← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 40

Sashe 2

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Ba mu dashi gaskiya anti Yagana ce babba a gidanmu a maza kuma Usani ne Hassan dinsa ya rasu. Ya gyad'a kansa tare da cewa." Tana gaya mini dan'uwanku hukuma ta kama da zargin damfarar wani mutum miliyan hud'u da rabi." Na ce." Shine me kuma? Ba zai wuce d'an'uwanta da na sani ba mamarta sai da ta yi aure a wani wurin har ta haihu sannan Babanmu ya aureta shine kawai abinda na sani. "Tunda har Mamanta tana auran mahaifinku ai idan da kara shi ma d'an uwanku ne ko ba haka ba ne." Na ce" Don girman Allah ka daina biyewa Hadiza bata da gaskiya fa, ba zan boye maka ba ko kwanaki nan karyar rashin lafiya suka shirya da Ummansu ita Fatin ma bata sani ba ka d'auki kudi ka basu har miliyan shida sannan kuma na ji labarin an ce ka bata jari har tana zuwa Dubai sarin kaya. kai baka gaya mini ba itama bata gaya mini ba, ko da yake ai ta san bata da gaskiya ba zata gaya mini ba, wannan ma ban yarda ba karya take yi wallahi." Jim ya yi yana nazari kafin ya ce." Ta bukaci na taimaka mata kasancewar bata da aure dana tambayi matakin karatunta ta ce mini ko sakandire bata gama ba a gidanku ke kadai ce ki ka danyi karatu to kin ji dalilin da ya sanya na d'auki kudi na bata da niyyar ta yi jari domin ta tsaya da kafafunta a matsayinta na bazawara rashin sanar dake ba shi da ala'ka da wani abu tunda ni ban iya alheri na fito ina shela ba." Da takaicinsa na ce." Don ka gaya mini sai ya zama wani abu to ta dalilin wa kasan Hadizan Ina ce 'yar'uwata ce." Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Ni ba 'yar uwata ba ce kenan?" Shiru na yi ina kallonsa. Ya girgiza kai bai sake cewa komai ba ya fara cin abincin dana hada masa. Bakincikin abinda Hadiza take yi mini ya hana ni sukuni sai da na bari ya fita zuwa gidan Hajja tukkuna na kira anti Yagana muka gaisa na gaya mata maganar tariyata a sabon gida sannan na sanar da ita irin rashin mutumcin da Hadiza take yi. Ta ce ai d'aurin gindin babarsu ta samu auran suke su gurgud'e miki Amina amma idan ba haka ba wannan ai zubarwa da kai mutunci ne tun mutumin nan yana yi musu kara da kawaici har sai sun kure ha'kurinsa ta zubar mana da mutunci wallahi " Na ce." Anti Yagana Ina ganin kawai zan je gidan ne mu yi duk wacce za mu yi da ita gaskiya na gaji da abinda take yi mini wallahi ba zan jura ba. Ta ce." Kada ki je yin hakan zai iya b'ata masa rai ai mai hankali ne shi ya san komai kawai yana biye mata na tabbata idan ya gaji ko sauraranta ba zai kara yi ba. Ki zuba mata Ido kawai saboda idan ki ka yi magana za a d'auka kece ki ke hana mijinki alheri shima kuma tunda bai gaji ba ai kudinsa ne ba na ki ba." [9/15, 9:26 AM] Aunty B: 82 Mafarin samun matsalata da Hajja kin amincewa da komawa legos kamar yadda ya zo yana gaya mini sun yanke shawara ita dashi akan ni na koma can din domin kula da Hauwa a matsayina na wadda ta yi haihuwa uku. A cewar Hajja duk da Hauwan nurse ce ai b'ata ta'ba haihuwa ba balle ta ce ga yadda take kuma koda ta zo haihuwar yana da kyau a ce da akwai wani a kusa da ita. Lokacin da ya zo yana gaya mini kawai jinsa nake yi da kunne domin na tabbatar da cewa zamana ne ba a buk'ata anan din saboda ya kafe kai da fata ba zamu tattaro mu dawo nan gabad'aya ba dole wata ta koma can tare dashi. Na farko dai Hauwa ba yarinya ba ce a lissafin ma shekaru ma ta d'ara ni da kusan shekaru hud'u sannan kuma wace irin haihuwa ce ba ta gani ba, idan ba a shigo da son zuciya ba ina ganin ita kanta ma za ta iya kar'bar haihuwarta idan ta kakare ai akwai asibiti sai su je can, zamana babu wani abinda zai amfana tunda ba wani shiri muke yi ba to kamar dai yadda ya nemi alfarma wurin inna Uwani Ina ganin shine maslaha kawai a kai mata dattijuwa daga cikin danginsu. Da har Hajja ta amince da da shawarar da ya yanke kafin ya bar gidan ta kira inna Uwani suka yi magana ita ta rusa shirin ta ce ita dai hankalinta sai ya fi kwanciya Hauwa ta dawo kusa har da yin kuka tana gayawa Hajja ai ta je ta taya ni rainon ciki har sai da na haihu tukkuna.. Wannan dalilin ya sanya Hajja ta ce ya gaya mini na shirya idan zai koma sai mu tafi a tare. Kuka sosai na dinga yi ina fad'in ba