Sashe 16
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mai kyau Ayuba ya kawo. Na daure na yi mata magana a hankali ta dube ni amma ba ta ce mini komai ba. Na ce." Ba ki ci abinci ba anti Yagana." Kanta ta girgiza a hankali ta furta." Ba na jin yunwa Amina har yanzu ban daidaita ba wallahi jiyan nan na shiga rud'ani ba kad'an ba sai nake ganin kamar za ki tafi ki barni ne." Hawaye ya sake silalo mata. Murmushi na yi cikin raina na ce dama abinda take yi wa kuka kenan. Anti Yagana kenan ai mutuwa kam ta zame mana dole ko na rigata ko ta riga ni babu wanda zai zauna a cikinmu.. Na daure na ce." Ni ma ban ta'ba jin ciwo mai azaba irin na jiya ba wallahi ni kadai nasan halin da nake shiga anti Yagana Allah dai ya takaita mini wahala." Ya gyada kanta da kulawa ta furta." Gashi ma ashe 'yan biyu ne amma me yasa ba ki taba gaya mini kina da ciki ba Amina, ai ko baki sanar da kowa ba kya gayawa wanda ya yi miki jiya da muka yi waya yana ta fad'a shi bai sani ba." A dan sanyaye na ce." Anti Yagana shurun da na yi masa shi ya fi alheri domin kuwa nasan halinsa idan ya samu labari zai hana kansa sukuni ne, ni a tawa fahimtar kawai na bari ne duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa. Ta ce." Wannan ba hujja ba ce ko dan gaba kada ki kara haka ai abin alherine kuma yana da hakki ki gaya masa. Baki san hakan zai yi masa ciwo ba kenan ga yanayin yadda yake magana a wayar ya tabbatar mini da cewa ya ji haushin abinda ki ka yi." Na ce." Zan kiyaye in sha Allahu rabbi yanzu dai ki ci abinci ba na so na dinga ganin ki cikin damuwa da alhini duk abinda Allah Ya yi daidai ne." Ta girgiza kanta da damuwar dai ta furta." Tabbas yadda Ubangiji ya yi shine daidai amma na so a ce kin haife tagwayen nan Amina, amma Ubangiji Allah Ya ba ki wani." Sunkuyar da kaina kasa na yi ban ce komai ba yanzu idan ba dan'uwanka na jini ba wanene zai gwada maka wannan soyayya. Tare muka ci abincin amma ni kadan na iya ci nasha maltina tana ci muna taba hirar lamarin Hadiza. Hamusu ya kira ni a waya ya ce gashi nan asibitin ya shigo dubani domin yanzu daya can gidana yake Yusura ta gaya masa ba ni da lafiya. Anti Yagana da kanta ta fita ta yi masa jagora muka gaisa sosai dalili tunda na dawo daga abuja ba mu had'u ba sai a waya idan na kira shi ko ya kira ni dangane da harkokinmu ya ce zai tafi amma da yamma za su so tare da Gwaggo anti Yagana ta ce masa sai dai su je can gidana domin kuwa ta ji likitan yana fad'in ya rubuta takardar sallama yana jiran zuwan Yallabai din ne. Ya ce idan ba su zo da yamma ba to gobe da safe za su je can gidan muka yi sallama ya kama hanya ya tafi shago. To sai bayan sallar azhar tukkuna suka zo asibitin tare da Hajja da Hajiya Saratu. Haka kawai sai na tsinci kaina da kasa had'a ido dasu gabad'aya domin hausawa suka ce mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi. Gabad'aya na kasa nutsuwa domin sai nake ganin kamar za a gane na yi wani yun'kuri a baya. Hajja sai sannu take yi mini tana fad'in an auna arziki ai tunda cikin ya fita ba tare da wata matsalar ba. Hajiya Saratu ma ta jajanta mini sosai tana cewa idan da rabo a kusa sai a kara samun wani. Shi ogan yana tsaye a gefan kaina tunda muka gaisa ya yi mini sannu bai sake magana yanayinsa dai ya nuna jimami da damuwar abinda ya faru. Jikina ya kara yin sanyi sai na kasa daga kaina na dube shi a lokacin da likitan ya shigo d'akin yana tambaya ko da matsala na girgiza kaina alamun babu komai. Yallabai din ya dora hannunsa a saman goshina sai likitan ya dube shi yana cewa." Da zu da muka yi magana da ita ta ce mini jiri ne kadai yake damunta amma in sha Allahu shi ma zai gusa nan da kwanaki uku tunda an dubata sosai babu wata matsala sai ta rashin kwarin jiki, bayan haka kuma ga magunguñan nan masu kyau na hada mata." Hannu ya ba shi suka yi musabaha da juna yana yi masa godiya yayin da likitan yake jadadda masa cewa babu godiya domin kuwa aikinsa. Tare suka fita sai hakan ya haifar mini da damuwa don sai nake ganin kamar akwai wani bayani da likitan zai yi masa wanda yake b'oyewa. Hira suke yi a d'akin tsakanin Hajja da Anti Yagana dama akwai shak'uwa a tsakaninsu tun zuwan da anti Yagana ta yi wajena a lokacin da ina Legos. Ni kuma jikina duk ya yi la'asar hankalina na can tunanin