← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 44

Sashe 15

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki mutanen kauye, wallahi yaransu na ganin rayuwa idan za a yayesu, yaro ya tashi cikin dare yana kuka a mika mishi tuwo ko koko me sanyi, amma ji wai nan duk kayan yaye ne kamar za a bude shago." na yi maganar a zuciyata, a fili kuma sai na ce

"Ina za ki kai Ramlan yaye?"

"Ba ko ina, dama kawata Rahma ke yayesu to yanzu kuma ba ta nan, suna waje ita da mijinta"

"To ni zan yayeta."

Waro ido ta yi hade da zuba su a kaina, ba tare da ta ce komai ba.

"Da gaske nake fa"

"Don Allah ki ji da kanki, yaushe za ki iya da rigimar yaye?"

"Ba za ta yi min rigima ba" cikin dariya na yi maganar.

Ita ma dariyar take lokacin da take fadin "Don Allah rufa min asiri"

"Kin san Allah ni zan yayeta a cire maganar wasa."
Kallo na take yi cikin ido cike da mamaki.

"Gaske nake fa"

"To ai shi kenan, idan ta dameki ai kya maido ta"

Murmushi na yi ina tuna shawarar Samira da Badiyya lokacin da na fada masu matsalata, masalaha ta farko da suka ba ni, shi ne in ja yaranta a jikina, in rika kyautata masu, mai ɗa mahaukaci ne, muddin ina hakan, zan saye zuciyar mijina, ta kishiyata da kuma yaran, sannan zai wahala ya rika ganin laifina, dalilin da ya sa kenan nake son fara yi masu bauta, tun da na fahimci muddin ka auri mai mata da yara sai ka zama kamar bawa. Ko ba komai za ka samu karɓuwa wurin miji.

Matar J✍🏻
[12/18, 06:38] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 13*

Kamar wasa na dauki yayen Ramla, kuma ba ta yi mini wani rikici mai yawa ba, ranar farko da ta biyu ne kawai mu ka sha rigima, daga nan kuma ta hak'ura, dan rikicin ba yawa.

Dalilin ya haddasa karin shakuwarmu da yarinya fiye da baya, son yarinyar da kaunarta ya kuma shiga zuciyata.
Komai nake Ramla, duk wani makusanci nawa idan mu ka yi waya sai ya tambaye ta. Musamman Ummana, kanwata Yusrah da kuma Maryam.

A bangare daya kuma kimata mutumcina sun karu sosai a idanun iyayenta, musamman Babanta da kullum nake ganin tsantsar kaunata a idonsa. Baya son ya ga ɓacin raina, yanzu zai damu har sai ya ga na warware.

Cikin sati daya da yaye Ramla ta warware sosai, babu wata rigima sai wasa.

Sosai iyayenta ke mamaki, musamman Mamanta ta kan ce "Ramla ce kawai yayenta ya yi sauki. Babu rigima babu ciwo"

Mun shiga sati na biyu da yaye Maman Khalil ta shiga shirin tarar kawarta Rahma.
Wacce za ta dawo daga China, wai mijinta ne aka tura aiki can shekararsu biyu.

Ni har na kosa in ga wannan Rahma, don kuwa hatta sabon dinki Maman Khalil ta yi masu iri daya, sannan ta yi wa yaran, gidan Rahman an je an share an zuba sabbin furnitures, na rasa irin wannan kalar kawance na amana, babu bakin ciki ko hassada. Ni dai nawa ido, wani lokaci kuma idan ina son yawo sai in bi ta zuwa wani wurin.

Ranar kuwa da za su dawo,, wai jirginsu karfe uku zai yi landing.

Maman Khalil tun biyu ta kammala komai na abinci aka kai gidan Rahman.

Ni ma sai na shirya yarinyata, cikin doguwar riga yar kanti mai kalar purple Amma light, kame gashinta na yi da ribom mai kyau, bayan na yi mata kunshin gargajiya da uwarta ke ta santi, ba ta gajiya da kallon kafar.

Karfe biyu da kwata na je bangaren don kai mata Ramla saboda na ga da yaran za ta tafi dukkansu.

Amma yarinyar nan fir ta ki bin su, wai sai idan da ni za aje, iya wayo mun yi mata amma ta ki bin su, haka suka tafi suka bar mu a gida.

Iskar wajen nake bukata dalilin da ya sa kenan na dakko tabarma na shimfida mana a baranda bayan na aje mata biscuit, cheese da happy Hour.

Wasanta take yi sosai, yayin da ni kuma hankalina ya koma kan wayata, ina bibiyar wani group a Facebook.

Comment din mutane shi ya fi dauke min hankali, wani ya ban dariya wani ya ban takaici.

Karar gate ce ta sanya ni dago kaina hade da zuba mishi ido, cike da mamakin yadda yake takowa a kasa.

Wani banbarakwai na ji, saboda ban taba ganinshi ya shigo gidan a kafa ba.

Ban dauke idanuna a kanshi ba har ya kara so in da nake zaune

"Me ya faru da motar, lafiya?" Na jefa mishi tambayar da ke ci na.

"Ina Maman Khalil?" shi ma ya tambaya yana kokarin zama a gefenmu

Idan na ce maku raina bai baci ba na yi karya gaskiya. Haka nan na daure na ce

"Sun fita"

"Tun yaushe kuma?"

"Ba jimawa" na kuma amsashi hankalina a kan wayata.

Kamar ba zan kara cewa komai ba, sai kuma na kasa jurewa na kara cewa "Ya na ganka a kafa, lafiya dai ko?"
Na karashe maganar ina kallon yadda idanunshi ke kam sashen Sakeena, da alama kuma hankalinshi ba ya tare da ni.

