← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 40

Sashe 36

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Kwanan Hauwa arba'in da shida da Haihuwa ya zo yana gaya mini za ta dawo amma ya nake gani domin ya bari ne ta gama wanka sai ya koma legos bayan mun yanke shawara. Na ce kawai ya bari ta zo nan 'din sai mu yanke shawara a tare domin ni har yanzu ban gama aminta da tsarin da ya yi ba, tabbas idan za mu raba wata shida shida ni da Hauwa to kuwa ban ga amfanin auransa da Hajiya Maryam ba domin kuwa idan ya ce zai biye mata akan abinda take so saboda wani dalili to kuwa babu shakka akwai gyara a cikin auransu. Ba zai yiwu a ce saboda mu kad'ai ne za mu d'aukar lalurarsa ba. Itama ai matarsa ce tsakani da Allah kenan ni na yarda zan d'auki wata shida idan ya so su kuma su raba wata uku uku a tsakaninsu.
[10/1, 9:08 AM] Aunty B: 98
Da kansa ya je bauchi domin ya d'auko Hauwa da yaronta. Tabbas idan a da can babu soyayyarta a zuciyarsa to yanzu kuwa ba za a rasa ba, ba don komai ba sai dalilin abinda ya ratsa tsakaninmu wato yaron da suke haifa a tare. Ban ji haushinsa ba dangane da duk rawar kan da yake nunawa akanta da yaronta domin kuwa na riga na tabbatar da cewa hakan sai ta faru to damuwa da bakincikin hakan zai iya haddasa mini ciwo ne don babu wani abu da zan iya hanawa, matarsa ce kuma uwar yaronsa. Babu dalili mai k'arfi zan ce masa abinda yake yi ba daidai ba ne. A wasu lukutan ma ni da kaina nake taya shi mu had'u gabad'aya mu yi ta kallon hoton yaron wanda kamaninsa ke k'ara fitowa sak kamar ya yi kaki ya tofar.
Ranar da ta dawo tare da ita ya kasance domin gidane mai yalwa wadataccen zaman mace hud'u kuma cikin sakewa babu takura balle wata ta ce an matseta.
Washe garin ranar da ta dawo da yamma muna tare falon Khalil yana hannuna muna hira da ita cikin kulawa kamar babu wata matsala da ta taba faruwa a tsakaninmu yadda na lura ma ba ta fiye so mu had'a ido ba ko magana take yi kanta a 'kasa ko tana kallon wani waje daban a haka muke yin hirar. Cikin zuciyata na godewa Allah da bai sa na cuceta a zamantakewarmu ba abinda suka yi a can baya shine yake damunta
Towol din goyansa ta d'auko mini na goya shi a bayana, cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke shi. Ina daga tsaye Ina dan jijjigashi tana gaya mini irin rigimar da ya dinga yi kafin su yi arba'in har yanzu bashin baccin da ta tara bai sake ta ba.
Maigidan ya shigo amaryarsa a bayansa ta nade jikinta da wata lafiyayyar lifaya irin ta manya. Duk shigar da za ta yi da gayu ba abin mamaki ba ne domin ko bata auran mai dukiya ita kanta hajiyar kanta ce ga uwar dukiyar da aka mutu aka bar mata da yaranta.
Fuskarta a sake ta zauna kan kujera tana dariya yayin da take kallon Hauwa tana cewa." Maijego ina fatan ba ki yi fushi da ni ba ko?"
Hauwa ta dan yi murmushi a takaice ta furta." Ban yi ba Hajiya ai maigidan ya ce ba ki ji dad'i ba ya jikin naki?"
Ta ce." Wallahi kam a lokacin na yi ta fama da zazzabi da mura har da ciwon kai, dalilin da ya sanya kenan ban samu zuwa ba."
Ta ce." Allah Ya sawwa'ke abinda ake ta fama dashi kenan."

