Sashe 33
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran na yanke cike da jin zafi, wai haka mutum yake ji idan ya ga mijinshi na neman wata. Kqi akwai zafi gaskiya. Ji nake komai babu dadi.
A haka na karasa gida. Maama na fara yi ma wanka, na canja mata kaya zuwa doguwar rigar atamfa dinkin yara mai kyau. Sosai ta yi kyau, musamman kitson kanta ya kara fito da ita, yadda take ta tsalle-tsallenta sai ta koma min Ramla. Na yi ta kallonta zuciyata na kara min babu dadi
Misalin karfe shidda su Khalil suka dawo, su ma wankan na sanya suka yi, hade da canja kaya sannan suka wuce masallaci, daidai lokacin kuma aka shigo min da Assidiq ya sha kukanshi ya yi gwaɓe-gwaɓe.
Dole na yi zaman ba shi nono, sannan na lallabashi na kwantar na yi sallahr magriba.
Sallahr isha'i kam sai da su Khalil suka dawo masallaci, suka rike min shi sannan na samu na yi ta.
Haka muka rika karba-karba har 10pm Sannan ya yi bacci, su ma suka kwanta. Ramla kam dama tuni ta yi bacci.
Sai da na gama shirin kwanciyata tsab, sannan na kira Bashir
"Ba ki yi bacci ba?" abin da ya fara tambaya ta kenan
"Kewarka ta hana ni" na ba shi amsa
"Kuma da ina nan kin iya saka Assidiq a tsakiyarmu ai"
Dariya mai dan sauti na yi kafin na ce tsoro nake ji.
"Shi ya sa na yi nesa da ke ai, saboda ba zan iya hak'uri ba, kuma na ce ki yi planning kin ƙi yi"
"Zan yi"
"Ya kamata, don ba zan iya ba, in fada miki gaskiya."
Na kuma yin murmushi kafin na ce "na ga bazawararka yau" haka kawai na ji na kasa rike maganar
"Wacce?" ya tambaya
"Kenan suna da yawa?" ni ma na jefa mishi tambaya.
Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce "Khadija tawa"
Na haɗiye wani abu mai daci sannan na ce "Don Allah ina son zuwa gida, a wannan karon dai ka duba min don Allah." na karashe maganar kamar zan yi kuka.
Saboda rabona da in je gidan tun kafin su yi accident, sama da shekara daya kenan, saboda ko yanzu Khalil watanshi hudu.
"Zan duba, kin san ba na son a bar yaran nan"
Shiru na yi komai ban ce ba, saboda kullum abin da yake fada kenan, bai so a bar yara. Yaran da gasu nan a tsakiyar dangi. Kila ni na daina zuwa unguwa saboda su.
"Na gode" na amsa hade da sauke ajiyar zuciya
"Take care!"
"Thank you!" na fada hade da lumshe idanuna, saboda yadda ya yi maganar
Ajiye wayar na yi batun Sarai na dawo min cikin kai, ban san haka mata ke ji ba, idan alamu suka nuna mijinsu na shinshinar wata mace, ko ita macen na shinshinarshi.
Abu kamar wasa sai na kasa bacci, har 12am,idanuna biyu, comparing kaina da Sarai kawai nake yi, ta ko wane fanni na yi mata fintinkau, amma lamarinta ya dame ni, kodayake an ce kishiya ba ta da kadan.
Bacci ba shirin daukata Assidiq ya farka, don haka muka dosa har 2am,sannan na samu ya yi bacci, ni ma na samu baccin ya dauke ni.
Safe kuma na dora hidimar gida, daga wannan sai wannan babu wani hutu.
Wannan abu sosai yake damuna.
Ranar Alhamis da yamma sai ga Bashir kwatsam, saboda bai fada min zai zo ba.
Inda Allah Ya taimake ni, komai nawa tsab, amma yana zuwa da batun Maama ya fara ko zama bai yi ba "Har yanzu ba ki mayar da Maama ba?" ya yi tambayar da alamun bacin rai.
Na danne nawa bacin ran na ce "Ita da kanta ta zo"
Wani kallo ya yi min kafin ya ce "Tun daga can gidan take zuwa nan ita kadai"
"To zan yi karya ne, ka gwada tasa ta gaba ka sha mamaki"
"Na san halin ki ai, za ki iya zuwa ki dakko ta"
Baki kawai na rabe,idan na ce zan mayar mara dadi ce, wai ya san hali na, irin na saba dakkotan nan.
Assidiq ya amsa da yake ta kallon shi ya ce "My boy, ka girma fa"
Shi ko ya wangale mishi baki
"Ina sauran yaran?" na dauka ma tambayar da zai fara kin kenan, Sai ya fara da batun Maama.
"Suna cikin gida" na ba shi amsa lokaci daya ina zare mishi takalman kafarshi da socks din.
"Ya gidan?"
"Yana nan lafiya sai kewarka"
Murmushi ya yi kafin ya ce "Kamar gaske"
Ni ma murmushin na yi ina fadin" gaske ne mana"
Ruwan wanka na hada mishi, bayan ya fito ya yi shirin masallaci saboda ana ta kiran sallah. Ni kuma na shiga gyara tsarabar da ya zo da ita, na kuma ware wacce za a kai cikin gida
Misalin 8:30pm ya shigo tare da yaran a zuciyata na ce "Sai da ka lalubo su kenan"
Abinci na hada musu, suna ci suna hira, ban samu kanshi ba, Sai da suka yi bacci sannan.
