← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 40

Sashe 17

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Ya gyad'a kansa yana kallona ido cikin ido sai na kasa dubansa na yi k'asa da kaina gabana na bugawa da k'arfi. Ya sanya hannunsa ya dago fuskata yana cewa." Ki rantse da girman Allan da ya hallice ki a wannan duniyar ba ki yi yun'kurin zubar da cikin nan ba Amina."
Shiru na yi ban ce komai ba zuwa wannan lokaci kuwa kafafuna sun fara rawa saboda fargaba da zullumi domin kuwa ban hangi kwanciyar hankali da yarda da kaddara daga gare shi ba.
Ya tashi ya je ya dauro alwala duk Ina zaune Ina kallonsa ya bude drowa ya d'auko al'kur'ani izu sittin ya dawo ya zauna a kusa da ni yana fad'in." Zan iya rantse miki da Allah cewa baki da gaskiya Amina, kuma bayanin da likita ya yi shine gaskiya."
Na ce." Me ya yi zafi da har sai an yi rantsuwa da al'kur'ani, kafi kowa sanin hakan babban hadari ne, kuma al'kur'ani ba abun wasa ba ne."
"Ban d'auko al'kur'ani da zummar wasa ba Amina, wallahi Allah daya ne kin yi yun'kurin zubar mini da ciki, ina so ki tashi ki je ki d'auro alwala ki yi yadda na yi ki d'auki al'kur'ani ki dora a saman kanki ki rantse da Allah muddin ki ka yi haka wallahi zan aminta dake d'ari bisa d'ari."
"Zan yi dai alwala amma ba ni da hurumin rungumar al'kur'ani domin ba ni da tsarki, ko ma ina dashi ni ba zan yi wannan gangancin ba gaskiya."
Ya jima yana kallona kafin ya furta." To na ji ki ba ni amsa me yasa ki ka rufe mini samuwar cikin ba ki gaya mini ba."
Shiru na yi ina d'an duban yatsun hannuna kafin na ce." Babu wani dalili mai k'arfi na bari ne kawai idan ka zo garin sai ka gani da idonka, kuma anti Yagana ta ce mini hakan kuskure ne don Allah ka yi ha'kuri."

"Ba ha'kuri na ce ki ba ni ba Amina gaskiya na ce ki gaya mini, tun muna mu biyu dake a d'akin nan idan kin yi mini gardama zan sanar da 'yar uwarki sannan na gayawa Mahaifiyata abinda ki ka yi mini."
Na zuba masa ido da yanayi na damuwa na ce." Na gaya maka gaskiya baka yarda ba to karya kake so na yi maka wai me zai sanya ni na zubar da cikin ne ai ba shege ba ne."
Sai ya tashi tsaye a fusace! "Ai kin shegantashi tunda ki ka zubar mini da shi, Allah Ya isa ban yafe miki ba Amina."
Ya fad'a jikinsa na karkwarwa idonsa ya yi jajawur.
Tsaye na mike ni ma da yanayi na ko'karin kare kaina na ce." Menene abin Allah Ya isa, shikkenan 'kaddara ba za ta faru ba sai a jingina mini ita, ai musulma ce ni nasan abinda addini ya koyar ko cikin da ba a same shi ta hanyar mai kyau ba haramun ne zubar dashi balle wanda aka sameshi ta hanyar halak, ban ga dalilin da zai sanya ku dinga kokarin dora mini lefi b......Ban 'karasa ba ya kawo mini hari na 'barin makauniya a kuncina sai na yi kasa da mugun sauri lamarin da bai taba ratsa tsakaninmu ba ko da wasa bai tab'a yun'kurin kai hannunsa jikina da zummar duka ba.
Jikinsa na rawa yake cewa." An jingina miki lefin, ai ba ki da imani kuma baki da kyawun zuciya Amina na jima da sanin za ki iya aikata abinda ya fi haka akaina tunda baki zaune da ni da zuciya daya. Ki bar ganin kina cikin hali na lalura hakan ba zai hana ni na huce takaicina ba. Abinda nake nema ruwa da iska rani da damuna na samu har guda biyu kin zubar mini Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!"
Ya kai 'karshen maganar da kiran sunan Allah kafin rigijib ya zube a kan gadon ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa gabad'aya yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! da baban sauti.
