin alwalar sallar azhur.

Bayan na idar doguwar riga mara nauyi armless na sanya, kafin na zuba abinci ni ma. Cike da jin dadi nake cin abincin.
Misalin biyu da yan mintuna motar Sakeena ta shigo.

Kamar 30mns da dawowarta na mike zuwa part din nata, hannuna cikin na Ramla.

Affan ne ya bude mana kofa, lokaci daya kuma ya mamutsi Ramla, sosai yaran ke son Ramla, tana da farin jinin mutane.

A wajen na bar su zuwa cikin falon nata, zaune take tana shan rake

"Ƙurmusu!" na yi maganar cikin salon tsokana
Dariya ta yi kafin ta ce "Ga naki can cikin fridge, na gaji ne yau sosai"

Fridge din na zarce hade da dakko nawa raken na dawo falon.

Hira muke yi sosai, a cikin hirar ne take fada min Rahma za ta shigo gobe. Na ce Allah Ya kai mu.
A nan na yi sallahr la'asar kafin na koma part dina, saboda na san mijinta yana kan hanyar dawowa.

Ban jima da baro wurintan ba kuwa ya dawo.

Kashegari da ta kama Friday, ana sakko masallacin juma'a Rahma ta iso, na so ganinta a lokacin da take shigowa, Sai dai lokacin ina sallah.
Ina idar da sallahr kuma na yi wa Ramla wanka, na shiryata cikin riga da wando yankanti wandon jeans blue black, da white shirt mai kyau. Ni ma cikin doguwar rigar material rubber na shirya, sosai rigar ta boye girman cikina, duk dama jiki ya sanya ni sosai.

Muka fito hannuna cikin nata, cikin sa a main kofar a bude, shi ya sa na saka kai, kaina tsaye
Maganar da na ji su na yi ne ta tsayar da ni, hade da rufe bakin Ramla da hannuna don ma kar ta yi magana su ji mu.

"Hmmm! Kishiya ko ta kara ce aka yi miki ita wallahi kawata sai kin ga canji, ina hakuri ne kawai game da danne kishina saboda kada girmana ya fadi, amma tabbas ina ganin abubuwa."

Mamaki ya kamani da jin kalamanta, "To me take gani?" na tambayi kaina hade da kame habata cike da mamaki.

Lokaci daya kuma na mayar da hankalina kansu

"Kin ga rawar kan Baban Khalil kuwa? To kamar bai taba hada shimfida da wata mace ba sai ita, koda rana ya shiga bangarenta to bai fita haka nan, ni kuwa nan wani lokacin sai idan ni ce na kusanceni shi"

Zaro idon mamaki na yi, "ya a kai ta san Abban Khalil ko da rana baya kyale ni ? Na kuma yi wa kaina tambayar ina kuma mamakin maganarta wai sai idan ita ce neme shi. Ni kuma a can nawa bangaren ina ganin kullum a manne suke da juna, wannan shi ne zargin-zargin.
Wato ita kishiya duk inda kika motsa idonta a kanki yake. To idan ba haka ba, ya aka yi ta san wani abu na faruwa tsakanina da Abbansu Khalil da rana, ko don kawai ta kama mu sau daya.

" Ko a dakina yake kaf hankalinsa a kanta yake, wani lokaci ko magana muke sai ya kira ni da sunanta"

"Ba ke kadai ba Madam, ni ma yana yi min irin wannan suɓutal kalam din, ashe ke ma kina jin haushi." na yi maganar a zuciyata tare da gyarawa Ramla tsayuwa don kar ta gaji ta tona min asiri.

"Shi ne ba za ki dakatar da hakan ba?" cewar Rahma cikin zafi

"Kawata ba ki san zaman kishi da wayau ake yin sa ba? Ai shi yaƙi ɗan zamba ne. Kuma a haka ma yana kokarin ganin ya daidaita kanmu kawai dai kin san sabon aure murnar ba ta boyuwa."
Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba

"Shi ya sa ni kuma na nuna ban damu ba, ita ma na kame mutumcina da girmana a gurinta, in ji, in yi kamar ban ji ba, in gani in yi kamar ban gani ba, ko ba komai ban bayar da kofar raini ba, na ja girmana."

"yarinyar ba ta miki rawar kansu irin na zamani?" tambayar Rahma cikin wata kasalalliyar murya

"To ga abu nan dai, abin da na fahimta dai tana da tsananin kishi, haka nan ma sai ta yi ta fushi musamman idan a dakinta yake ya shigo bangarena, ke kwanakin baya ma mun kai sati biyu ko magana ba ma yi, ni ma kuwa na shareta, da kanta ta sakko, da ina biye mata da abubuwa marasa dadi sun faru, don kuwa kishina ma ya fi nata, ina jan girmana ne kawai tare da danne shi "

"Ikon Allah ki samu mace da mijinta, kuma har ki nuna wai kin fi ta kishin sa " Akwai alamun mamaki a maganar Rahma

"Kuma wayau gareta fa, yanzu ta canja tako, ta janye yarannan gurinta musamman Ramla, to yanzu dai hankalinsa ya kuma komawa wajenta kullum cikin yabonta yake, idan yana yi taya shi nake ba na son ko kadan ya fahimci ina kishi sosai, amma a kasan zuciyata kamar wuta, wai a gabana Baban Khalil ke yabon wata ba ni ba, hmmmm! Wani lokaci sai in yi kuka mai yawa in share hawayena, ko ba komai da karuwar waje gara ta gida."

"Ki yi hakuri tun da ma ba ta yi kokarin raba ki da mijin ba, sannan ba ta yi miki rashin kunya, sai a lallaba a tafi haka, ki ci gaba da rike girmanki, yara kuma tun da ba hanyar banza take sanyasu ba rika yi mata kara, ki kuma mika mata su ita ma idan nata sun iso ki kama ki rike hannu biyu." Cewar Rahma cikin sigar lallashi

Jin shiru Maman Khalil ba ta yi magana ba sai Rahma ta kuma dorawa.

" Kishi kawai yan dabaru ne, kuma kishin cacar baki yanzu an daina shi, kishin neman kudi da yadda za ka zauna da mijin da kuma yan'uwansa ake yi. Kuma wajen wannan kawata bana jin ki, tuni kika kama danginsa kika rike, kina da tsafta, kin iya kwalliya, kin iya girki, kina da jiki mai kyau, kina kula da yaranki, mijinki kina kokari a kan duk abin da ya shafe shi sai dai ko butulci zai yi miki, uwa uba kina da hanyar samun kudi, to me ya rage kawata? "

" Hmmmm! "

Kawai na ji Sakeena ta iya fada.
Chapter 16 · 0% Book details