abinda zai faru domin kuwa nasan ko likita bai gaya masa wata magana ba na tabbatar da cewa sai ya tuhume ni dalilin da ya sanya na yi shiru ban gaya masa samuwar cikin ba tsayin wattani uku da satika. La'asar a gidana ta yi mana tare gabad'aya muka dunguma har dasu Hajja a ka yi sa'a kuwa Baba Tabawa tana ta hidimar abinci koda ta fito suka gaisa cikin barkwanci take cewa da maigidan towo take yi saboda ta ji labarin zai zo kuma ta sanya an samo mata daddawa da kuka masu kyau tunda ta fahimci ya fi k'aunar miyar kuka fiye da sauran abin ka'di. Ya dinga godiya kuwa cikin kulawa da sakin fuska wannan dabi'ar tasa ta rashin 'kyama tana kara masa martaba. Hajja fadi take yi kin kyauta kuwa Tabawa sai ki tu'ka towon da yawa ni ma na tafi dashi na d'umama da safe. Tashi ya yi ya nufi d'akinsa dake saman bene wanda ya jima a rufe tunda ni duk dabdalata a kasa nake yi ban sake hawa saman ba tun washe garin ranar da na tare a gidan. Duk da rashin jin kwarin jikina hakan bai hana ni tashi na bi shi bayan shi ba. Waya yake yi da Sukairaju a lokacin da na shiga d'akin tare suke zo dama tunda shi ya d'auko mu a mota ma. Na nemi kusa dashi na zauna a hankali Ina nazarin d'akin bai yi wata 'kura ba tunda ko'ina rufe yake da tagogi irin na gilashi da narka narkan labuleye a kewaye babu ma wata kofa da kura za ta shigo sai dai idan an dan gyara wasu guraran hakan ba zai zama lefi ba. Ya kashe wayar yana dubana a tsanake ya furta." Ya gajiya da jikin kuma?" A hankali na furta." Na ji sauki kai ma ya gajiyar hanya." "Ban gaji ba." Yafada idonsa a tsaye a kaina. Sai na yi kasa da nawa idon ina dan jin fargaba kad'an zan yi kokarin ganin na kare kaina ta kowace siga domin kuwa na fahimci zallan rikici da fitina a cikin kwayoyin idonsa." "Ina so ki gaya mini abinda ki ka taka, kada ki rufe ni Amina domin kuwa babu abinda na tsana a rayuwata sai zamba cikin aminci. Na kan ji na tsani mutum tsana ta har abada muddin na fahimci cewa yana zaune da ni da wata zuciya ta daban. Ki fito fili ki gaya mini me kike nema a wajena? Menene a can kasan zuciyarki dangane da zama da ni." Cikin nutsuwa na furta." Ban gane inda maganganunsa suka dosa ba Baba." Ya tsira mini ido da b'acin rai a tare dashi kafin ya gyad'a kansa ya ce." Kin san idan wani likita zai b'oyewa kowa wani lamari da ya shafe shi tsakaninsa da mara lafiyarsa ni dai alfarmata da yadda Ubangijina ya karramani a nan gidan duniya ba za a rufe mini wani lamari da ya dangance ni ba. Likitan da ya yi tsaye a kanki a daran jiya ya yi mini bayanin da ke kanki bai yi miki shi ba, ya sanar da ni dalilin zubewar cikinki wanda ki ka boye mini samuwarsa bincike ya nuna cewa lallai an yi yun'kurin fitar dashi ta kar'fi da ya ji, hakan ya haddasa matsala babba cikin ya canza mazauni, shi bai fice ba haka zalika kuma shi ba zauna daidai yadda ake so a mahaifar ba. Ya gaya mini biyu ne na farko ya fita jim kad'an bayan zuwanku asibitin na biyun ne sai da aka kai ruwa rana kafin su fitar dashi ko kina da ja akan hakan, ni dai na san Dr Iliyas haka kawai ba zai 'kir'kiri 'karya domin ya 'bata ki a wajena ya gaya mini ba, ya sanar mini ne domin akan akinsa yake ni kuma na aminta da bayaninsa sanin da na yi miki za ki yi aikata fiye da abinda ya fi haka. Na ro'ke shi ya rufe maganar ba don Ina gudun tozarci da tiriri na jama'a ba, nasan ni dai babu wanda zai zage ni, sunana kuma ba zai 'baci ba, na yi hakan ne kawai saboda idan maganar ta fita dole idan an rubuta sunanki za a rubuta nawa a gaba. Kuma da sauran igiyoyin aurena a kanki ba ni da yadda zan yi na 'karyata domin sakamako ne daga wajen mahukuta wad'anda suka san abin. In banda ke dashi Dr Iliyas din da ni na uku babu wanda ya san yunkurinki na fitar da cikin ta k'arfi saboda haka mu yi magana ta tsakani da Allah da annabi dake anan, na san matsayata lullub'e mini gaskiya kuwa zai iya janyo miki miki b'acin rai da fushi mai tsanani daga wurina." Cikin dauriya da ko'karin aro jarumta na ce." Ni wannan maganar ban santa ba. Sharri ya yi mini domin neman suna a wurinka to wai akan me zan zubar da cikin da Allah Ya ba ni, me ka yi mini ko ma ka yi mini wani lefi shi cikin Ina ruwansa da zan zubar dashi, kawai Allah Ya k'addari fitarsa ne a wannan lokacin amma ni kam ban san da wannan maganar ba.