← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 40

Sashe 39

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rana ta uku uwa da wuri muka fita saboda gida biyu nake so mu je, gidan Sahura da gidan Alhaji Muntari can muka fara zuwa saboda nasan idan gidan Sahura muka je da farko bai zama lallai ta bari mu fito da wuri ba.
Alhamdulillahi na ji dadin ganin yadda anti Maimuna ta samu nutsuwa ta kafa sana'a kala uku tana sayar da itace manyan d'auri sannan ga buhuhunan gawayi anan a jibge kusa da itacen sai manja da man kulli da take sayarwa galan-galan. Lokacin da muke je duka yaran suna makaranta tunda da safe ne. Na tambayeta Salima ta ce itama ta samu koyarwa a wata nursery dake bakin titi gaskiya ne a lokacin da Babansu yake raye ya yi kokarin sanya su a makaranta da wannan yarinyar ta tsira gashi har wasu suna amfana da iliminta kuma tana samun kwabo da dari.
Na tambayeta Jamila ta ce mini ta ji dai kwanaki an ce ta yi aure amma kuma tana zaune aka zo aka gaya mata wai an ganta a wani hausa film da ta yi bincike sai ta tabbatar da itace din auran ne ya mutu ta shiga wasan hausa.
Sai abin ya ba ni dariya da mamaki cikin zuciyata na ce to Allah Ya kyauta.

**
Yini zur muka yi a gidan Sahura ta dinga yi mana soye-soye har da su wainar fulawa. Ta soya mama dubalan cikin bokiti wai mu tafi dashi. Da daddare kuma ta hana mu tafiya sai da gama awara nan ma ta cika mana fulas wai idan muje gida sai mu ci a madadin abincin dare. Sahura kenan sarakan kirki da kyauta.

Washe gari ranar da za mu tafi kenan da wuri ya yi waya ya ce sha biyu ta yi mana a filin jirgi domin ya gama yi ma shiri, dama na gaya masa tare muke da Baba Tabawa ya ce babu damuwa don haka da wurwuri muka shirya na ce Ayuba ya kai ni gidan Baba Sule domin shi kadai ne ban je na gaishe ba, ita kanta Hadiza na so na kai mata ziyara amma lokaci bai ba da damar hakan ba, sai da na bawa Ummansu kudi na ce a yi mata siyayya a kai mata.
A gurguje muka gaisa da Baba Sule da iyalinsa na yi musu alheri daidai Gwaggwo sannan muka nufi gidan Hajja wanda daga can din sai kuma mu wuce airport.
Hajja bakinta kamar gonar audiga ganinmu a tare kanmu a had'e sannan ga 'yan jikokinta da take ta burin Allah ya nuna mata su.
Ita kyautarta dama ta turarece domin idan ta je saudiya su take sayowa da dayawa duk wanda ya ziyarceta ta bashi, ta had'o mana da yawa na jiki dana wuta tana ta yi mana addu'a da fatan alheri cikin tsananin farinciki mara misaltuwa.

Ganin da sauran lokaci da muka fito daga gidan Hajja na ce da Hauwa mu je gidan Hajiya Saratu don ni sai na ce zuwana gidanta d'aya tunda nake. Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba yanayinta ya nuna dai kamar ba ta son zuwa. Nan na fahimci cewa har yanzu akwai rashin jituwa a tsakaninsu tun daga lokacin da suka samu sa'bani akaina basu daidaita ba. Zaman amana muke yi a yanzu dole a tsakaninmu duk wanda ya hangi kuskure daga bangaran dan uwansa idan har da amana bai kyautu ace ya yi shiru ba mussaman idan aka yi duba da cewa ta dalilina suka samu matsala gashi zumunci ne mai karfi a tsakaninsu.
Tun kafin mu shiga mota na nuna mata fa yana da kyau ta gyara domin kuwa kaf Hajiya Saratu ba'asar yin ta ba ce, ta wuce matsayin Yaya a wurinta sai dai uwa, gashi kuma yayar mijinta ce dole ita za ta yi hakuri ta nemi hanyar daidato domin su gyara zumuncinsu tun kafin yaranta su fahimci halin da ake ciki.
Jikinta ya mutu sosai a lokacin da nake yi mata maganar ba kuma ta yi mini jayayya ba ta ce mu je din, dama ai ita bata d'auka da zafi ba, ita Hajiya Saratun ce ta ga kamar har yanzu bata huce ba domin koda ta haifi Khalil ba ta je mata barka ba. Na ce mata kada ta duba wannan kawai ta yi 'ko'karin gyara kuskuran da ta yi a baya.
Takuwa ji dad'i sosai da muka je gidan nata, kuma duk yadda Hauwa take d'ari-d'ari da ita sai ba ta nuna mata komai ba a fuska ba, ta sakar mata fuska kamar babu wani abu da ya ta'ba faruwa na saba'ni a tsakaninsu. Sosai na ji dad'in ganin yadda suka samu daidaito da fahimtar juna. Muka rabu cikin girma da mutunta juna ta yi mana alheri sosai tunda dama can a sanin da na yi mata itama hannunta a bud'e yake.

