← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya sake furta." Mun yi al'kawari ko Amina."
Da 'kyar na ce." Ai mun yi tun a gaban Baban Saude."
"Wani nake so mu sake yi ni dake kawai, kin ji rabin rayuwata." Na dube shi da sauri jin abinda ya furta wai rabin rayuwarsa. Lallai ban yarda ba idan har ni din rabin rayuwarsa ce ai ba zai dinga yin nesa da ni ba duk tsaurin lefin da na yi masa.
Ganin na'ki biye masa ne ya sanya ya rabu da ni, a haka muka isa kasaitaccen hotel din da sai wane da wane, yana ta tsokanata ya d'auki gefan rigarsa yasa a jikina ni kuma bana gajiya da cirewa
Na ce da Sukajiru ya shigo mini da akwatinana dole akwai abinda zan buk'ata kafin na kwanta sai na yi burush da kuma kayan baccina a ciki. Idan ya so gobe idan za mu tafi din ya kuma kai su motar tunda na tabbatar da cewar tafiyar jirgi za mu yi sai dai har yanzu ban gama tabbatar da cewa ina zai kai ni ya ajiye ba legos din ne ko Abuja.
Tunda na yi wanka na fito yake ta bina da kallo don da kyar ma ya iya tashi ya je ya yi nasa wankan ya fito babu riga a jikinsa sai dogon wandon kayan da ya cire ya zauna kusa da ni a gefan gado lokacin muna magana da Sahura ta Whasap ina gaya mata sai ta kwantar da hankalinta auran bai mutu ba ga ni ma yanzu a tare da shi a d'akin hotel.
Ganin ya zauna kusa da ni ya sanya na kashe data tare da ajiye wayar a gefe, Ina kallonsa ya d'ebi nasa wayoyin duka ukun ya kashe su, ban ce masa komai ba a hankali dai nake nazarinsa yanayinsa kadai ya gama fahimtar da ni halin da yake ciki. Ai na d'auka har yanzu da dokin amarcin a tattare dashi to mutumin da yake da amarya irin haka, zan d'an jarraba shi na ga ni saboda nasan babu wani dalili da zai hana shi 'kin kwanciya da ni a irin yanayin da yake ciki.
Abinci muka ci a tare hankalinsa duk rabi yana kaina don ma ni ce karfin cin abinci. Da ga karshe sai ma ya ajiye cokalin hannunsa yana fad'in shi dan gargajiya ne bai saba da wannan ciye ciyen ba. Na ce sai ka sanya a kawo maka abinda ka ke so ko?"
Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma sai ya ce." Amma na ji dadin towon nan da aka sauke ni da shi a gidan Kawunki Baban Saude mutumin kirki ne Amina.
Murmushi na yi kad'an amma ban ce masa komai ba.
Shiru ya dan ratsa d'akin a kafin a hankali na ji ya kira sunana. Na daga kaina na dube shi a tsanake ya furta. Da gaske fa nake da na ce miki mu d'aura alkawari."
Ina tauna abincin da ya rage a bakina na ce." Ai ban fahimci alkawarin da ka ke nufi ba.
Zamansa ya gyara babu alamun wasa a fuskarsa ya ce." Tsakanina dake babu cuta babu cutarwa duk rintsi duk wahala kada ki zauna da ni da wata zuciya ki amince da cewa ni mai kaunarki ne ba kuma zan cutar dake ba, wallahi tallahi Amina da wata ce ta aikata mini abinda ki ka yi mini da har yanzu tana d'aure don ba zan yarda ba zan saketa kuma na yi shari'a da ita, babu ruwana da terere da surutun mutane sai Allah Ya ragewa aya za'kinta ke ce Amina wadda zuciyata take yi wa mahaukacin so. Ina sonki wannan kowanene zai shaida haka, kuma ina da burin gama rayuwata dake, ina da burin tara zuria dake koda duka za su kasance miskinai. Kamar yadda Kawunki ya fad'a na sani a zaman aure dole akwai kuskure dole kuma a samu sa'bani amma ina so ki sani sonki da kaunarki ne ya sanya mini wani ciwo mai wahalar magani a zuciyata. Wannan zafin kishin da zargin da nake nunawa a kanki ba yin kaina ba ne, Amina zuciyatace, na sha gaya miki ni mutum ne mai kishi da tsantsami a duk lokacin da na tuna cewa ba ni ne namiji na farko da na fara saninki a matsayin 'ya mace ba zuciyata tana yi mini wani irin ciwo wannan shine dalilin da ya sanya nake kasa sarrafa kaina, amma in bacin haka ai nasan wacece ke tun kafin aure ya ratsa tsakaninmu had'uwarmu ta farko na bijiro miki da wani lamari wanda hakan ba dabi'ata ba ce, na yi da manufar samun dace da macen aure mai tsoron Allah da gudun abin duniya. Kin fi kowa sanin ibtila'in rayuwar dana fuskanta dangane da matayen dana aura wanda da yawa mutane suka fara dora ayar tambaya a kaina. Auranki shi ya korar da wannan rud'anin ki ka yi hakuri ki karbe ni a haka da wasiwasin za ki mutu ko kuma za ki rayu. Wannan sai ya bawa sauran mata damar kawo mini hari da sunan soyayya tunda ai kin rayu tsayin shekara ba ki mutu ba. Amina in bacin Hauwa 'yar uwata ce, kuma Ina gudun 'bacin zumunci da babu dalilin da zai sanya ni na aureta tunda a can baya ai guduna ta yi saboda kada ta rasa rayuwarta kamar yadda 'yar uwarta Samira ta rasa tata rayuwar. Aurena da Hajiya Maryam kuwa wannan cikasa wasiyyar abokina na yi domin a cikin abinda yake rubuce cikin wasiyyar da ya rubuta da hannunsa kafin rasuwarsa har da neman alfarmar na auri matarsa domin cigaba da kula da ita da yaransa. Alhaji Amadu ya wuce komai a wurina domin duk yadda zan fad'a miki kirkinsa sai na rage mutum ne na k'warai mai kaunata da son cigabana. Ko ni ne na riga shi tafiya ba abin mamaki ba ne don na bashi wasiyyar ya auri iyalina saboda rufin asirinmu bakid'aya. Mu zauna lafiya don Allah, ki yi hakuri da ni, zan yi hakuri dake. A yanzu ke ce uwargina da ni da sauran iyalina muna hannunki. Muddin ki ka bud'e wata kofa ta samun sa'bani a gare mu to kin kashe kanki. Sai maganata dake ta karshe kada ki sake kaini 'kara wurin kowa domin kuwa ni ba yaro ba ne, ke ba ki ji kunyar kai mutum kamata 'kara ba Amina ke ce fa ki ka yi mini lefi kuma na yi shiru ban gayawa kowa ba amma saboda k'in gaskiya sai ki tafi ki kai ni 'kara na ji ciwon hakan sosai, kuma kin ci sa'a, ina sonki da ba zan je ba wallahi zan ta barinki da igiyoyin aurena a kanki duk ranar da ki ka gaji kya dawo."

