Sashe 12
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi wahala ce dai nake kar'ba nasan kuwa shima da akwai hujjarsa ta cewa ta yi zamanta acan din har sai cikin ya yi k'wari yadda ake so domin kuwa idan ya amince da zuwanta a yadda yake jin karfin nan da fitina kwanciya daya za a samu matsala idan cikin bai zube ba ta ci wahala. Haka na kasance cikin lissafi kwanaki tunda ya ce sai anyi sadakar arba'in tukkuna tunda kuwa na zo garin babu ranar da zata waye dare ya yi bai kwanta da ni ba. Saura kwanaki uku addu'ar arba'in din Alhaji Amadu Baba Sule ya kira ni a waya yana sheda mini rasuwar Alhaji Muntari jiya da daddare yake gaya mini har an yi jana'izarsa. Na shiga rud'ani mai tsananin gaske wanda har na kasa jurewa hawayen na nadamar duniya suka dinga zarya a kumatuna. Da magidan ya shigo ina kukan nake gaya masa rasuwar ya jimanta amma ba sosai ba ya yi masa addu'a a takaice ya cigaba da abinda yake gabansa. Na yini cikin alhini da damuwa duk yadda na so na danne damuwata akan rasuwar Alhaji Muntari na kasa domin daga zarar na tuna dashi da irin zaman da muke yi da wahalar da yasha ta jinya da yadda zuriarsa ke fuskantar kalubale sai na ji hawaye ya zubo mini mutuwar Yaya Aminu sai ta dawo mini sabuwa na dinga goge hawaye a fakaice tunda muna tare dashi yana aikinsa a Lopton ashe duk wani motsina yana hankalce shiru kawai ya yi mini har sai da na ki ci abinci tukkuna ya tanka mini ya fara fad'a yana cewa mutuwa kowa dole sai ya mutu na duba babban rashin da yayi akwanakin nan haka ya ha'kura ya ci abinci kuma ya cigaba da sabgogin rayuwarsa wai na shirya ci masa fuska ne shiyasa na sa shi a gaba ina kuka saboda rasuwar tsohon mijin dana aura a baya. Na yi shiru ban ce masa komai ba domin a lokacin ma da yake mini fad'an kukan nake yi don shi kadai zan yi na ji dad'i akan kaina nake tunanin faruwar hakan ace mace mijinta ya rasu ya barta da yara haka na yi ta fama da nawa yaran dad'inta ma ba a zaune nake ba ita anti Maimuna ba mai wayo ba ce kamar doluwa haka take don ba na tunanin ma ta yi karatun boko gashi yanzu an mutu an bar mata yara ita anti Jamila ta watsar da nata ta gudu saboda rashin tunani. Irin wannan wahalhalun rayuwar kawai nake tunawa sai na ji hawaye na zubo mini ita duniyar nan duk yadda ka kai ga yi mata dabara ta fi ka wayo kuma sai ka tafi ka barta babbar mafita kawai ka ri'ke addu'a kuma kada ka cutar da kowa. Ganin na yi masa shiru ban tanka masa ba sai ya kara fusata wai na tashi na fita daga d'akin muddin abinda zan yi masa kenan yana aiki Ina raba masa hankali. Ni ban ga abin damuwa ga mutumin da ya riga ya rasu ba kuma bayan mutuwar tasa ma abin tausayi ne da taimako a ganina idan ya ce mini akan me nake zubar da hawaye kamar ya so kansa ne tunda shi ma ai ya yi kukan mutuwar abokinsa. Dole a wannan ga'bar ya yi mini uzuri domin kuwa koda ban zauna zaman aure da Alhaji Muntari ba iya hallacin da ya yi mini ya kyautu ace mutuwarsa ta gigita ni. Na san bala'in kishinsa ne ya motsa ba wani abu wannan dalilin ne ma ya sanya na tashi na bashi waje kamar yadda ya buk'ata din tunda ni dai ba ni nake sarrafa kaina ba kuma hawayen dake zuba daga idonna ba ni da kwanji hana su fita. Washe gari da safe sukuku na tashi da damuwa da tunaninka fal a cikin raina na yi mamaki da bai biyo ni ya neme ni ya kwanta da ni ba wannan ce kadai ranar da ya raba mana shimfid'a tun bayan zuwana garin. Da kyar ya amshi gaisuwata yana ta jin haushin koda ya lura da rashin kuzarina sai ya fara 'kirkira mini aiki duk kuwa da yaransa masu yi masa hidima a gidan ya ce na yi masa towo na yi na gama ya ce na hada masa wasu takardu da ya zube a gado nan ma na gama ban ce masa komai ba domin na fara gajiya da abinda yake yi mini. Ya gama abinda yake yi ya zo ya zauna zai ci abinci ina bud'e miyar yaga taushece ya ce ai ba ita ya ce na yi masa ba kuka yake so. Na fara kuka ina fad'in." Ka kyale ni na huta dan girma Allah jiya ban rintsa ba saboda tunanin rayuwar nan ka ce na yi maka towon shinkafa na yi maka kuma yanzu ka ce mini miyar kuka babu kuka a gidan nan sai ku'bewa d'anya ko kwanaki ma da ita na yi amfani jiri ne yake damuna a yanzu kwanciya zan yi." Na zame na kwanta kasan wajan hawaye na cigaba da fita ta gefan ido. Ya d'auki flat din towon da na zuba masa ya tallafe da hannunsa na hagu kamar dai