a yi mini adalci ba domin sai da na shekara daya a can kafin Hauwa ta tare me zai sanya kuma yanzu a ce mini na koma saboda wani dalilin da bai shafe ni ba, iyakacin gaskiyata na gaya masa ba wai ina b'akinciki da haihuwar da za su yi ba, ina ganin kamar akwai son zuciya a wannan hukuncin dukda Hajja ta wuce ta nemi wata alfarma a wurina na turje mata to amma na riga na gama tabbatarwa da kaina cewa wannan hukuncin itama ta yanke shine domin son rai da kuma farantawa 'yar'uwarta ai ya gaya mini tunda aka samu cikin ta rasa sukuni idan zai yiwu ita din sai ta sake komawa ta zauna mata kamar yadda ta zauna mini ai ba hujja ba ce a ce dole sai ni zan je na zauna tare da ita tunda suna da yadda za su yi. Rarrashin duniya babu irin wanda bai yi mini ba na ce ba fa zan bi shi ba domin da muna abun arziki da ita ne ma da sauki to kowa ta ciki na ciki me zai sanya na je na bautata mata daga baya wani sharrin ya b'ullo. Ya nuna ai saboda shi zan yi, idan ma bai isa ba to na bi umarnin Hajja kamar yadda ta buk'ata kada na bijire, na ce ai ba ra'ayinta ba ne itama ta yanke hakan ne domin ta farantawa 'yar'uwarta rai. Kwana da yini muna ta abu daya domin duk ta inda ya biyo nasan hanyar da zan zame kaina na nuna masa ba da hurumina ne ba, ni ma lokacin da na haihu 'yar uwata Hadiza ce ta zauna mini. Na kuma gaya masa ko da wasa kada ya sanar da mahaifina domin yin hakan zai janyo mana matsala mai girma saboda na riga na san halinsa sarai. Itama anti Yagana ban gaya mata ba duk da mun yi waya da ita a ranar muna tattauna matsalar da ta shafe mu amma har muka yi sallama ban fad'a mata maganar ba. Da yamma sai ga Hajiya Saratu na karbeta hannu biyu sosai muka gaisa dama can muna girmama junanmu akwai kuma kunya da kawaici shiyasa ko da ta fara yi mini maganar ban iya jayayya da ita ba kawai na yi shiru saboda Ina jin nauyin na ce mata ba zan koma ba yanayin dana shiga ya nuna mata cewa ban yi na'am da abinda suke so ba. Jiki ba kuzari muka yi sallama ta tafi.. Sai da ya shigo gidan yake tambayata Hajiya Saratu ta zo na ce masa eh daga haka ban sake wata magana ba. Ya dinga bibiyata yana so ya ji abinda muka tattauna da ita bance masa komai sai da daddare tukkuna ya kira ta a waya a gabana suka yi Ina jin sautin maganarta tana cewa dashi idan zai yiwu kawai ya ha'kura tunda abu ne na lokaci Hauwan ta dawo tunda haka suke so saboda itama tana ganin kamar idan aka ce dole sai na koma an shiga shakkina idan ta haihun anan an yi taron suna sai ya tsara yadda zaman zai kasance idan ma za mu dinga zuwa can muna yi masa wata shida shida mu dawo hakan zai yi alheri. Na fahimci azancin Hajiya Saratu kuma kamar ta zo da sasanci anan a wannan ga'bar zai iya ha'kuri tunda ta b'angaransu sun dage ya ha'kura ta dawo nan din har ta haihuwa abu ne na lokaci kad'an bayan ta haihu sai mu raba na je na yi wata shida idan na dawo sai itama ta je ta yi nata wattanin. Ya kar'bi shawarar ne saboda gajiya da ja'ina daka kowane bangare amma na fahimci dan ba yadda zai yi ne ya amince ya fara shirin komawa amma cike yake da jin haushina acewarsa ni ce ya kamata na dubi halin da zai shiga amma kishi da son rai ya hana ni yin abinda ya dace. Shiru kawai na yi masa ban tanka ba har ya kammala shirinsa babu cikakkiyar jituwa a tsakaninmu na yi ta so mu rabu cikin girma da mutunci yana bijirewa haka na zuba masa ido har ya kammala shirinsa ya tafi babu wadataciyyar sallama a tsakaninmu. Bayan tafiyarsa da kwanaki uku Hauwa ta dawo a gidan Hajja ta sauka na samu labari ne a wurin Hajiya Saratu a lokacin dana kira ta a waya da kuma sutturuna na can da aka kawo mini na kira Hajiya Saratu ne a waya domin na sake wanke kaina tunda ita ta fahimce ni. A ranar kuma na kira shi duk da bai ne me ni ba, amma nasan yanzu ya huce daga fushin da yake yi tunanina ne ma ya rabu kashi biyu ban sani ba da Yusi ya koma ko kuma ya bar shi a gidan Hajja nasan dai da wahala ya bar shi a can din saboda makaranta kuma akwai sabo mai yawa a tsakaninsu zamansu a tare zasu debewa juna kewa.'' Wallahi ban zaci abin ya kai haka ba a ganina ban cancanci haka ba a wurinsa idan fa da adalci shima ya so kansa ne idan kullum zai dinga zuwa nan yana komawa yana da ikon yin
Chapter 2 · 0% Book details