Sashe 9
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To tunda kin nemi sulhu zuwa za ki yi inda nake ai ki lallaba ni domin ni ma ba ni da wata lafiya rashin lafiyar abokina ta dame ni a kwanakin nan Ina buk'atar mai kula da ni ta ba ni magani ta kuma kwantar mini da hankali da kalamai masu dad'i zuciyata ta daina yi mini tunanin kamar ban yi sa'ar iyali ba." Cike da mamaki na furta." Yallabai duk me ya kawo wannan maganganun don Allah." Ya nisa kafin ya sake cewa." Kulawar da abokina yake samun wurin iyalinsa shine ya sanya nake jina kamar maraya gashi dai babu abinda Allah ya rage ni na jin dadin duniya amma matata ta na yi mini wulakanci." Dariya maganarsa ta ba ni wai wulakanci wato shi baya duba abinda yake yi mini a matsayin wulakanci saboda namiji ne duk abinda ya yi daidai ne." Na yi dariya 'yar kad'an kafin na ce." To shi ba ka ganin bashi da lafiya ai dole a ninka bashi kulawa ko ka manta lokacin da ka yi mura a gidana yadda na dinga lalla'baka ina rarrashinka kamar jariri." Ya ce." Ni dai na gaya miki zan sanya a kawo miki ticket da za ki same ni anan abuja gobe kafin mu wuce saudiya ki ba ni magani kada na tafi da lalura. A dukunkune yake maganar amma na gama fahimtar inda ya dosa wannan ya nuna mini cewa a mutukar bukace yake dauriya ce kawai da son dole sai an nuna iko ba zai neme ni ba muddin ba ni na neme shi ba yanzu kuwa dana tsaga billena na kira shi kai tsaye yake neman abu a wurina. Ni ma saboda tawa biyan buk'atar yasa babu ja'inja na amshi gayyatarsa nasan ta wannan hanyar zan iya samun abinda nake so kai tsaye tunda Allah Ya riga ya ga zuciyata da munufaar da zanyi hakan. [9/18, 9:57 AM] Aunty B: 85 Direbansa ya turo da mota ya d'auke ni bayan saukata a garin abuja kai tsaye gidanshi da yake maitama ya nufa da ni kamar yadda ya umarci direban nasa mai suna Ade wani bayerabe mai gaggausan jiki da rashin fara'a. Sai dai da yake ya san matsayina duk cudewar fuskarsa bai hana shi risina mini ba. Gidan kwatankwacin na Legos me d'auke da bangarori da dama kuma cike da ma'aikata da masu tsaro da iyayen motacin da na tabbatar da cewa wasu ma sai a yi shekara ba a hau su ba. Wurin ajiye motoci ya nufa domin gyara parking yayin da nake hangen maigidan da Yusi can daga nesa bakin wata bukka irin ta hutawa. Yana kashe motar ya fito da sauri ya bude mini kofa har yana dan risinawa na fito a hankali Yusi ya tawo a guje ya rukunkume ni yana dariya mamaki mai yawa ya lullubeni ganin yadda yaron ya yi wata iriyar ki'ba kamar wanda aka hura ya zama kato Na dinga binsa da kallo irin na mamaki da al'ajabi wannan wace irin ki'ba ce. Maigidan ya k'araso wurin yana sanye da jallabiya fara mai karamin hannu kansa da fara hula irin ta larabawa as'usul idonsa da farin gilashinsa. Na dube shi na 'yan dakika na fahimci zurmawarsa ya kara tsukewa dama abinka da mai karamin jiki ko dai da gaske yake shima din bashi da lafiya. Ade ya fito da k'aramar akwatina da na zubo kayana kala uku a ciki ya tsaya suna magana ni da Yusi muna gefa ya rike hannuna gam a cikin nasa yana cike da tsananin farinciki ni kam kallonsa kawai nake yi har na gaza ha'kuri na ce." Kai me ka samu ka ke ci ka zama d'an lukuti kana duba mudubi kuwa?" Dariya ya kama yi yana cewa." Abinci kawai nake ci ai an yi hutu makaranta Mama amma ina hawa gym na tsinka jina na." Na dube shi a lokacin da ya zo ya tsaya gabanmu Yana cewa." Ke kuma daga zuwa sai tuhuma." Yar dariya na yi a hankali na ce." Abin ne ai da mamaki wallahi kibar ta yi yawa." Ya wuce ciki yana cewa." Ke ki ka gada masa ai ba kowa ba.'' Yusi ya kamo hannuna muka bi bayansa yana ta yi mini labari yaran Alhaji Amadu wanda suka zama abokansa jinsa kawai nake yi amma ban ce komai ba sai dai zuciyata cike take da farincikin ganinsa cikin walwala da kyawun yanayi tare da lafiya da suttura irin ta 'ya'yan manya a jikinsa. Ga gida har gida babu abinda babu a ciki ko 'diyar shugaban kasa za a iya ajiyeta a gidan amma kash babu mace a cikinsa asalima ya tanadi gidan ne kawai domin idan ya zo garin ya sauka a cikinsa tunda karfin zamansa ya fi legos. Ya d'an ba ni tausayi kad'an domin kamar yadda ya fad'a cewa Allah bai tauyeshi da komai ba na jin dad'in duniya sai ta bangaran iyali, Ina ganin da zamansa anan yake dindindin zan iya ha'kura da can na zauna tare dashi to karfin zamansa ba anan yake ba, ni kuma gabad'aya zaman legos din ne