[9/23, 9:23 AM] Aunty B: 90
Ganin halin da ya shiga ya sanya mini muguwar fargaba domin kuwa tunda nake dashi ban ta'ba ganinshi a cikin yanayi na rud'u da tashin hankali ba. Tabbas lokacin rasuwar baby Nana ya shiga damuwa sosai amma sai nake ganin wannan lamarin ya fi d'imauta shi fiye da wancan din. Jikina babu kuzari ko na gamin gafara na kama hanya domin fita daga d'akin saboda ban san wace irin fitina zamana zai haifar ba. Fargabata da tsananin damuwata kada ya fitar da maganar domin kuwa ya fi ni gaskiya da hujja mai karfi dalili ni tun farko na d'auri kaina da ban gaya masa ina da ciki ba. Idan kuwa zan kafa hujja da cewar ai na zubar da shine domin gudun haihuwar mai sikila ba kowa ne zai fahimce ni ba, da yawa ma wasu za su ga ai don ina da yaran ne ya sanya ni yun'kurin zubar da ciki ba tare da damuwata ba. Ammafa muddin an zauna an dubi lamarin ta fuskar adalci za a fahimci abinda nake nufi. Wannan kadai itace hujjata ko da kuwa maganar ta fasu na tabbatar da cewa ya fi ni hujja mai karfi domin masu k'adaita Allah da tauhidi ai za su ga gangancina domin kuwa tun fil'azal ai haka iyaye da kakanni suke yin auransu su haihu lafiya ba tare da wata rikitarwa irin ta yahudu da nasara ba.
Kai tsaye d'akina na wuce na kwanta don ba zan iya zaman falon ba dalili kwata-kwata bana cikin hayyacina ga jikina babu k'wari don har yanzu jirin bai gama sakina ba.
Anti Yagana ta shigo d'akin ta same ni a kudindine a cikin bargo lokacin ma kuka nake yi amma mara sauti sai na yi saurin rintse idona ina goge hawaye a fakaice bata fahimci komai ba tunda daga bakin kofa ta tsaya tana tambayata ko jikin ne na ce mata a a Ina hutawa ne sai ta juya ta zata fita tana fad'in bari ta kawo mini abinci na ci sai nasha magunguña.
Da kyar na iya cin loma biyar shi ma sai da ta matsanta mini tukkuna na ci sai da ta tabbatar da nasha maganin kan ka'ida tukkuna ta fita daga d'akin.
Sai bayan ishi'i su Hajja suka tafi bayan sun shigo sun yi mini sallama tare da fad'a mini cewa za su sake dawowa domin sake duba ni cikin satin da za mu shiga.
Ina daga kwance muka yi sallama cikin kulawa yadda suka nuna damuwarsu a kaina hakan ya faranta mini sosai sai dai can kasan zuciyata ina jin fargaba kad'an idan har suka samu labarin abinda na yi shin da wace fuska za su dube ni.
Tunda na fito daga dakinsa ba mu sake haduwa ba sai da garin Allah ya waye anti Yagana ta matsa mini lallai sai na rage kwanciya na fito falo na zauna kan kujera hakan zai k'arfafa mini gwiwa domin idan ina yawan kwanciya kasala da ciwon jiki ba za su barni ba.
Saboda haka ina yin wanka na shirya na fito falon na same su suna kallo har da Baba Tabawa na nemi kujera na zauna hankali na saman ina tunanin ko ya sauko ko wane hali yake ciki.
Yusura ta kawo mini abinda suka yi na karin kummalo na kasa cin komai saboda bakina har yanzu babu d'aki. Baba Tabawa ta d'umama mini ragowar towon jiya bashi dai da yawa tunda Hajja ta tafi da wani amma ya isheni kuma ni kaina na yi mamakin yadda na ci sosai a lokacin na ji karfin jikina ya k'aru... Cikin wani yanayi na tambayi anti Yagana maigidan ya sauko tunda tun safe suna falon ta ce mini ya sauko har sun gaisa ya fita amma bai jima ba ya sake hawa saman bai kara saukowa ba kuma.
A gogon da yake falon na duba sha daya da rabi domin kada ta fahimci akwai 'baraka ya sanya na tashi ina fad'in bari na hau mu gaisa. Kai tsaye na nufi benen da zullumi mai yawa a kirjina.
Kofar d'akin kawai na tura ta bude bai murza mukkuli ba, Yana zaune a gefan gado ya shirya sosai cikin milk din shadda tazarce da aiki mai kyau a gaban rigar hularsa tana ajiye a gefe amma as'usul gilashinsa na ka'ida yana idonsa. Magana yake yi a waya a lokacin da na shiga d'akin na samu wuri gefansa na zauna amma gabad'aya na gagara kallonsa saboda tsananin yadda nake cikin damuwa.
