← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To daga cewa zai je ya dawo a yini sai gashi sai da ya share kwanaki uku tukkuna kafin ya dawo sauran kwana dayan Hajiya Maryam da kwana biyuna ya yi su ne a tare da Hauwa.
Ban damu ba saboda nasan hakan da ya yi shine daidai yana da kyau itama ya zauna da ita sosai domin su tattauna abinda ya shafe su.
Da daddare ya dawo wajan goma da rabi har na kwanta ya shigo yanayin dana gan shi ya nuna mini cewa ya d'an jima da dawowa domin jallabiya ce a jikinsa. A can gidanta ya sauka zai cike mata cikon kwana dayanta.
Ya zauna gefena ni kuma na tashi zaune Ina laluben hulata data fadi na mayar kaina a nutse na gaishe shi ya amsa yana yi mini wani irin kallo. Hakan ba sabon abu ba ne a wajena domin ni kaina na kan rasa me yake kallo a jikina babu dai abinda bai sani ba, babu kuma sabon abu.
Saukar hannunsa na ji saman kirjina. Da sauri na ture ina dan hararsa. Ya sake matsowa jikina na matsa da baya
Sai ya tsaya yana kallona kafin ya gyad'a kansa kamar wadda ta yi masa mugun lefi.
Na daure tare a ce wa." Ina Hauwa da jariri suna nan lafiya?"
"Lafiyarsu." Ya fad'a yana duba wayarsa kafin ya miko mini wayar yana fad'in." Kin ga hoton jaririn."
Na kar'ba da sauri ina dubawa. Kamarsu daya wallahi, ina dariya na ce." Kamarku daya fa Baba, wannan yaron hotonka ne."
Da d'an murmushi a fuskarsa ya ce." Haka mutane suke ta fad'i Hajja tana gaisheki yaushe za ki je ne?"
Shiru na yi ban bashi amsa ba, ina ta duba hotonan yaron da yake cikin wayarsa.
Sai ya sake maimaita tambayarsa.
Ba tare da na dago kai ba na ce." Gaskiya ba zan rufe maka ba babu inda zan je."
Ya dube ni da wani irin yanayi kafin ya furta ." Akan wane dalili, mai aka yi miki?"
"Ba a yi mini komai ba." Na fad'a cikin mamakin yadda aka yi ya manta irin wulakancin da suka hadu suka yi mini har dashi. Hauwa na je garinsu cikin gidansu amma bola ta fi ni daraja suka mayar da ni abar nunawa da yi wa dariya ita da 'yar uwarta.

"Idan kuwa hakane babu wani dalilin da zai sanya ki ce ba za ki je ba Amina muddin zan bada umarni ki bi shi."
Hawaye ya ciko idona na ce ." Don Allah kada ka takura mini, ka kyaleni na ji da abinda ya dame ni, ba zan je fa domin kuwa ina da dalilina, idan kai ka manta ni ban manta ba."
Ya gyara zama yana kallona tare da cewa." Ni ban manta komai ba Amina, ki fito fili ki gaya mini abinda yake damunki ba ki zauna kina barin shi a cikin ranki ba, na lura kwana biyu nan tun kafin Haihuwar nan ba ki da walwala ina alkawarin da muka k'ulla dake?"

Hawayen dake cikin kwarmin idona ya d'igo. Na sanya hannu na goge tare da ce wa." Ai ni ban k'ulla alkawari da kai ba saboda na san ba iya cikawa za ka yi ba, kawai mu yi ta zama a haka cikin munafurtar juna."