ya fice mini daga raina. Wajan cin abinci cike yake da cima kala kala da kayan marmarin dogon daning ne mai d'auke da kujeru takwas gaba da baya tsarin gidan gwanin ban sha'awa kuma a gare cikin tsabta kasancewar akwai masu aiki maza da suke yi hidima a gidan koda baya nan. Sama ya hau nan turarkarsa take Ade ya shigo da akwatina ya ajiye ya fita, Yusi ya tashi da sauri ya bi bayan shi yana kiran sunan shi na bi yaron da kallo da alama akwai sabo a tsakaninsu. Ajiyar zuciya na sauke a nutse nake bin falon da kallo ya tsaru ainun ya ji kujeru da labuleye na alfarma hotonsa dana iyayensa gasu nan birjik a falo can na hangi na baby Nana kato a wata kusurwa a jingine ba a kafe shi a bango ba. Na jima tsaye ina duba hoton na share kwallar da ta ciko a idona na d'auka a gidansa na legos kadai ya ajiye hotonta ashe yana dashi a nan d'in ma. Yana ba ni tausayi sosai a wasu lukutan domin shi din abun tausayi ne.... Sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na hau saman tunda nan naga ya nufa ai nasan wulakanci da shan kamshi zansha shi nasan sai dai na kai zuciyata nesa. D'akuna hud'u ne kowanne a rufe sai guda daya da naka key a jikinsa ta waje hakan ya tabbatar mini da cewa yana cike ina ta'ba kofar kuwa ta bude na shiga da sallama a bakina. Ya fito daga bandaki daidai lokacin da na shiga d'akin wanka ya yi ya ce." Shigo ciki sosai mana." Na kàrasa na zauna gefan gado ina dubansa da gaske fa ya rame yanzu na sake gazgatawa da babu riga a jikinsa sa towol da ya dauro. Ya dube ni yayin da yake ko'karin zama kusa da ni yana fad'in." Ya gajiya?" Na daure a hankali na ce." Alhamdulillahi ya jiki ashe da gaske dai ba ka da lafiya Baba." Ya ce." Lafiyata lau me ki ka gani?" Kai tsaye na ce." Ramewa na ga ka yi?'' "Fargaba ce kawai wallahi na jima ban ga ciwon da ya tayar mini da hankali kamar na Alhaji Amadu ba sam ya'ki jin magani, yana nan fa sai dai a kwantar a tayar na gaya miki yana asibiti a yanzu amma jibi za a yi masa transfer zuwa asibitin makka. Cike da alhini na ce." In sha Allahu zai samu lafiya kaima ya kamata ka cire damuwa daga ranka kada wani ciwo ya sameka ka rame fa sosai Baba dama kai ba jiki ba." Yana yi mini wani irin kallo ya ce."Abin har da zolaya Amina." Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ban isa ba, kawai dai ramar taka ce ta d'an tsorata ni Yusi kuwa kamar wanda ake hurawa." Ai irin jikinki ne dashi na gaya miki ke ce ki ka gada masa 'kiba. Ya tashi ya nufi wardrobe yana fito da kayan da zai sanya ya ce." Da daddare idan kin huta za mu je ki duba shi ko?" Na ce." In sha Allahu rabbi." D'akin ya yi shiru na mintina shi yana ta hidimar shirya jikinsa yayin da ni kuma nake bin d'akin da kallo karaf idona ya sauka kan dirowar dake gefan gadonsa karamin hoton Samira ne irin wanda ya ajiye a gidansa na legos wanda na sanya ya cire shi. Kishi na ji ya soke ni, ai ta riga ta mutu shekara da shekaru ya kamata ace yanzu ya cire ta a ransa amma ace kowane gidansa da hotonta a ajiye ban san menene amfanin hakan ba. Ya juyo yana kallona ni kuma na janye idona daga kan hotonta ina ko'karin danne abinda nake ji. Bai ce mini komai ba ya zauna gefan gadon tare da gyara zaman hoton dukda ba abinda ya yi ganin haka ya sanya na tashi tsaye sai ya yi saurin fad'in." Ki yi wanka sai mu sauka mu ci abinci ko?" Ban ce komai ba na nufi bandakin zuciyata babu dad'i hotonmu ya fi kamata a ce ya ajiye gefan gadonsa ba na wadda bata raye ba, na fahimci har yanzu akwai sonta a cikin zuciyarsa hirarta ne kawai ba ya yi mini tunda ya fahimci ba na so. Muna cin abinci yake gaya mini Yusi a gidan abokin nasa yake kwana tare da yaranshi da yake matarsa daya Hajiya Maryam auran saurayi da budurwa suka yi kuma da yake 'yan boko ne sun tsara rayuwarsu haihuwa uku sukayi suka dakata sun fara da mace mai suna Nusaiba wadda suka aurar da ita shekara biyu da ta wuce anan abujan tana auran babban ma'aikaci a central bank. Sai kuma Salim wanda yanzu yake matakin shekara ashirin Adam kuma sha bakwai. Hajiya Maryam yar boko ce kuma muguwar 'yar gayu ce irin matan nan ne masu kyawun jiki da ado da kwalliya shekarunta sun buya sosai idan ka kalleta sai ka d'auka bata fi talatin ba amma ba haka ba ne shekarunta arba'in da d'aya a yanzu tsabar gyaran jiki ya sanya komai nata yana nan cif mussaman kirjinta tana kula dasu sosai kuma Yar kasuwa ce domin manyan shop ne