Sashe 1
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[9/14, 10:34 AM] Aunty B: 81 Ya ba ni tausayi sosai a wannan lokacin dalilin da ya sanya na kasance tare da shi har na riko hannunsa cikin taushin harshe na shiga kwantar masa da hankali, ita rayuwar duniya dama ai darashi ce walau maikudin ko talaka. Ba abin mamaki ba ne don wanda ka suturta ya karfin komai ta silarka ya nemi ganin karshenka hakan ba sabon abu ba ne shiyasa waliyyan bayin Allah irin na da ba su k'aunar wata d'aukaka ko mulki idan kuwa Allah ya ba su dukiyar suna kar'ba ne don ba yadda za su yi ammafa daga zarar sun lura mutuwa ta tunkaro su suke yin kasafin abinda suka tara a duniyar tun kafin su mutu ko su haka rami a wurin da babu idanun jama'a su binne kudi da gwalagwalansu ko sun mutu babu wata hatsaniya da za ta tashi bangaran 'ya'yansu da 'yan uwansu. Ganin yadda na dage ina yi masa nasiha kamar wata malamar islamiyya sai ya kara langwa'bewa ya dora kansa a saman kirjinta ina dan jin saukar numfashinsa kad'an kad'an. Har ga Allah a lokacin zuciyar Imani ce ta motsa mini domin ba k'aramin tausayi ya ba ni ba, da yawa sai a dinga ganin idan Allah ya azurta mutum ya gama samun jin dadin duniya da kwanciyar hankali kuma abin ba haka ba ne wani talakan ma ya fi mai kudin kwanciyar hankali tunda shi babu mai yi masa hassada babu mai farautarsa kuma zai kwanta ya ci baccinsa ya koshi bashi da wani lissafi na rayuwa. Daga rarrashi da nasiha sai lissafin malama ya kwancewa tun ina daurewa har dai jikina ya nuna na kwanta a gadon kansa a saman cinyata. Ganin haka ya sanya ya mik'a hannuna ya kashe fitilar dake gefan gado ya matso jikina sosai tare da rungumeni a kirjinsa a tare muka sauke ajiyar zuciya daga lokacin kuma fara gudanar da lamarin da zai sassauta mana damuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Da safe kamar sabon aure muka tashi mussaman ta b'angaranshi garau dashi kamar bai yi fama da wani ciwo ba. Na ji dadin hakan sosai kuma na yi farincikin yabawar da ya yi mini jiya cikin raina na yi ta addu'ar Allah ya kawar da sake samun sa'bani a tsakaninmu. Kicin na nufa na bar shi a d'akin bayan ya yi wanka ya kimtsa yana ta aiki da kwamfiyuta a cewarsa ya tara ayyuka rashin sukuni bai sanya shi dubawa. Na shigo d'akin bayan na gama shirya mana abin kari na same shi yana waya da Hajja karshen maganar dai na tsinta yana ce mata da yamma zai shigo. Na ji muryata tana fad'in." Hauwa ta kira ni wai kun barta a gida ita kadai don haka itama za ta biyo bayanku na ce dama tare ku ka zo da Amina." Ya ce." A a ita Amina ta je can garinsu maiduguri kamar yadda na yi miki bayani sai ta zo nan ganin gida, yanzu haka tana nan gidana na sharad'a na sanya an gyara mata zata zauna anan ita kuma Hauwa ta zauna mini a can, idan na zo da yamma zan yi miki bayani sosai." Ta ce." To in banda abinka ai mai lalurar ya kamata ka kawo kusa ba wai ka ajiyeta a can ba, kun taho kun barta ita kadai bayan ba lafiya ce da ita ba." Jiki a sanyaye na ajiye tiran hannuna na fita ina mamakin maganar da Hajja take yi, ko da yake ni ma ta zauna mini a lokacin da nake laulayi, to shi kuma idan aka ce za a yi masa haka kamar ba a yi masa adalci ba tunda karfin zamansa ya fi a can din. Na dawo na same shi yana cigaba da aikinsa ammafa fuskarsa ta dan canza kad'an. Hankalinsa na kan abinda yake yi ya ce." Kina jin mu da Hajja ko?' Na nuna ban fahimci komai ba. Ya furta." Wai itama Hauwa ta dawo nan tunda tana da juna biyu, Hajja tunda ta samu labarin cikin nan ta hana kanta sukuni, na ce mata a a dai ai ba zama zan yi ba wata'kila ma jibi zan koma." Na ce." Me yasa kace mata a a, ta dawo nan din don Allah idan tare take so mu zauna ai da d'akuna idan kuma gidanta daban take so ai kana da iko, itama Hajja tana da dalili ai lokacin da nake rainon baby Khadija ta zauna mini." Ya ce." Idan har Hauwa za ta dawo nan to ke za ki koma domin ba zai yiwu a ce ku nan ni ina can ba, idan sha'awa ta motsa mini matan banza kuke so na bi." Shiru na yi kawai ban ce komai ba, ba na tsammanin zan sake komawa legos koda kuwa Hajjan ce ta bada umarnin haka. Na ce.'' Yanayin yadda Hajja take magana ya nuna kamar a cikin bacin rai take shiyasa tun farko naso na je na gaisheta ta san da zuwana domin sai ta ga kamar ana 'boye mata wani abu ne. Na tare a sabon