Sai kawai ya yi sakare da baki yana kallona. Ni kuma ina ta kuka kamar wadda aka yi wa rasuwa. Gadon ya hayo sosai ya riko hannuna kafin ya ce." Munafurci na yi miki?"
Shiru na yi ban tanka masa ba. Ya ce." Ki tona mini asiri kawai ba wai ki dinga b'oyewa ba, ki gaya mini hak'kinki dana take tun zuwanmu nan, ashe duk takatsantsan din da nake akan kada wadda ta zarge ni a cikinku wato hakan bai yi miki ba, kina yi mini wani irin kallo."
Hanci na ja, na cire hannunsa da yake cikin nawa na ce." Idan zaman gaskiya da amana muke yi menene na 'boye mini matarka tana da juna biyu, ai na gane nufinka kada ka gaya mini, na ji haushi ko na yi mata hassada ko?"
Da wani irin yanayi ya furta." Wace matar tawa ce take da ciki?"
Kallonsa na yi, muka had'a ido, sai na d'auke kaina ban ce masa komai ba
Yasa hannu ya dago kaina ido cikin ido ya ce." Ki gaya mini wacece take da ciki."
Na ce."Amaryarka?"
"Ita ta gaya miki tana da juna biyu?"
Shiru na yi domin ba ni da amsar da zan bashi sai na ce masa alamar hakan na gani. Sai a lokacin ma na fara jin kunya da nauyin abinda nake yi wanda hakan zai sanya shi saurin gano cewa kawai zafin kishi ne yake damuna."
[9/30, 9:08 AM] Aunty B: 97
Ya jima yana kallona jin ban bashi amsar da ya tambayeni ba sai ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Ni ne dai mijinta Ina ganin kafin ta gayawa kowa tana da juna biyu ni za ta fara gayawa, amma tunda maganar ta fito daga bakinki tabbas nasan ba 'karya ba ne, zan je na tambayata na ji dalilin da ya sanya ta 'boye mini abina."
Ri'ke hannunsa na yi a sanyaye na ce." Kada ka tambayeta don Allah."
"Akan wane dalili?" Ya fad'a cikin wani irin yanayi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba. Sai ya sake maimaita tambayar da ya yi mini a karo na biyu.
Na daure cikin daburcewa na ce." Ni ma fa ba gaya mini ta yi ba kawai ina hasashene."
Ya zuba mini idonsa 'kuri yana kallo. Nauyi da kunya ya sanya na yi kasa da nawa idon. Sai ya yi murmushi.
mai sauti kafin ya ce." Momi ba ta da ciki Amina, domin kuwa da tana da shi nasan ba zata rufe mini ba zata gaya mini tunda tasan abinda nake nema ne ido rufe, daga yau ki daina yanke hukunci akan abinda ba ki da tabbas akai."
Na yi shiru ban tanka masa ba, domin kuwa ni kaina nasan ba ni da abin fad'a kuma ya fi ni gaskiya to idan ma cikin ne da ita menene abinda ya dame ni.
Kamar yasan tunanin da nake yi kenan ya matso kusa da ni sosai yana cewa." Ni zan fi so ma ki fara samun cikin Amina."
Kallonsa na yi. Sai ya daga mini kai da wani yanayi ya cigaba da cewa." Momi ta kwana biyu shakararta arba'in da uku fa, ina tsammanin idan ba tsananin rabo ba a wannan matakin za ta iya wuce haihuwa don dai tana da karamin jiki ne."
"Humm." Kawai na ce masa ina nazartarsa sanin halin maza akwai wahala, sun iya dadin baki da yaudara amma in ba haka ba yaushe zai zo ya zauna yana tsara mini magana. Shekara arba'in da uku shine ta wuce haihuwa muddin tana yin jinin al'ada bai d'auke ba za ta iya d'aukar ciki.
Fuskata ya dago da hannunsa muka kalli juna sai ya matso da bakinsa daf da nawa yana so ya sumbuta gabad'aya yanayinsa ya canza da sha'awa. Ban yarda na bashi damar da hakan ba, ya gama lalube mini jiki da hannusa ya tashi ya tafi da sanyi jiki domin ga dukkanin alamu yana cikin wani yanayi na buk'ata. Bai fito ya gaya mini ba amma ina zargin ba wata cikakkiyar gamsuwa yake samu daga wajenta ba, Ina gane hakan ne a duk lokacin da kwana ya dawo hannuna. Yakan nuna d'oki da murnarsa.

Washe gari da safe ina nad'e a gado ya shigo mini. Yanayin yadda ya shigo a hargitse ya sanya na gane akwai matsala. Na tashi zaune da sauri ina gaishe shi. Ya amsa a gajarce kafin ya ce." Ki shirya zuwa bauchi gobe in Allah Ya kaimu."
Kallonsa na yi naga babu nishadi a tare da shi. Sai na daidaita yanayin fuskata ni ma a nutse na furta." Na gaya maka fa ba na tsammanin zan je gaskiya saboda Ina gudun wulakanci, tunda a wancan karon ni na je, to mai zai hana wannan kuma ita ta je."
"Ba na son jayayya da taurin kai fa, kada ki 'bata mini rai, baki da wata hujja anan"
D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana fad'in." Bari na kira Baban Saude na sheda masa tunda ba za ki yi yadda nake so."
Cikin kuka na ce." Na fa na gaya maka irin wulakancin da ta yi mini a wancan lokacin Hajiya Saratu ce kawai ta goyi da bayana, ya za a yi ka tursasani zuwa wurin da za a tozarta ni."
Ya zauna kusa ni a hankali." Zuciyata ba dad'i Amina, ke ma kada ki 'bata mini rai, ki yi abinda na ce dake kin ji ko, kada ki duba kowa ki duba ni Amina."
Yadda yake magana da yanayi na damuwa shine abinda ya sanya mini kasala. Na goge ragowar hawayen da yake idona na ce." Ba na gudun zargi da zagin mutane Baba, amma ina kishin kaina, kuma wasu lukutan ba ni da juriya idan aka nemi a ci zarafina sai inda karfina ya kare ba na so na je garin mutane a yi rigima da ni."
"Na fahimceki tuntuni Amina, amma ina so ki sani wannan zai zama abin zargi da gutsiri tsoma, ba na so na ji ana zaginki, ko a fadi mummunar magana akanki, duk abinda za ki yi ki yi shi domin ni kin ji matata."
Tausayi ya ba ni sosai gabad'aya a hargitse yake ga dukkanin alamu akwai abinda yake dannewa bai fito ya fad'a ba. Ni ma kuma ba zan so na ji ba tunda tsakaninsa ne da iyalinsa.
Zan je dominsa kamar yadda ya nemi alfarma, amma ba na tunanin zan kwana don ban ga dalilin yin hakan ba.
A wannan matsayar muka tsaya na ce masa ba zan kwana ba kuma sai dai mu je tare ya ce ya amince da hakan.
To na d'auka shikkenan magana ta 'kare har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya sake zama a kusa da ni kawai ya zuba mini ido.
Ni ma sai na zuba masa nawa mu jima muna kallonsa juna kafin a kasalance ya furta." Ba ki gane ina da matsala ba Amina?"
Na ce." Ban gane ba, ai na d'auka matsalar muka warware yanzu."
Chapter 34 · 0% Book details