← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 44

Sashe 41

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har wani gayyar abokanshi na Abuja yake yana washe baki kamar bai taba aure ba.

Sosai nake jin tausayin Sakeena idan har haka ta ji a lokacin da Bashir zai aure ni, lallai ta yi ta ji babu dadi sosai , kuma ta isa gwarzuwa, Sai dai in ce Allah Ya kai haske kabarinta, ni kam ba zan iya irin hakuri da kawar da kan da ta yi ba.

Saboda dole ce kawai ke hadani magana da Bashir, dolen ma idan na jefa daya biyu, sai kawai in yi shiru. Shi din ma bai kula ba, hidimarshi kawai yake yi. Abin da ya fi kular da ni.

Ana gobe daurin aure ya tafi Ruma, wai za su yi party a ranar da yamma washegari kuma za su taho da amarya bayan an daura aure.

Jin abun nake yi kamar mafarki, wai za a yi min kishiya, ranar kam ban warware ba, Sai da su Yusrah, Samira da Badiyya suka zo, ga makotana sun cika gida, ga su Maman Hana da Umaima, ai fa sai na sake aka yi ta sha'ani, magriba gidan ya koma shiru. Uwani ma ana yin isha'i ta tafi.

Ranar kam an sha hira, labarai da suka shafi kishiya nai ta ji mai dadi da mara dadi, a nan na kara fahimtar lallai kishiya kala-kala ce, kowa da irin ta. A wannan karon ko da wace kala zan hadu oho.

Safiyar daurin aure dama ba zama, abincin da za a kai aikatau aka kai, wanda kuma za mu yi a gida aka fara.

Zuwa 12pm mun kammala duk wani abincin da za a ci, wanda aka kai aikatau ma an kawo.

Daya part din duk muka kintsa kayan abincin, sannan aka shiga gyaran gida, ko ina ya yi fes, kamar ba biki ake ba, part dina su Maman Aiman suka rufe bayan an gama gyarawa muka koma dayan part din.

Dama tun 12pm abokan Bashir suka tafi da Affan, Khalil da Assidiq Ruma, wai daurin aure.

Wajen 3pm na fito fes cikin irin shaddar da su Assidiq suka sanya da za su tafi, haka Maama ma, hatta Haidar irin ta ce, light make up aka yi min, sosai na yi kyau, musamman kunshi da kitson da aka watsa min ya kara fito da fatata mai haske.

Su Maman Hana ne, suka matsa lallai sai a dakko Dj, zuwa karfe hudu kuwa, Dj din ya gama decoration din gidan, an kafa runfuna, ga manyan speakers masu duka.

Gida a cika makil da mata yan gayu masu aji da ji da kansu, kuma wai don duk ni suka taru. Sai na ji zuciyata wasai, duk babu wannan tarin damuwar. Tun ba da sauti kida ya fara tashi a tsakar gidan ba, nan da nan mata suka cika fili ana rawa, kun san ƴan Katsina da rawa dai 5&6 ne.

Ai tun ina yin bayan fage na shige tsakiyar fili aka rika takawa da ni. 5pm amare da angwaye suka iso. Tare da wasu dangin Bashir da na Maman Khalil.

Yadda dangin amarya ke nuna ni sai na ji ni a sama uwa hula, saboda zame masu na yi kamar wata a tsakiyar taurari, wannan ya tuna min lokacin da aka kai ni Abuja. Dangina suka ci karo da Maman Khalil mace mai matukar kwarjini da iya ado, ga wani sassanya kyau, tana cikin kawayenta wayayyu ƴan gayu. Haka dangina suka rika bin ta da kallo cike da tsoro gami da fargabar yadda zan zauna da ita.

Saboda dai babu wani abu da zan nuna mata, to irin wannan kallon dangin Saratu ke yi min.

Ita kam wucewa aka yi da ita lullube zuwa dakinta.

Ni kuma na shiga hidima da bakina da suka iso yanzu. Ga Affan yana ta bi na uwa jela ran nan a bace, na rasa abin da ke damunshi, na ce zai ci abinci ya ce kuma a'a

Kaya ma su Khalil duk sun kara canjawa, amma shi bai canja ba.

"Wai wannan me yake so ne, yake ta bin ki kamar bindi?" cewar Hadiza kanwar sannu Sakeena

Na juya kan Affan ina kallon shi kafin na ce "Wlh ban sani ba, na ce ko abinci ya ce a'a."

"To ai wannan baƙin ran tun da suka isa yake yin shi, a can din ma ko ruwa bai sha ba. Kuma ya ƙi yi wa kowa magana" cewar Murja da take cin abinci.

Aunty Habi ma da take shigowa ta ce " Ni ma tun da ta shigo na tambaye shi ko ba shi da lafiya amma ya yi shiru"

Duk maganganun da ake yi yana ji komai bai ce ba. Kuma har lokacin gefen doguwar rigata yana rike a hannunshi, kamar na ce zan gudu

Bayan na sallami duk wadanda suka iso da abinci, ba wai iya bakina ba, har dangin Saratu, Sai da na tabbatar an kai musu komai, kafin na ja Affan zuwa sama.

Gefen gado na zaunar da shi, ina fuskantarshi kafin na ce "Babban masoyina ya aka yi? Me kake so? Wa ya taba ka? Fada min"
Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Na kuma cewa "Ko dinkin ne bai yi ma ba?"