Cikin kuka na ce." Ai kai kaso hakan, mai yasa ka'ki ha'kura, ai na gaya maka gaskiya ban 'boye maka ka dalilina ba, kuma da na fahimci na yi kuskure ba 'a yi wa Allah wayo na yi nadama na ro'ki gafararsa, kaima na ce ka yafe mini, sai ka k'ullece ni, ka dinga gaba da ni, ka rufe duk wata hanyar da kasan zan hadu da kai, ta ya ya ba zan nemawa kaina mafita ba, ai Allah ma muna yi masa lefi ya yafe mana, a lokacin ya kamata ka kar'bi tubana mu sasanta junamu ta inda babu wanda ya ji ya kuma ga ni, hakan bai yi maka ba sai kawai katin d'aurin aurenka na gani, ni ma shine dalilin da ya sanya kenan na nemi iyayena domin su kira ka su ji menene matsayin aurena."

"To mai yasa ba ki sanar da mahaifinki ba har sai kin yi tafiyayyiya kin je kin gayawa wani mutum, a ganina ai mahaifinki shi ya kamata ki sanarwa da halin da ki ke ciki Amina ba wai ki d'auko maganar ki kawota har nan garin maiduguri ba."

"Shi ma ai Baban Saude ba bare ba ne, kamar yadda ya yi maka bayani uba yake a wurina. Babanmu kuma yana da kawaici sosai bai zama lallai ya iya ce maka komai ba."
Murmushi ya yi kad'an kafin ya ce." Shi wannan din da ki ka kawo masa k'ara ta shi bashi da kawaici kenan."
Na dube shi da wani yanayi domin maganar tasa tana nema ta d'auki wata hanya. Sai kuma da sauri ya gyara maganar da ce wa." Yana da kirki Baban Saude amma d'an tattaunawarmu na fahimci yana da wasu 'yan matsaloli ammafa ba masu muni ba ne ainun. Na dai gaya miki kada ki sake kai ni 'kara koma wajen wanene."
Chapter 30 · 0% Book details