Siririn tsoki na ja, wanda ya sanya shi juyowa yana kallona

Shiru ya ratsa wajen, yayin da na janye duk wata fara'a da ke kan fuskata, na kuma mayar da hankalina a kan wayata sosai, kamar ban san yana wurin ba.

A can kasan zuciyata wata irin kuna nake ji, ni a haka rayuwata za ta kare a tsakanin wadannan mutanen biyu, na mayar da kaina tamkar wata baiwa don dai kawai ni ma ya zama tauraruwata ta yi haske, na sadaukar da ra'ayina don kwanciyar hankalin kowa amma ya zama duk a banza.

"Anya matar nan ba asiri ta yi masa ba kuwa?" na yi tambayar a hankali wanda labban bakina ne kawai suka motsa.

To idan ba aikin asiri ba, ta ya za a ce duk irin kyautata mishin da nake yi, amma ya kasa dakushe koda daya bisa ukun tasirinta a zuciyarshi. Ina kallon shi ya mike zuwa dakina, amma na ƙi bin shi. Kamar 5mns da shigar shi ya rika kwaɗa min kira

Dole na mike ba tare dana amsa ba na nufi dakin, ji nake ma kamar ina shiga in rufe shi da duka, sai dai mugun kwarjini yake min daga shi har matarsa, duk yadda na shirya rashin mutunci in yi wa Maman Khalil muna hada ido sai in ji duk na daburce.

Na san hakan baya rasa nasaba da yadda ta kame kanta da kuma girmanta, saboda duk iya sharrina da kuma rashin kaunata a kanta karyata in ce ga shi yau ta yi min abu da bai dace ba, idan ma ta yi sai ta ba ni hakuri.

Abun da na sani dai kawai shi ne tabbas ta iya rike miji ta ko wane bangare.

Kuma gaskiyar Ummata, haka ko wace mace ya kamata ta zama kamar Maman Khalil ciki kuwa har da ni.

Saboda hakan ne zai ba ta damar cike duk wani gurbi a zuciyarsa.

Sannan a bangaren kishi ma ta zama mai wayo, ta kame miji ta can kasa, ta kyautatawa abokiyar zama, Sanna ta ja girmanta, tabbas kame kai, da girmama shi yana jefa kwarjini a idon abokan mu'amala ciki kuwa har da makiya.

Shigata bedroom din ke da wuya, na ji ya janyo ni hade manna ni a kirjinsa, ya mayar da hannayensa a bayana, har zuwa lokacin da bugun zuciyata ya daidaita.

Kafin ya dogo kaina, ya zuba min idanunsa da suka canja launi, ba zan iya jure kallonsu a haka ba dalilin da ya sa kenan na lumshe nawa.

Bakinsa ya hada da nawa, yayin da hannayensa ke aika min da sakon da ba zan iya jure karbarsu a tsaye ba, dole na fara kokarin janye jikina zuwa gado.

Da ya fahimci me nake son yi, da kansa ya kai ni inda nake bukata.

Jin kiran sallah bai hana Baban Khalil biyan bukatarsa ba.

Cikin dabara na ture shi daga kan jikina, saboda kunnena ya jiyo min alamun tafiyar mutum.

Duk da jikina ba kwari hakan, bai hanani yin hanzarin fita falo ba, tare da yaye labulen window da zai sada ni da tsakar gida.

Daidai Maman Khalil na shigewa part nata, kafadarta dauke da Ramla. Wannan ya tabbatar min da ita ce ta same mu a yanayin da bai dace ba.

Haka nan sai na ji na kasa fita in yi mata sannu da zuwa, kuma ban fadawa Abbansu Khalil matarsa ta yi mugun gani ba. Bakina na kame abu na. Har ya kintsa jikinshi zuwa part dinta, ko ya suka karasa oho.

Ni dai ban shiga part dinta ba, kamar yadda ita ma ba ta leko ko kofa ba.
Shi kuma gogan bai shigo gidan ba sai takwas na dare. Ya ci abinci hade da yin wanka, bai bar sashena ba dai sai goma na dare

Zuciyata nata sake-sake a kan Ramla, wata na fada min in je in dakko ta, wata kuma na hanani, amma sosai ba na ji dadi, ji nake kamar duniyar ba kowa.

Wani sanyin dadi na ji, lokacin da ya kara dawowa kafadarshi saɓe da Ramla tana bacci.

Sam ban yi tunanin za a kawota ba, saboda idan ni ce Maman Khalil na samu mijina da abokiyar zamana a lokacin da nake ganin kamar ta fita a girkinta, sannan ya kuma komawa dakinta ya ku san shafe awa daya, to yakin ranar ba mai karewa da wuri ba ne, sannan zan karbe yarinyata, in hana yarana zuwa gurinta.

Da kansa ya lallabata ta kwanta, sannan ya shafa cikina da ya dan fara fita yana fadin

"Na kosa in shigo in sameki da Baby a gabanki fa, za ki yi matukar kyau"

Murmushi na yi kafin in ce "Ni kaina ina son ganin wannan ranar, sai dai kuma in tsoron haihuwa"

Zaunawa ya yi kusa da ni, hade da kama hannuna cikin sigar kwantar da hankali ya ce " In sha Allah lafiya za ki haihu, kamar yadda Maman Khalil ke haihuwa cikin sauki, ki daina damuwa a kan hakan, saboda kullum ina miki addu'a"

Sosai na ji kwarin gwiwa duk da ban yi magana ba.
Chapter 15 · 0% Book details