← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kuma sai na yi mafarkin wa'adin da aka dibarwa Affan din ya cika, muna zaune ba zato ba tsammani sai ga wasu fararen larabawa su biyu, da shiga irin ta larabawan, wai sun zo sun kama Affan yana zaune yana wasa suka ce wa'adin da aka debar mishi ya cika.

Duk mutanen wurin babu wanda ya yi kokarin karbar Affan sai ni.

Muka fara kokawa da mutanen ina kuka, amma suka karbeshi da karfi yana kuka ni ma ina kuka, irin kukan nan mai nuna tsananin damuwa.

Ganin sun fi karfina sai na ce masu to su yi hakuri su ba ni shi mu yi bankwana.

Sakinshi ke da wuya sai ya fado jikina yana kuka, ni ma ina kuka wata sabuwar kaunarsa na ratsa jikina, cikin kuka na ce

"Affan ina sonka wallahi, kar ka ga kamar ban damu da kai ba amma ina sonka sosai, don Allah ka yafe min rashin kulaka da nake yi."

Yaron bai yi magana ba sai dai kuka, da karfi suka banbareshi yana turjewa suna jansa, har muka daina hangensa da jin kukansa.

Ina zuwa nan na farka.

Sosai mafarkin ya ban tsoro, na rasa ta ya zan ba shi fassara.

Jiki a mace na yi sallahr asuba, hade da rokon Allah ya sada ni da alkairin mafarkin sharrin kuma ya tsare ni da shi.

Ina idarwa na kira Maman Khalil

"Turo min lambar Maman Farhan"
Abin da na fara fada kenan bayan ta daga

"Lafiya?" cike da mamaki ta tambaya

"Lafiya kalau." Ni ma na ba ta amsa, har yanzu muryata a sanyaye take.

"Kodai alamun haihuwa kike ji"

Dariya na yi kafin in ce "Ni ina na san wani abu alamun haihuwa. Kawai ina son yin magana da Affan ne"

Ita ma can dariyar ta yi "Ai alamun haihuwa idan ya zo ko ba a fada miki ba za ki gane. Yau kuma da Affan kika tashi ba yar gold dinki ba, Affan din da kike koro min idan ya zo inda kuke."

Na kuma yin dariya "Ni dai turo min, yau soyayyarmu ce ta tashi."

"OK." ta fada

"Yarinyata ba ta tashi ba?"

"Ba a nan ta kwana ba ai, tana wurin Inna"

"Ni na fi natsuwa ma da zamanta a wurin Innar?"

Dariya ta yi sannan ta ce "Kin ci bashi, sai mun dawo an jima kadan sha Allah za mu ta so."

"Ai gara, kwana dayan nan kamar shekara nake ji, Allah ya kawoku lafiya"

"Amin" ta fada hade da yanke kiran.

Sai da na ji muryar Affan sannan hankalina ya dan kwanta.

Misalin karfe goma kuma sai ga kiran Oga

"Ni ɗin ma da ba kya so ina lafiya." abin da ya fara fada kenan bayan na daga

Siririyar dariya na yi "Ma sha Allah da kake lafiya"

"Ga mu nan zamu taso yanzu sha Allah"

"Allah ya kawo min ku lafiya"

"Amin ya Rabbbb! Sannan ki shirya idan na dawo za ki yi biyan bashi, na gaji da kullum ki ce min ciki."

"Amma dai Maman Khalil ba ta kusa da kai ko?"

"To idan tana nan fa, ba ta san muna yi ba ne? Cikin jikinki na waye?"

Dariya na yi sosai daga bisani na yanke kiran ba tare da na ba shi amsa ba.

Matar J ✍🏻
[12/22, 15:01] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 17*

A yadda muke waya dasu na san sha Allah 7:30pm zuwa 8:pm sun shigo gida.

Dalilin da ya sa kenan karfe biyar na fara shirin abincin tarbarsu, kowa abin da yake so na yi niyyar yi mishi, Oga tuwo, Maman Khalil dambu, yarinyata kuma danwake.

Tun da nake kira ba ta cewa komai amma haka nan zan sanya a kanga mata wayar a kunne in yi ta surutu tana ji, amma dazu da na ce "Me kike so in dafa miki" Sai cewa ta yi "An wake" Ina jin su Maman Khalil na mata dariya, ni ma na yi dariya sosai.

Shi ya sa zan yi mata daidai cikinta.

Zuwa 7:pm kuwa na kammala komaina har da watsa ruwa, na haye sallaya don gabatar da sallahr magriba, saboda tun 6:47 aka yi sallah.

Ina kan sallaya na ji sallamar Rahma don haka na fito, ina tunanin ko yara ta maido.

Amma kuma sai ban ga yaran ba.

Gaisawa mu ka yi sannan ta ce "Kun yi waya dasu Sakeena ne?"

"Eh tun dai wajen shida da mu ka yi bamu kara ba, dama jira nake in idar da sallah in kirasu in ji suna ina." na ba ta amsa ina kallonta.

"Ok. Sun iso tun dazu amma sun buga ma wani mota yanzu haka suna asibiti"

Na yi saurin sakin casbahar da ke hannuna tare da fadin "Subhanallah! Amma su ya suke?"

"Su kam suna lafiya, motar dai wancan ce ta samu matsala."

Na sauke ajiyar zuciya mai karfi "To yanzu ya aka yi?"

"Zuwa na yi mu je tare."

Ban yi wani dogon tunani ba na ce "To mu je kawai"

Ita din ma ba ta ce komai ba, ta yi gaba na ja kofata na bi ta a baya ko wayata ban dauka ba.