Na kwanto yaron fuska a sake na mik'a mata shi ta kar'ba da walwala a fuskarta. Ko ba a fad'a ba ita din macace mai masifar son yara ko ba na bata ne wallahi irin rikon da take yi wa Yusi ko ni albarka duk abinda yaranta za su sanya a jikinsu za su ci babu bambanci wannan kad'ai ya kan sanya ni jin kunya da nauyin yin tutsu akan lamarinta. Kuma sam ba ta da fitina a haka dai tana zaune da kowa lafiya ban ta'ba ganin kishi a idonta ba.
Dad'in ganinmu mun sake muna hira gabad'ayanmu ya sanya shi kashingida kan kujera yana ta murmushi tunda suka shigo bai ce komai ba sai kallonmu yake yi yanayinsa ya nuna ya ji dadin ganin yadda muka fara fahimtar juna.
Sai bayan mun nutsu tukkuna ya gyara zamansa domin mu tattauna tare da samun matsaya akan yadda za mu shirya zama. Legos ne kowacce bata so a cikinmu amma kuma tilas ya kamamu duka saboda babu yadda za a yi ace mu bar shi a can shi kadai alhalin duka muna raye adalci shine a ce a raba.
Ni ya bawa damar magana tunda ni ce gaba dasu gidan cikin nutsuwa na ce." Ni na amince zan dau'ki wattani shida idan ya so ku kuma sai ku raba kowacce wata uku ina ganin hakan zai fi."
Hajiya Maryam tana murmushi cikin nutsuwa ta ce." Anya kuwa ni zan iya akwai abubuwa da yawa da suka sha kaina anan din wallahi ba na so na yi nesa yanzu ko kad'an shi Yallabai din ya sani da za ku yi mini alfarma sai na ce ku barni a nan babu damuwa ta b'angarena in sha Allahu."
Falon shiru ya yi bayan maganarta. Yana zaune bai ce komai ba alamu sun nuna tun a gidanta sun gama maganarsu ya d'aukota ya kawota ne don ya wanke kansa kada mu zarge shi.
Na dubi Hauwa da tun da muke maganar ba ta ce uffan ba na ce." To ke me ki ke ga ni Hauwa."
A takaice ta ce." Duk yadda kuka tsara ya yi mini sister."
Sai na dube shi a nutse na ce." To ka ji abinda kowa ya fad'a menene ra'ayinka?"
"Ra'ayina shine naku Amina, ku tsara yadda kuke ganin za ku zauna babu takura idan kun yi mata alfarmar da ta nema ni a wajena daidaine amma kada wadda ta kalubalanceni anan gaba. 'Yar uwarku ce ta kuma fito ta gaya muku dalilanta nasan zamanta anan din cikinku duk kun sani, idan kun goya mata baya to duk 'karuwar ta mu ce bakidaya."
Cike da takaicin maganganun da yake yi na ce." To wa ka ji ya ce bai amince ba, na d'auka ai zaman da muka yi gabad'aya don mu samu matsaya ne a junanmu, ni ta b'angarena babu damuwa tunda har na iya d'aukar rabi na basu rabin na ce su raba a tsakaninsu Yallabai duk wannan maganganun ba su taso ba."
Hauwa ta zumburi baki tana fad'in." To ni ma dai haka na ga ni."
Ita kam dariya ta yi tana fad'in." Na gode sosai, Allah Ya daidaita zamanmu ya kuma amfani zuriyarmu, na gode ni zan koma." Ta mike tsaye tana gyara yafen lifayar da take jikinta.
Na ce." A haba Hajajju ai babu buk'atar godiya duka taimakon kai ne wallahi kada ki damu an zama daya gabad'aya Allah Ya shige mana gaba."
Ta amsa da "Amin." Fuskarta yalwace da fara'a ta kama hanyar fita tana fad'in." Sai na sake zuwa mu gaisa da yarona yanzu bacci yake yi ba mu gaisa sosai ba." Hauwa ta ce." To shikkenan sai an jima.

Tana fita Hauwa ta dube shi kamar za ta fashe ta ce." Gaskiya zan gaya maka irin yadda kake nunawa matar kamar itace take auranka ya yi yawa. Ina lefi akan kawaici da karar da muka yi mata har sai ka fad'i wasu maganganu, ai sai ta d'auka hassada muke yi mata, kuma macace mai mutunci da sanin ya kamata gatanan babu wata matsala a tare da ita."

Ya ce." Mai na yi muku kuma, shikkenan daga na fad'i magana sai ku juya mini, halinta na fad'a tana da sau'kin kai gashi dai duk ta girmeku amma bata nuna muku gadarar hakan. Sannan duk da dukiyar da take da ita bata d'auki kanta a wata tsiya ba, ta sake daku sosai ta daukeku 'yan uwa daga fad'in haka sai ya zama lefi."

Na ce." Mu ai dama ba muce maka wata tsiya ba ne, kuma duk abinda take yi ai ba a sanyata ba gani ta yi zata iya, abinda dai zan gaya maka idan zama ya sake hadamu irin wannan muddin kasan zaka goyu da bayan bangare daya to kawai ka yi shiru da bakinka domin kuwa yin hakan zai janyo maka bacin rai za ka rikita gidanka da kanka."

Ya ce." Tunda kece Hajja sai ki ba ni umarni kin ji ko, ku abu kad'an mutum zai yi sai ku zargeshi Allah Ya sawwa'ke."
Yana rufe baki Adam da Yusi suka shigo janye da wata madaidaiciyar akwati gaban Hauwa suka ajiye Adam ya ce." Momi ce ta ce wai gashi ba Khalil ne."
Ta ce." Ku ce mata na gode sosai Allah Ya kara arziki."
Suka juya za su fita muka had'a ido da Yusi sai yasa dariya ya rike hannun Adam na d'auke kaina ina fad'in." Taka zata kawo ka wurina ne yaro."
Har za su fita sai ya kira su ya dubi Yusi yana fad'in." Mai ka yi mata take hararaka?"
A hankali ya ce." Babu komai Baba, ai muna shigowa kullum mu gaisa da ita ko ?" Ya fad'a yana kallon Adam da yake murmushi. Ya amsa da "E Muna zuwa." Ya ce musu ku tafi abinku rigima take nema."
Suka bud'e kofa suka fita kamar wasu 'yan tagwaye komai na jikinsu iri d'aya ne.

Kaya ne na waje irin wad'anda take sayarwa cike da akwati kayan nan kudinsu zai haura dubu dari uku domin duka babu k'ananu har da takalma da tarkace dai kala kala. Tare muka duba kayan yana zaune bai ce mana komai ba, har muka gama dubawa muka rufe akwatin bai tanka ba daga karshe ma sai ya tashi ya haye ya sama ya barmu a falon mu biyu.
Chapter 36 · 0% Book details