← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 40

Sashe 38

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haihuwa na yi cikin koshin lafiya haihuwar da ta sake bud'e kofofin arziki da alherai masu yawa. Duk irin zullumi da fargabar da na kasance a ciki a lokacin da nake d'auke da cikin da haihuwar ta zo sai na yi cikin sauki da taimakon Allan da ya ba ni ajiyarsu a cikin cikina. Lafiyata lau hakan nan yaran ma da na haifa lafiyarsu lau duka ba su d'auke da kowace irin lalura daidai da irin murar nan da ake haifar jarirai da ita tagwayena ba su d'auke da ita..
Tubarkala ma sha Allah shine abinda kowa yake fad'a a kansu domin kuwa yadda Allah ya gina musu jiki da lafiya tun a ciki ba wanda zai d'auka cewa 'yan tagwayene dalili wasu akan haifesu da rashin lafiya irin ta jarirai ko yan'kwanewa da yamushewar fata, su kam kalau suka fito cikin mahaifa daya kamar kuma an tsaga kara babu ita inda suka yi bambanci. Tunda aka haifesu ake ta hasashen da wa suke kama wasu suce da ni, wasu kuma su ce da babansu. Ita Hajja ma cewa ta yi da inna Uwani suke kama mai gabad'aya kenan. Jin haka ya sanya ina Uwani kasa rufe bakinta daga zarar an yi magana sai ta ce ai da ita suke kama. Can dangin Hajja suka kwaso domin ni kaina basa kama da ni balle kuma Babansu Hajja ta ce suna kama da inna Uwani shi kuma ya ce da Samira suke kama matarsa ta farko. Ni dai dariya kawai nake yi musu domin ba ni da ta cewa ganin yaran daidai da yatsuna ba su d'auko ba.
Umara ya tafi a tsakankanin haihuwar ya je ya nuna godiyarsa ga Allah subahanawu-wata'ala. Satinsa daya ya dawo ya ce zai shirya walima domin sake nuna godiyarsa ga kyautar da Allah ya yi masa. Ban so ba saboda ba na so abinda zai kawo rud'ani a zamanmu na ce masa lokacin da aka yi masa haihuwar fari ma bai yi ba sai yanzu ya kamata ya bar shi kawai umarar ma da ya yi ta isa. Fad'in haka ashe lefine a wurinsa yana fad'a na kyaleshi ya yi yadda yake so kudinsa ne kuma yaransa ne ba zan tsara masa abinda zai yi ba, Yana da kyau ya nunawa Ubangiji godiyarsa ta sigogi da yawa.
Hajja da inna Uwani da ita kanta Hauwan suka shiga maganar domin kasa barinta ya yi a tsakaninmu sai da har suka fahimta. Nan suka had'a baki gabad'aya suka nuna goyan bayansa akan a yi walimar ko da na nesa ba su zo ba ya yi ai hadayace ga jama'a.
Jin haka ya sanya na yi musu shiru ban kara cewa uffan ba na zuba musu idona.
Amaryarsa akwati biyu ta yi da kaya kowacce shake wai Hassana daya usaina ma d'aya. Wallahi rasa bakin magana na yi a lokacin da na bude kayan Ina dubawa. Da yake duk a gabansu ne Hauwa har tana cewa kada matar nan ta rusa jarinta akan yi wa 'ya'yan miji gwaninta. Ina dariya na ce ko daya tunda ki ka ga tana irin wannan kyautar ta yi nisa ne wata'kila yadda kike d'aukarta ta wuce haka. Hajja ta ce kuma ma dai mai son yi ce domin wasu akan su bayar sun gwammace wuta ta cinye domin Ubangiji yana duba duk wanda ya azurta baya fitar da kazantar dake cikin dukiyarsa da kansa zai fita ta hanyar tashin gobara ko ta wata sigar ta daban. Ta nisa kafin ta cigaba da cewa mijinku shi yake gaya mini cewa har gidan marayu ne da ita a can garinsu jos din tana d'aukar nauyinsu bayan makarantu da massalatai da ta gina duka hobosi ga tsohon mijinta da ya rasu. Wannan dalilin ya sanya ni jin kaunarta a cikin raina domin kuwa macace ta gari, ina kara horarku ku zauna lafiya da ita, kuma kada ku dauketa a matsayin kishi sai yayarku domin ta girmeku ku muntata da kyau.
Sosai jikina ya kara yin sanyi da sha'anin matar wato mutane suna daukarwar kansu zunubi a duk lokacin da suke munana zato akan mutum alhalin ba su da sheda kawai zargi suke yi da k'age. Sai na tuna irin maganganun da Sahura ta dinga fad'i a kanta a lokacin auransu da Yallabai ya zama dole kuwa Sahura ta yi nemi gafarar Allah domin kuwa ta yanke hukunci akan abinda ba ta ta'ba ga ni ba.