yadda ya saba idan zai ci abinci yana yi masa ladabi sosai kuma ba kasafai yake ci da cokali ba hankalinsa a kwance ya furta." Shin ko dai ke ma bin bayan mutumin nan za ki yi ne Amina." Shiru na yi masa ban ce komai ba. "Da na yi niyyar zuwa gaisuwa amma abinda ki ke yi ya ba ni haushi ba zan je ba." Yafad'a yana kallona. Nan ma ban ce masa ci kanka ba. Ya d'auki ruwa ya sha ya ajiye ya dube ni ina kwance sai ya gyada kansa da takaici ya furta." Ina ganin mutuwar mahaifi ko miji ya kamata a ce an shiga irin wannan matsananciyar damuwar Amina, ni kam wane irin dadi Alhaji Muntari ya ji jiyar dake wanda ya sanya kike ta yi masa kuka tun jiya ko kina da ajandar komawa gidansa ne mu dai wahalar da junanmu ni dake." Zaune na tashi ina goge hawayen idonta na dube shi sosai kafin na ce." Ba ni da ajandar komawa gidan Alhaji Muntari domin kuwa da da niyyar hakan a cikin raina wallahi tallahi da baka aure ni ba." Na numfasa Ina kallonsa shi kuma ya sake hade fuska tare da zubo mini ido. "Abu daya zuwa biyu ya sanya ni kokawa da rasuwar bawan Allan nan ko ka yarda ko kada ka yarda bai dame ni ba na farko shine hallacin da ya yi mini a lokacin da nake buk'atar agaji ya yi mini da kudi da karfinsa daidai gwargwado. Na biyu yadda gidansa ya tarwatse tun yana raye yaranshi suke walagigi ina ga kuma bayan rasu. Maganar nan da muke yi da kai a yanzu hankalina nakan babban yaronshi Turmuzi wanda tun asali nasan da cewa fitinanne ne an ce mini yanzu lamarinsa ya sake ta'barbarewa, ba zan manta ba mahaifinsa ya sha kokawa akan sha'aninsa. Wad'annan abubuwa biyu dana lissafa maka sune suka fi tsaye mini a rai domin kuwa na riga nasan sha'anin zumunci a yanzu ya zama abinda ya zama tunda can ma danginsu ba masu zumunci ba ne balle yanzu da baya raye kuma dama shi kadai ne mai dan rufin asiri a cikinsu. Ni uwa ce kuma na yi gwagwarmayar rayuwa da yarana nasan zafin da ake ji idan aka rasa wani 'bangare dalilin da ya sanya kenan nake tausayawa Anti Maimuna uwargidanshi domin ita amaryar ta gudu ta watsar da yaran yanzu gabad'aya suna hannunta kusan su tara ka gaya mini ya za ta yi dasu wane hali za ta shiga domin ciyar dasu da basu tarbiya. Shiru ya yi bayan na kammala maganata ya nisa sosai kafin ya dube ni a nutse ya furta." Yanzu ya kike so a yi ai na zama rumfa sha shirgi muddin wannan hawayen zai tsaya ki fad'i yadda ki ke so a yi miki zan yi in sha Allahu." A hankali na dube shi Ina nazartarsa akwai sasaauci a fuskarsa da kuma alamun tausayi da nadama kuma tunda ya ce zai yi to babu shakka kuwa zai yi din." "Abinda nake so kawai wannan yaron nasa Turmizi akai shi makarantarsu Kamalu bayan haka kuma ka shirya mana zuwa gaisuwa ni kuma zan zauna da anti Maimuna mu tattauna idan ya kama sai a bata jarin da zata kama sana'a ko?" Idonsa a kaina ya ce." Hakan ya yi miki?" Kaina na daga. Sai ya ce." Ai ni mai aiwatarsa ne tunda haka ki ka tsara shikkenan za mu je amma sai bayan an yi addu'ar arba'in din Alhaji Amadu idan na yi musu ta'aziyya daga nan sai na wuce Legos abinda na manta ban gaya miki ba kuwa hajiya Maryam ta bukaci akan na bar mata Yusi dalilin sha'kuwar da take tsakaninsa da yaranta akaran kaina ban so hakan ba sai dai ba yadda zan yi ne a yanzu tana buk'atar rarrashi da kuma biye mata akan dukkanin abinda take so domin dakushe mata kewar maginanta, nasan macace mai kokari sosai za ta kula da yaron kamar nata sannan ta yi alkawarin mayar dashi makarantar da Adam yake zuwa sai ya cigaba da dora karatunsa ina fatan babu matsala ta b'angaranki ko?" Haka kawai na ji ban ji dadin saurin yanke hukuncin da ya yi ba. To amma ba yadda zan yi koda kuwa raina bai so ba haka zan kar'bi hukuncin da ya yanke na tabbatar da matar tana da wata matsala mai muni ba zai bar mata yaron ba. Washe garin ranar da aka yi addu'ar cikar kwanakin arba'in na rasuwar abokinsa kamar dai yadda ya fad'a muka nufi kano bayan ya jima a gidan abokin nashi wanda na tabbatar da cewa ya shiga ne domin yi masu sallama da kuma kara tausarta yadda yake nuna kulawa da iyalin marigayin nake ji kamar kafin rasuwar tasa ya bar masa wasiyayya ne Gidan Hajja muka sauke ta ce itama sai a yi tafiyar da ita don haka muna idar da sallar la'asar muka nufi gidan Alhaji Muntarin dake kawo jirga inda na zauna yau kwanaki hud'u kenan da rasuwar an tashi daga zaman makokin sai