Muna kwance bayan ya gama sauke nauyin da yake ta cewa ya zo da shi ya ce "An gama komai na gida fa sai tarewa"
"Kai Ma Sha Allah, yaushe kenan tarewar?"
"Shi ne har yanzu nake ta tunani, ba na son a kara cire yaran nan daga makarantar nan zuwa wata, abun sai ya yi yawa. Tun da saura term daya su gama na ce ko mu jira su kawai, kin ga muna komawa js1 za su tafi."
Kai na jinjina alamar gamsuwa kafin na ce "Tunani mai kyau, hakan ya fi, Allah Ya nuna mana lokacin"
"Amin" ya amsa hade da janyo ni jikinshi sosai ya ce "Sosai fa na yi kewarki, ina jin kamar a koma second round"
Da sauri na janye jikina, ina fadin" matsa don Allah "
Dariya ya yi mai sauti hade da maido ni jikinsa ya ce" Khadija idan zan yi aure ya za ki yi? "
Matar J ✍🏻
[12/22, 21:21] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 27*
Na tabbata ya ji yadda zuciyata ta buga, ba iya zuciyata ba, har numfashina sai da ya yi season for some seconds Kafin ya dawo daidai. Na yi ta kokarin daidaita nutsuwata kafin na ce "yaushe za ka yi auran? "Ni ma na jefa mishi tambayata
" Ban san ya rana ba, amma ina ji a jikina zan yi, kin san an ce duk namijin da ya saba da mata biyu ba zai iya zama da guda daya ba"
Idanuna na lumshe a hankali, kafin na ce "Sarai za ka aura?"
"I don't know"
"Ka aure ta, tana sonka" na fada har cikin zuciyata, saboda ina ji a jikina za ta fi min saukin kishi, bazawara ce wacce miji ya mutu ya bari, secondly ba ta yi boko ba, ba ta da wayewa, na fita cika mace a zahiri dai, duk wanda ya kalle ta, ya kalle ni, tabbas zai fahimci ni ba sa'arta ba ce, kuma a haka kamar ba ta da matsala
Ya kuma janyo ni sosai jikinsa kafin ya ce "Me ya sa ita?"
"Saboda tana sonka"
"kodai don kin fita wayau?"
Karon farko da na yi murmushi jin ya harbo jirgina ba tare da na ce komai ba.
Shi ne ya kuma cewa "Allah Ya iya mana"
A hankali na ce "Amin"
Daga haka ya kuma shigewa jikina ba jimawa na ji saukar numfashinshi alamun ya yi barci.
Ni kuwa na nemi baccin sama da kasa na rasa, maganganun da muka tattauna suna ta min yawo, in juya can in juya can. Amma tabbas Ina ganin cinta a kan Sarai.
Safiyar juma'a kasancewar yara ba makaranta sai aikin safen ya dan yi min sauki, saboda suna taya ni, Babansu ma ba a bar shi a baya ba. Cikin kankanen lokaci muka hada break fast muka karya, a tare muka kara gyaran gida, ni kuma na shiga hidimar abincin rana, kasancewar ana fita da abincin kofar gida duk ranar Friday.
Su Khalil ke taya ni, zuwa 1pm ya rage saura karashe, yayin da su Affan suka yi shirin masallaci. Shadda gambari fara dinkin babbar riga suka yi anko, sosai suka yi kyau, girman Khalil yana ban mamaki, girman jikinshi ya fi shekarunshi.
Bayan sun dawo masallaci suka ci abinci, suka dauki abincin Inna da kuma na Hajiya mahaifiyar Maman Khalil, saboda duk lokacin da na dan yi abinci na canji ina kai mata, kuma duk ranar Friday ma ina kai mata.
Misalin karfe biyar na yamma ina zaune a falo cikin kwalliyar Lace riga da siket wadanda suka karbe ni sosai, hannuna rike da wayata ina chat da su Samira da Yusrah aka yi sallama kofar falon, na amsa Sarai da Baban Khalil suka shigo, gabana ya yi wata irin faduwa, har suka karaso cikin falon ban janye idona a kansu ba. Musamman Sarai wacce take sanye cikin Lace ita ma mai saukin kudi riga da zane hade da farin hijab.
"Za ta wuce na ce ya kamata ta shigo ku gaisa" cewar Baban Khalil a lokacin da yake zama kan kujera
"Ai kam na gode. Sarai ya gida?"
"Lafiya kalau" ta amsa min a hankali
Daga nan duk mu ka yi shiru, Sai shi ne yake ta jan mu da surutu, like 30mns ta mike tana fadin "Na gode, a gaishe da yaran, na ga ban ga ko daya ba"
Mikewa na yi ni ma tare da fadin "Wlh duk sun fice har Assidiq din ma"
Iyakacina bakin kofar falo, na yi tsaye Ina kallon yadda suka jera, Bashir ana ta jefa kafa, ita kuma tana tafiya a nutse daurin zanen nan Das kamar an yi mata da injin.
A zuciyata na ce, wai kodai daurin zanen nan ne ke daukar Bashir ne, na son shi da son ganin mace a cikin riga da zane. Shigowar Murja ce ta katse min tunanina, cike da girmamawa ta matar kane ta gaishe da Bashir, kafin ta nufo cikin gidan.
Tare muka juya zuwa falo tana fadin "Wai abun nan kodai da gaske yin shi za a yi?"
"Sai Allah kam. Amma ku a nan babu damuwa ne mace ta rika sintiri a gidansu saurayin ta?"