gida baka gaya mata ba sai 'boye-boye kake yi baka so a san kana garin nan ban gane dalilin yin hakan ba har yanzu." "Dalilina na yin haka suna da yawa Amina, amma yanzu tunda mun sasanta ba kya jin haushina zan gaya miki ba farko duk wanda ya ga jerin motocina na gidanki zai zargi wani abu rabuwar auranmu da nake ta b'oyewa duniya zata sheda hakan har ita hajjan ta ji labari gani can ina zawarcinki ke kuma kin koma zaman kanki irin na baya wanda mutane suka shede ki da haka. Za a yi ta yawo damu a duniya kowa na tofa albarkacinsa bakinsa. Na gayawa Hajja cewa kin je can maiduguri biki ni kuma na ce mata zan zo nan domin duba Gwaggo wadda ta haifi mahaifin Yusi, ko da na sauka garin nan hakan na sake gaya mata. Amma wannan ba abin da za a tsaya ana ta magana ba ne, zan yi magana da Inna Uwani a samu wata dattijiwar sai a tura mana ita can su zauna tare har Allah ya sauketa lafiya." Na ce." Idan dai hakan zai janyo matsala don Allah Hauwa ta dawo nan itama ba na son abinda zai sa Hajja ta ga rashin kyautawata" Babu damuwa ya ce." Idan kin aminta hauwa ta dawo ai abu ne mai sau'ki sai ta dawo din ke kuma sai mu koma tare " Girgiza kai na yi na ce "A a ni kam ai na dawo kenan in sha Allahu." Ya ce." To sai ki ja bakinki ki yi shiru tunda ke kin yi nasara amma ba zai yiwu a ce duk ku tattara anan waje daya ba. Ya fita sallar azhar bai dawo ba ya bar wayoyinsa a d'akina ana ta kira na shiga d'akin a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa na d'auki wayar na duba sunan Hadiza ne yake yawo cike da mamaki nake bin sunan da kallo. To kai tsaye dai ba zan yanke hukunci cewa Hadizar gidanmu ba ce tunda mutam ne na mutane akwai ma'aikata mata da suke yi masa aiki mabambamta har da k'warori. Ba yadda za a yi na daga wayar tunda akwai tsaro (security) sai na ajiye har ta katse wani kiran ya sake shigowa a k'alla akan idona sai da aka kira sau kusan shida kafin a hakura. Ya shigo a gurguje yana fad'in.'' Ban san me mutane suka zama ba a wannan duniyar ba ni da lokacin da zan 'bata akan yin jawabi dangane da Sammani abinda suka samu na shaci fad'i ya ishesu babu wata gidan jaridar da zan tsaya bata lokacina a kansa. Na ce." Wani abun ne ya faru kuma?" Ya zauna gaban abincin dana shirya masa yana cewa." Sun ankara da ni ne duk da na rufe fuskata da takunkumi yanzu bakin gate din gidan nan mutane ne cike manema labarai da mabukata." Gabana na dan bugawa na ce." Akan me suke neman labari kuma? "Dangane da abinda ya faru mana tsakanina da Alhaji Sammani suke neman jin ta bakina." Na ce." Ka ja bakinka kawai ka yi shiru don Allah kada ka ce komai bayanin da ka yi da farko ya wadatar wata'kila wasu sun samu labarin ko ya yi yun'kurin kashe ka ta hanyar sanyawa a kwance maka k'ososhin mota." Ya ce." Ba na tsammanin haka, lamarin dai da suka samu shine na salwantar mini da gidan gonata dake tiga da kuma sabon kamfanin da na fara ginawa a mariri wanda shi kadai ya san da ajandar hakan to akan hakan dai suke so su ji abinda zan ce." Na ce." Ai ka ce ka yafe masa ba shikkenan ba. Mutane ne ba su san zaman lafiya shi kansa nasan yanzu yana can cikin jin kunya da damuwa ga kuma fargabar irin kallon da mutane za su dinga yi masa. Ya ce." Ai idan har suna ganina ba za su daina bibiyata ba Amina, ba ki san dan jarida da na ci ba ko." Shiru na yi ina kallonsa ya janyo wayarsa dake saman gado yana fad'in." Zuba mini abinci ina so na fita zuwa gidan hajja ina fargaba wallahi." Na fara had'a masa abincin a tsanake na ce.' An kira ka a waya ka ga ni ko?" Ya na duba wayar ya ce." Hadiza ce yayarki." Na dube shi cikin nutsuwa." Hadiza kuma?" Ya d'aga kansa a hankali ya sanya wayar a kunnansa kiranta ya yi. Kaina ya kulle da mamakin lamarin dama tana kiransa ashe shiru na yi kawai domin na ji wannan karon kuma dame take tafe. Gaisuwa suka yi ita dashi cikin girmawa har tana tambayata da Yusi shi ma ya bata amsa da kulawa tunda na fahimci duk abinda ya shafe ni yana bashi girma. Magana take yi masa cikin rauni har da rawar murya amma sakamakon yadda muryarta ta yi kasa ban ji komai ba. Na ji yana fad'in." Allah Ya rufa asiri in sha Allahu za a duba yiwuwar yin hakan, Allah Ya shirye shi da sauran masu hali irin nasa. Ya kashe wayar yana dubana kafin ya ce." Kuna da wani d'an uwa wanda Allah Ya jarabta da rashin ji ?" Da