Sashe 40
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Abin mamaki da d'aure kai. Tun ina tsammanin dawowar Kamalu har na cire rai domin kuwa sha daya na dare har ta gota. Zuciyata ta shiga yi mini nazari ko kallo suka yi ne, ko kuma dai yaran sun d'auke masa hankali sam ban kawo cewa matar gidan ce ta hana shi dawowa ba sai da na kira ta a waya na tambayeta tukkuna kai tsaye ta ce mini zai kwana cikin 'yan uwansa ne. Mamaki mai yawa ya lullube ni amma ban iya cewa da ita komai ba muka yi sallama har tana cewa a shafa mata kan twins.
Da zullumin lamarin na kwana a cikin raina. Don haka gari yana wayewa ban yi kasa a gwiwa ba na kira maigidan a waya da muka gaisa na gaya masa fa makaranta sun sallamo Kamalu yanzu haka muna tare da shi anan abuja jiya Ayuba ya kawo mini shi. Sai ya ce ai Hamusu ya kira shi a waya ta gaya masa. Daga can makarantar ma sun sanar da shi. Na ce zai yi sati sati daya anan domin mun gama yanke magana da Hamusu zai zauna a can wurinsa domin dora shi akan harkokin da muke yi.
Bud'ar bakinsa sai ya ce bai amince ba dama ai tuntuni ya gaya mini idan yaron ya dawo zai had'ashi da d'an uwansa su tashi tare . Idan kuma ina ganin hukuncin da ya yanke bai yi mini ba sai na yanke nawa tunda duka 'ya'yana ne.
Na dinga kokarin nusar da shi hakkin da dangin ubansu suke da shi akan yaran, idan fa magana za a yi ta gaskiya yana da kyau a ce suma an basu damar yin abinda suke so da yaran. Ya fahimci dalilina amma sai ya mayar da abin rigima . Ganin haka ya sanya na kashe wayar raina a b'ace.
Ni wannan 'karfa-'karfa da ake yi mini akan yarana ya fara isata wallahi duk na gane take-takensa shi da matarsa wata'kila ya yi mata kyautar yaron tuntuni ban sani ba, tunda haka ya bata Yusi ba tare da neman izinina ba.
Wannan lamari ya janyo mana sa'insa sosai a tsakaninmu, wanda har sai da na gaza ha'kuri ina kuka na kira Hajja na gaya mata ta yi masa magana ta ba ni ha'kuri sosai ta ce za ta sanya a kira mata shi a waya.
Ranar kuwa da suka yi waya Baban Saude ya kira ni tare da rufe ni da fad'a irin wanda ban ta'ba tsammani ba. Shiru kawai na yi Ina sauraransa wato tunda na kira mahaifiyarsa to shi ma bari ya had'a ni da nawa iyayen. Baban Saude ya gama nasa fadan. Anti Yagana ma ta kira ni tana yin nata tana ce wa Ba ni da wato har yanzu kuma har yanzu na kasa gane irin k'aunar da mijina yake yi. Idan duk zai d'auki yaran da zan haifa ya bawa matarsa ai ta cancanta ne tunda kowa ya shaida ita din uwar marayu ce. Har da Allah Ya isa ta yi mini idan na kuma tashin maganar da kanta zataje ta yi wa Gwaggo bayani tana da tabbacin samun goyon baya da amincewa daga wurinta.
Kuka na ci na 'koshi na ha'kura na kyalesu kullum dai da safe suna shigowa mu gaisa. Shi ma kuma kamalun ya fi sakewa a can saboda yaran don ma shi Salim yana can saudiya yana 'dora karatunsa sai 'yan yaran Nusaiba Sahib da Yasmin da ake kawo su duk ranakun weakened.
Kiran Hamusun na yi a waya na yi mas bayani duk yadda al'amirin ya juye. Sai ya dinga dariya cike da nuna rashin damuwarsa yake ce mini wannan ai ba wani abu ba ne hakan ma da aka yi daidai ne da kuma hujja mai k'arfi.
Dole na ha'kura na zubawa sauratar Allah Ido, amma kuma ban ta'ba nunawa matar wani abu a fuska ba, dalili ta wuce na ya'keta akan komai ba, wanda ya riga ya ce yana son naka ai kai yake k'auna.
****
Haka zamanmu ya cigaba da gudana ni da Hauwa muna safara daga abuja zuwa legos yayin da ita kuma Hajiya Maryam take zaune a waje daya tana d'auke mana lalura da hidimar yaranmu. Bayan mai aikinta ta burni ta 'karo guda biyu masu d'an jini a jika domin kuwa wannan dawowar da Hauwa ta yi da ciki ta dawo har ya yi k'wari gabad'aya sabga da dawainiyar Khalil ta kuma gidanta. Kamalu kuwa har ta kai shi makaranta boko a cewarta bayan ya samu na addinin yana da kyau shi ma ya samu na bokon domin babu wanda ya san abinda zai zama anan gaba. Abinda Kuma ya k'ara zaburar da ita game da sha'anin yaron yadda yake koyar da su Adam karatun addini tare da sake nuna musu hukunce hukuncen tsarki da abinda ya shafi gyaran ibada.
Kafin mu tafi legos kuwa Kamalu ya fara limancin wani sabon massalaci da maigidan ya gina anan kusa da mu. Abin ya ba ni sha'awa sosai wai yau Kamaluna ne yake jan ragamar mutane da yawa zuwa gaishe da Ubangiji. Na yi kuka a zucci na yi na fili na kuma yi godiya ga Allah da ya nuna mini wannan rana da raina da lafiya, rayuwa kenan wataran asha zuma wataran asha mad'aci. Ubangiji Allah kasa mu d'ayantaka duk rintsi duk wahala ka barmu da imaninmu kada ka bari mu kauce daga bin tafarkin sunnar Annabi Muhammadu S.A.W.