Kai ya girgiza alamar a'a

Murmushi na yi kadan kafin na ce "Mutane sun cika gidan ko?"

Kai ya daga alamar eh.

Bayyanan nen murmushi na yi, saboda tun da naga yana ta kumburi na san mutanan ne suka yi mishi yawa. Shi bai son hayaniya, baya son ya ga ana taro a gidansu.

Gefenshi na zauna cikin sigar lallashi na ce" Ka yi hakuri Affan, daga gobe kowa zai watse ka ji ko"

Kai ya jinjina, kamar ba zai yi magana ba, Sai kuma ya ce "Auntynmu wai Abbanmu aure ya yi?"

Wani abu mara dadi ya taso daga a kirjina, a hankali na daga mishi kai alamar eh. Saboda ba zan iya magana ba

Rai ya kuma ɓatawa kafin ya ce "Amma ba a nan gidan za ta zauna ba ko?"

"A nan za ta zauna mana Affan, ba ka ga an kai ta dakinta ba"

Fuska ya kuma hadewa ya ce "To ni dai ba zan zauna da ita ba, Sai dai in koma wurin Inna ko wurin Momyn su Affan idan sun dawo daga tafiyar da suka yi"

"Za ka ci abincin ko?" na kawar da waccan maganar, saboda kara tayar min da hankali yake yi

Kai ya jinjina alamar eh.

Waya na dauka hade da kiran Yusrah na ce ta kawo min abinci Affan zai ci.

In less than 5mns Sai ga ta dauke da abincin, hannunta daya kuma rike da Haidar.

Abincin ta ajiyewa Affan, ni kuma na dauki, Haidar da zummar ba shi nono, saboda daga bacci ya tashi.

Bayan na ba shi nono, aka kira min mai kwalliya, ta dan kara gyara min kwalliya, na dora wani farin lace mai golden a jiki, haka ta yi min dauri mai kyau. Ni kaina na san na yi kyau. Haidar kuma na canja mishi kaya zuwa yan kanti masu kyau irin wanda Assidiq da Khalil suka sanya. Shi ma Affan irin su ya sanya bayan ya gama cin abincin. Na dauki lace din Maama na sauka zuwa kasa, don in canja mata.

Lokacin da na sauka filin tsakar gidan ya kara cika, dangin amarya ma sun bi layin yan kallo.

Tun da Mc din nan ya hango ni, aka canja waka zuwa "Uwargida ran gida..."

Ai ni da kaina sai na ji takuna ya canja, kamar wata sarauniya ta gaske, tun daga wurin kuma kawaye da abokan arziki suke zuba min kudi har cikin fili, ana ta rafka guda.

Takun rawa nake na kasaita ana dauka ta video ga kudade ana ta zuba min. Dangin amarya sai kallo da rike haba, ana gulma....

Matar J ✍🏻
[12/23, 14:57] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 33*

Daga lokacin da Bashir ya fada min ya kai kudin aure, ban taba jin wata rana da na yi nishadi da farin ciki kamar wannan ranar ba. Jin zuciyata nake wasai kamar an yi min sharar bakin ciki.

Shi ya sa da dare na sha bacci sosai, dama ga gajiya, dakyar na tashi da asuba, na yi sallah muka shiga hidimar abun kari, su Affan na fara sallama, saboda Babansu ya ce su tafi Islamiya, ai an gama biki.
Sauran mutane kuma zuwa karfe tara mun sallami kowa da abun kari.

Zuwa shadaya kuma baƙi duk sun fara watsewa, musamman dangin Bashir da ƴan'uwan Sakeena wadanda suka yi mana kara.

Wadanda suka rage daga Samira, Badiyya, Yusrah, Goggo Saude, Aunty Na'ima da Maryam. Su kuma duk a bangarena suke. Sai Murja da ba ta bi 6an Ruma ba, saboda za ta shiga cikin gari.

Ina zaune a falo bayan na yi kintsa kaina cikin atamfa doguwar riga da ta sha stone work Ina ba Haidar cerelac Murja ta shigo.

Bayan ta zauna ne ta ce "Uwargida ana can an fama da amaryarki, ta zo ku gaisa ta ki"

Baki na tabe ba tare da na ce komai ba, saboda ni ban san irin wannan sabuwar tsirfar da take yi ba. Matar da take zuwa har dakina, amma yanzu ta zo da sabuwar gulma.

Ni dai ta kan maganar ma ban sake bi ba, su Yusrah ne ke ta tattauna maganar.

Misalin sha daya su Samira suna shirin tafiya dangin amaryar suka shigo, amma babu amaryar.

Tun da suka shigo idanunsu a ko wace kusurwa ta dakina, tun jiya suke zuwa min kallon kurillar daki suna kus-kus. Yanzu din ma muna gaisawa suna karewa dakin kallo, a haka mu ka yi sallama, suka tafi, ni ma na saka hijab di ta don yi wa su Yusrah rakiya zuwa tasha.

Ban baro tashar ba sai da naga motarsu ta tashi, shi ya sa ban dawo gidan ba sai sha biyu saura.

Da yake na bar Uwani ban damu ba, na san za ta yi komai kafin in dawo.

Lokacin da na dawo har ta sauke farar shinkafa, saura miya.

Shi ya sa ina sauke Haidar, ban huta ba, na shiga kitchen. Don taya ta sauran ayyukan.
Chapter 41 · 0% Book details