Tun da muka fara tafiya ba mai cewa komai tukinta kawai take yi, ni kuma na kosa in je in gansu, ji nake ma kamar ba ta sauri.

Tun da mu ka shiga asibitin nake karo da abokan Baban Khalil da makotanmu wadanda na sani.

Yadda nake ganin fuskokinsu kamar abun babba ne.

Kofar A&E din cike yake da mutane, da yawansu kuwa makusanta ne ga Baban Khalil

Matan da ke wurin basu da yawa maza sun ninkasu yawa.

Sai kallona suke yi suna kus-kus, ga Rahma ta shige ciki ta bar ni a tsaye.

Can kuma sai ga ta, jan hannuna ta yi, tana kokarin boye hawayenta. Ni dai tuni jikina ya gama mutuwa, na rasa duk wani wayau nawa.

Gefe ta kai ni, hade da zaunar da ni a daben barandar wurin .

"Khadija!" ta kira sunana

Daga kai kawai na yi ina kallonta, saboda bakina ya yi nauyi ba zan iya amsawa ba

"Sakeena, Ramla da Basheer suna cikin wani hali, ki sanyasu a addu'arki, sun ji ciwo amma dai sha Allah ana ganin akwai sauki." Ta karasa maganar hade da share hawayen da ke bin fuskarta. Daga bisani kuma sai ta rushe da kuka mai sauti.

Ni dai ina jin mutuwar zaune na yi, don kuwa ko zuciyata ma a lokacin ba ta aiki, saboda ni dai ban ji na tuna komai ba.

Kwakwalwata ma a cunkushe take, ta yi jingim.

Sosai Rahma ke kuka, har sai da wasu mata da ina jin kawayenta ne ita da Maman Khalil su ka iso asibitin suka karaso gurinmu suna ba ta hakuri, kuma su din ma kukan suke yi.

Ni dai nawa ido kawai, bayan shi ba na jin akwai wani abu a jikina da yake aiki.

"Ku kai ni in gansu." Da kyar na iya kalato maganar a bakina.

Ina jin su suna ta gardama wasu su ce a kai ni wasu su ce kar a kai ni.

"Ku kai ni in gansu don Allah." na kuma fada da kyar.

Rahma ce ta mike tare da fadin "Ina zuwa"

Ban san ina ta je ba, can kuma sai ga ta, kama ni ta yi ta mikar, sannan ta ce "mu je."

Kamar rakumi da akala haka nake bin ta, har zuwa wani daki, gaban wani gado muka tsaya, ta yaye zanen da aka lullube mara lafiyar.

Cikin kaduwa na ja baya ina kallon Rahma, ita ma ni take kallo.

Hannu ta sanya hade da share hawayenta.

"Khadija kin ga aminiyata, kawata ta amana, masoyiyata, abokiyar sirrina, mai share min hawayena. Yau ta tafi ta bar ni ni kadai." kuka ta kuma fashewa da shi mai sauti.

Sauri na yi na juya gadon da ke bayana, saboda wani tunani da na yi, bayan zuciyata ta dawo aiki cikin sauri.

Da sauri na kai hannu na yaye zanen da aka rufe koma waye a kwance

Ramlata ce kwance cikin jini hannunta guda daya fit ya fita, idan ka dauke wannan ciwon babu ko kwarzanen wani ciwo a jikinta. Idanuwanta a lumshe kamar tana bacci. Sabanin Maman Khalil da ta fita a kamaninta, hatta hakoran bakinta ba na jin akwai saura.

Saurin sakin zanen na yi, na nufi kofar fita, har ga Allah ban san ma ina nake zuwa ba, ban san ma wacece ni ba, Kwakwalwata ta daina aiki, tafiya kawai nake yi ko waige ba na yi.

Daga nan kuma ban san ya aka yi ba

Kawai dai na farka, na ga kanwar Ummata da ke Zaria a gefena, da yayar Baban Khalil,

Bin su kawai nake da kallo, su kuma suna ta min sannu.

Ina jin ma fadawa mutane a akai na farka, shi ya sa wannan ya shiga wannan ya fita.

Da na fahimci su dan rage shigowa, yunkurawa na yi da zummar tashi, amma kafin hakan cikin sauri Yaya Habi (yayar Baban Khalil) ta mayar da ni tare da tambayata ina zan je.

Bakina ya yi nauyi, da hannu na nuna mata kofar toilet.

Ita ce ta kai ni, na yi fitsari hade da yin brush na fito, sai kuma kanwar Mamata (Inna Saude) ta miko min kofin tea mai kauri.

Gefe na kawar da kaina, ko ganinsa ba na son yi.

"Sha Khadija ko don abun da ke cikinki" cewar Aunty Habi tana lallashina.

Yadda suka rufu a kaina ne ya sa dakyar na dan kurba kadan na ba ta, sannan na mayar da kaina a kan filo na yi shiru.

Fuskar Maman Khalil ta fado min, wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga ramin idona.

Cikin hanzari na tashi, kamar ba ni ce dazu na kasa tashi ba.

Wannan karon ma yaya Habi ce ta yi saurin dakatar da ni, na zuba mata idon cikin dabara na fizgo maganar da nake son yi

"Ina Maman Khalil, Ramla da kuma Baban Khalil? Me ya faru da Maman Khalil na ga kamar fuskarta a kumbure, yarinyata kuma fa?" na karashe maganar cikin muryar kuka ina kallonta.
Chapter 20 · 0% Book details