← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 40

Sashe 18

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Shi kadai ne zai yi mini maganinki tunda ai kin gagara Amina kin nunawa duniya cewa baki da na gaba dake kin fi 'karfin kowa ciki har da mahaifinki ni dai muddin ina da hakki akanki to fa ba zan daina cewa Allah Ya saka mini ba."
Ya sanya hannu zai bude kofar domin fita na sake tare hanyar a karo na biyu cikin jarumta na ce." Ubangiji ba mutum ba ne kamar kowa kuma akan yi masa lefi a tuba ya yafe duk sharri da bala'in da kake nema dashi da izinin Allah ba zai same ni ba domin kuwa wanda ya hallice ni ya fi ni sanin menene a zuciyata Ina ce dai idan na gaya maka gaskiya shikkenan ai ikon hukunci ko azabtarwa ko d'aukar rai duka ba a hannunka suke ba. Na yi kuskure tabbas a lokacin da na tabbatar da cikin a jikina na yi kokarin fitar dashi kamar yadda Dr Iliyas din ya gaya maka. Dana fahimci bai zube ba sai na ha'kura kawai na barwa Allah kuma na ro'ke shi gafara a sa'in da na kuskure masa kuma ina da tabbacin ya gafarta mini, abinda zan iya gaya maka kenan domin a duniyar nan babu wanda baya kuskure Ina me baka ha'kuri hakan ba zata sake faruwa ba."
Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da al'ajabi ni kuwa ban ji komai ba domin kuwa na lura rufe maganar da nake yi bashi da wani amfani gwara kawai na sanar da shi gaskiyar lamari tunda ya fi ni sanin hujjata ta yin hakan.
"Hakan ba zata sake faruwa ba." Wannan maganar ya fad'a kafin a gaggauce ya bud'e kofar d'akin ya fice da saurin gaske.
Na jima ina nazarin maganar da ya furta sai na shiga zullumi da tunanin domin ya yi ta ne a d'ukunkune karshen dai hukunci shine saki a shirye nake da kar'bar gakan daga wajensa.

Da yamma muna zaune a falo anti Yagana suka yi waya da Babanmu nan take sanar dashi kwana biyu ni ce ban ji dadi ba shine dalilin da ya sanya ba mu sake zuwa ba tun ranar da aka sallameshi daga asibiti. Na ce mata ta gaya masa na ji sau'ki don zai iya tashin hankalinsa jin ba ni da lafiya
Duk da ta gaya masa haka kuwa washe garin ranar sai da suka zo duba ni tare da Baba Sule sun jima a gidan muna tattauna sha'anin Hadiza domin kuwa kowa ya riga ya mik'a wuya don a zaman kutu na farko da aka yi ba a hangi sasaauci a tare da alkalin ba. Yanzu tana can gidan kaso kafin shari'ar ta kammalu a yanke mata hukunci. Bayan sun tafi da kad'an sai ga Gwaggo Hamusu ya kawota to ita tare muka yini har dare sai bayan Isha'i, tukkuna ya taso daga shago ya zo ya d'auketa a babur ya kai ta gida.
Sai da na warware sosai sannan na gayawa Sahura abinda ya faru da ni amma ban gaya mata cewa ni ce sila ba. Ta jajanta mini sosai tana fad'in Allah bai yi rayayyu ba ne itama haka tasha wannan wahalar lokacin da nata tagwayen suka zube ta ce mini za ta zo ta duba ni ranar da babu aiki.

****
To tafiya ta mik'a sosai don yau sati uku kenan da abinda ya faru amma tsakanina da maigidan muguwar gaba ce ta 'kullu. A zahiri shi ya d'auki lamarin da zafi na sani kowaye aka yi wa haka ba zai ji dad'i ba amma ya kamata ace ya yi hakuri ya kar'bi tubana tunda na gane abinda na yi ba daidai ba ne. Na kira shi ya kai sau bakwai tun bayan tafiyarsa na tura text amma daga karshe ma sai ya sanya ni a black list idan na kira duka layinkansa busy. Ban damu ba da farko saboda a ganina duk fushin da zai yi na dan wani lokaci ne zai ha'kura ya sauko ya kar'bi tubana ni kuma na kiyaye a gabana. Na dai ji dad'i sosai da ya rufe maganar bai gayawa kowa ba dama kuma kusan haka halinshi yake yana da zurfin ciki mussaman akan mas'ala irin wannan.