Jin yana ambaton sunan Maryam ya sanya ni shiga tunani daga bisani Kuma na gane da Hajiya Maryam suke yin magana matar abokinsa da ya rasu kwanaki. Sun jima suna tattauna abinda ya danganci mamacin yanayin maganganunsu ya tabbatar mini da cewa suna tattauna yadda za a raba abinda ya bari tunda mahaifiyarsa ta na raye kuma yana da 'yan uwa. Dole Mamansa ta gaje shi koda kuwa 'yan uwansa ba su gaje shi ba dalili akwai maza biyu a cikin yaranshi.
Bayan sun yi sallama ya dube ni babu yabo babu fallasa amma bai ce komai ba sai ya cigaba da latsa wayarsa yasa a kunnansa ina dai zaune Ina jin shi Hauwa ya kira a wayar cikin kulawa na ji suna magana don ba na jin abinda take cewa tunda kamar ya yi kasa da murya ne don shi ma idan ta fad'i magana sai ya sake tambayarta abinda ta ce saboda maganarta can kasa take fita. Sai na juyar da kaina gefe ganin kamar ba ya so na ji maganar da suke yi na ji yana gaya mata daga nan din kai tsaye bauchin zai taho zuwa yamma ta tsammaci zuwansa tunda tafiyar mota zai yi.
Jikina ya d'an yi sanyi Jin yadda yake lalla'bata da rarrashi har da kalamai irin na tausayawa da sadaukarwa. Sai na tsargu da jin abinda yake yi wanda na tabbatar da cewa wanzuwata a wurin ya kawo hakan. Na ji haushi sosai amma sai na danne domin kuwa a yanzu fushi ba nawa ba ne dalilin abinda na tabbatar da cewa ni ce mafi rinyen lefi dole a wannan ga'bar ko ban fito na gaya masa na aikata ba na nemi hanyar shiri da kuma ko'karin kwantar da matsalar don gudun fasuwar maganar.
Ya ajiye wayar a kusa dashi bayan sun kammala ya d'auki agogonshi dake saman drowar yana daurawa bai ce mini komai ba. Na daure na ce." Ina kwana Baba?"
Hankalinsa na kan abinda yake yi ya amsa da "lafiya ya gajiya." Sai na yi shiru ina dan satar kallonshi a fakaice. Sukairaju ya dan buga kofar kafin ya bashi umarnin shigowa ya turo a hankali cikin ladabi ya tsaya daga can nesa yana fad'in." Sir ka kammala ne?"
Ya mike tsaye da hularsa a hannunsa yana gyarawa ya ce." E, na kammala zo ka d'auki wad'annan." Ya fad'a yana nuna masa Loptop dinsa dake ajiye da 'yar jakarshi."
Da sauri ya yi abinda aka sanya shi ya bude kofar ya fita daga d'akin. Yana ko'karin sanya hular a saman kan sa ya ce." Ni zan tafi Amina, Amma kafin nan zan je Bauchi wurin Hauwa domin dubata ina fatan ba ki da matsala ko?''
Na mike tsaye da rashin karsashi na ce." Ba ni da matsala Baba amma ina so mu yi magana dangane da abin nan da ya furu na ga kamar ba ka yarda da kaddara ba don Allah kada ka tafi da 'kullacina a cikin ranka."
Ya dube ni sosai wanda tun shigowata d'akin bai yi mini irinsa ba.
"Kin aikata hasashen Dr Iliyasu ko ba ki aikata ba, wannan amsar kawai nake so na ji daga gare ki."
Shiru na yi ina kallonsa shi ma yana kallona ido cikin ido. Mun d'an jima a haka kafin daga bisani na janye nawa idon daga cikin nasa zuciyata na dan harbawa ko alama ban hangi sasaauci a cikin idanuwansa ba.
"Shirunki da yanayin yadda alamun rashin gaskiya suka bayyana a tattare dake ya bayyana mini ce wa." Dr Iliyas ba karya ya yi miki ba saboda haka ni kawai sai dai na ce na barki da Allah."
Daga haka sai ya kama hanyar fita daga d'akin. Da saurin gaske na cimmasa idona cike da hawaye masu radad'i na furta." Maganar bari da Allah ba adalci ba ne, ka yi duk hukuncin da kake ganin za ka yi mini tunda ka'ki kar'bar kaddara, amma kwata kwata ka daina had'ani da Allah
Chapter 17 · 0% Book details