***
Bayan komawarmu da kwanaki uku na kira Hamusu a waya na ce masa ya fitar da kudi ya kuma nemi kwararrun ma'aikatan da za su gyara gidana na kuntau sannan ya sayi set din kayan d'aki da kujeru da gado labuleye masu kyau ya sanya a shirya gidan. Idan komai ya kammala kawai ya kaiwa Sahura mukkulin na mallaka mata shi gabad'aya tunda dama takardun suna hannunsa sai ya bata. Shi kansa ya taya ta murna sosai ya kuma bani tabbacin zai kammala komai a cikin sati d'aya.

To mun yanke shawara har da maigidan kan cewa tare za su sake komawa da Hauwa saboda yanayin garin koyaushe cikin ruwa ake yi duk da gidansa ya sha bam-bam da sauran gidajen da suke garin legos amma dai hankalinsa ya fi kwanciya da mu zauna anan abuja zuwa wattani shida lokacin yaran sun yi k'wari sosai..
Na ji dadin hakan sosai kuma na yaba da yadda suke nuna mini kulawa dashi da matarsa. Sai dai tunda muka yanke wannan shawarar nake cin 'kaniyata a hannunsa duk ranar girkina nakan ji jiki kwarai da gaske baya daga mini 'kafa, idan na yi magana sai ya ce abinda ma ya kusa tafiya. Haka na yi ta hakuri dai har ya kammala musu shiri suka tafi sannan na samu sa'ida.

**
Cike da mamaki Sahura ta kira ni a waya tana tambayata wai Hamusu ya kai mata mukulli da takardun gida in ji ni, na ce mata 'kwarai kuwa gidana na kuntau na mallaka mata halak malak. Sai ta rasa bakin magana ta yi shiru ta kasa cewa komai ba. Sai da na sake yin magana tukkuna na ji sautin muryarta cikin rawa kamar za ta yi kuka tana yi mini godiya na ce kin wuce haka a wurina Sahura dukiyata taki ce kuma ki shirya zuwa umara in sha Allahu farkon Azimi maigidan ya baku kyautar kujera ke da Anti Yagana da Baba Sule.
Sai ta fashe da kukan da take ta b'oyewa na kashe wayar ina dariya da mamakin kukan da take yi a ganina ai Sahura ta wuce duk wannan abin a wajena yadda nake jinta a raina kamar anti Yagana da muka fito ciki d'aya.

***

Ubangijina ya jarabce ni da abubuwa da yawa a lukutan baya wanda har nake ganin kamar ni kadai ce nake cikin masifa da ibtila'in rayuwa. Na yi kuka kamar ruwan idona zai tsiyaye yadda na ji dad'i na kuma godewa Allah shine ban ta'ba had'a Allah da waninsa ba, shi kadai na k'adaita na kai kukuna wurinsa domin kuwa nasan shine mai iko da kowa.
Allah na gode maka wannan kalmar ba zata ta'ba yankewa daga bakina ba har na koma ga mahallicina. Yadda Allah Ya kar'bi adduata a yau da Kamalu yake zaune a gabana cikin Kamala da suttura tare da tsantsar nutsuwa da wadataccen ilimin Islama a tattare da shi. Kamalu ya girma ya zama saurayi mai tattare da tsafta nutsuwa da ladabi. Ban iya daurewa ba rungumeshi na yi sosai a jikina ina kuka ina tuna mahaifinsu har shi ma ya kasa daurewa ya fara taya ni Baba Tabawa dake goye da Hassana a bayanta ta fito daga kicin da saurin domin sautin kukan namu har can ta tsaya tana ba ni baki wai na daina yin kuka Allah ya kamata na godewa domin duk abinda yake faruwa hukuncinsa ne. Da kyar na yi shiru shi ma ya rike hannuna gam ya kasa saki.
Cikin wannan halin Yusi da Adam suka shigo domin lokacin da aka kawo mini Kamalun ba sa nan. Wani tsalle Yusi ya yi ya rungumeshi suka fadi a wajan Adam ya dinga yi musu dariya. Shi ma Kamalun dariya yake yi wa Yusi ganin yadda duk kwalla ta cika kwarmin idonsa.
Ya dube ni yana tambayata wai wane irin abinci Yusi yake ci ya kumbura irin haka, ko bashi da lafiya ne. Na ce masa lafiyarsa lau hutu ya samu da jin dadi. Adam dai yana tsaye yana ta dariya da yake yaro ne mai sakakkiyar fuska kamar ta Mamansa. Kamalu ya gyara hannun rigarsa ya daga k'wajinsa na hannun dama duk a mur'de ya dubi Yusi yana cewa ka ga ni da nake cikin hatsi ina kuma aikin gona da motsa jikina dubi kwanjina malam haka ake son namiji ya kasance.
Adam ya ce abinda ake gaya masa kenan amma kullum sai ya ci nama ya zuba suga da madara da vombita da yawa ya tea Momi na bashi goyan baya.
Yana dariya yake cewa ku raka ni na je na gaishe da Momi ni ma." Ya mike tsaye ya shiga tsakiyarsu suka kama hanyar fita. Ni da Baba Tabawa muka bi su da kallo cike da wani irin farinciki a zukatanmu bakid'aya.
Chapter 39 · 0% Book details