Duk da damuwar da ta fara yi mini 'kawanya ban yarda anti Yagana ta fahimci wani abu ba har dai ta tattara ta tafi bayan an yi zaman kotu daya da ita inda ake tsammanin zama na gaba za a yanke hukunci na karshe.
Bayan tafiyar anti Yagana Ummansu Hadiza ta zo mini a ki'dime tana kuka sosai duk ta figale ta lalace wai na taimaka na daukarwa Hadiza lauya domin kuwa a cikin lauyoyin gwamnati an rasa wanda zai kar'bi case din ganin haka ya sanya kowa yake tunanin zama na gaba Hadiza za ta san matsayinta.
Na rasa yadda zan yi da ita domin dai Ina ji Ina gani ba zan daurewa karya gindi ba. Hadiza ta fad'a da bakinta tana da hannu dumu-dumu shedu sun shaida to me zai sanya haka kawai na d'aukar mata lauya saboda son zuciya. Kuka take yi sosai tana gaya mini halin da Alhajiji yake ciki shi ma yana can hannun 'yansanda a jos suna azabtar dashi mahafinsa da 'yan uwansa da suka uba daya sun ce babu ruwansu ga Hadiza ma za a yanke mata d'aurin rai da rai."
Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita wurin rarrashinta domin kuwa Allah ne kadai ya san irin rad'adin da take ji a cikin zuciyarta.
Ban yaudareta da zumar zan yi mata abinda take buk'ata ba. Na dai rarrasheta da tausasan kalamai na kuma jadadda mata ce wa ta mikawa Allah lamarin sannan kuma ta tsananta da addu'a Ubangiji zai kawo mata d'auki.
Da zata tafi na bata dubu talatin na ce kuma Ayuba ya kaita har gida don abincin ma dana sanya a kawo mata bata ci ba sai juye mata na yi a leda ta tafi dashi.

***
Yau wata biyu kenan da tafiyarsa wanda ya yi daidai da abinda ya faru da farko da na ce ba zan kara kiran shi ba amma yau tunda garin Allah ya waye na tashi da wata irin kewa da sha'awa. Na zauna ina tunanin abinda ya janyo mini shiga yanayin tunda na farko ni ina gujewa sha da cin duk abinda zai daga mini hankalina babu namiji a kusa da ni. Amma yau din nan na wayi gari da tsananin kewa kuma tasa da son jin wani abu daga gare shi.
Duka na bi layinkansa ina busy har yanzu bai cire ni ba, na duba shi a ta whasap na ga ya sauka tun kwanaki uku da suka wuce.
Sallama na yi masa cikakkiya da addu'ar Allah Ya sa ya amsa mini a duk lokacin da ya bud'e ya ga sa'kona.
Na kasance koyaushe cikin duba shi ta whasap din tsayin kwanaki tara da tura sa'kona bai hau ba sai yau. Na ga alamun ya duba sallamata amma kuma bai ce komai ba ya ma sauka.
Sai na sake tura masa wata sallamar again ina ta addu'a Allah Ya sa ya magantu.
Bai duba ba sai da gari ya waye tukkuna nan ma dai bai amsa mini ba.
A takaice dai sai da na yi masa sallama sama da biyar ya bud'e ya ga ni amma ko d'aya bai amsa ba.
Raina ya 'baci ainun. wannan mummunan dabi'arsa tasa ta gaba tana mugun b'ata mini rai. Kuma na fahimci yana da rike abu a zuciyarsa ba kasafai ake bashi ha'kuri ya ha'kura a lokaci daya ba.
Sai kawai na share shi gabad'aya ni ma na fita daga sabgarsa duk kuwa da cewa tunani da kewarsa na d'an damuna amma dai Ina yun'kurin dannewa domin tsira da sauran mutuncin da ya rage mini.
Chapter 18 · 0% Book details