To walima ta kyau sosai, kuma ta samu halartar manyar mutane malamai da ma'aikatan gwamnati har ma da 'yan siyasa. Sahura ta samu zuwa itama yan gidanmu kuwa Babanmu ya samu halarta tare da Baba Sule sai anti Sakina da Fati. Anti Yagana da Yafalmata sun zo Baban Saude kuma a lokacin baya gari sai da ya kira ni a waya ya yi mini barka ya kuma kira maigidan shima ya yi masa barka. Hamusu ma ba a bar shi a baya ba ya zo shi kadai Amma domin da ya gaya mini za su zo tare da Gwaggo na ce masa a a saboda tafiyar mota ce Kuma bata da lafiya sosai na yi alkawarin idan na yi arba'in da kaina zan kai mata yaran ta sanya musu albarka.

An yi hidima sosai yara sun samu alheri irin wanda ba zai misaltuba hotonsu kuwa yana ta yawo a kafafen sadarwa tare da yayansu Khalil da ya yi wayo har yana gudu da kafafunshi.
Gida ya watse ya rage mu kad'ai. Ni da Hauwa muka cigaba da rainon yaran a wasu lukutan kuma Hajiya Maryam tana aikowa a d'aukar mata su, har su d'an jima a wajenta kafin su dawo.
Kwanana arba'in da takwas na shirya zuwa kano. Amma ina jimanta yadda zan yi dawaniyar yaran ni kadai dama burina idan na isa na samu Baba Tabawa mu yi magana idan ta amince mu tafi tare domin zamanta a tare da ni zai taimaka kwarai tunda kaf gidajensa daga na Legos din har na abujan babu mai aiki mace duk maza ne. Hajiya Maryam ce kawai naga tana da mai aiki dattijuwa mai suna Taburni, itace ma takan yi dawaniya da yaran idan an akaisu can wajenta.
Ya ce Hauwa ta shirya sai mu tafi tare. Sosai na ji dadin hakan kuwa ban yi nauyin baki ba na yi masa godiya sosai ya ce kwana hud'u kawai ya ba mu dama za mu yi mu dawo. Kwanakin sun yi kadan amma ban iya gaya masa ba saboda Ina gudun ya ce ya fasa ma gabad'aya tunda ya nunawa kamar akan dole ya ha'kura da tafiyar.

***
Alhamdulillahi lafiya lau muka sauka a kano. Gidana na sharad'a muka sauka inda muka iske shi tsaf Baba Tabawa da Yusura sun gyara ko'ina har an yi mana abinci. Na yi mamaki kwarai da gaske nasan wannan aikin ba na kowa ba ne sai Sahura domin mun yi waya da ita ana i gobe tafiyar har ta na yi mini tambayoyi ashe abinda ta shirya kenan. Hidimar tace yin cefane mai kyau ta kuma sanya a yi mana abinci mai rai da lafiya. Cikin zuciyata na sake kudire wani alheri da ya jima a cikin zuciyata.
Dadaddare Ayuba ya shigo mana da kayan abinci ya kai a store bisa umarnin maigidan ne ya tsaya muka gaisa sosai kafin ya juya ya fita.
Ko da na gayawa Baba Tabawa kudirina ba ta yi jayayya ba ta ce ta amince za ta bi ni duk inda zan je, yadda na nuna mata tausayi da kulawa a lokacin da take neman d'auki yanzu ne daidai lokacin da za ta biya ni. Ina dariya na ce mata ai ni don Allah na yi mata ba don ta biya ni ba. Daga ranar kuwa ta shiga hidima da yaran bakid'aya.
To duk inda ya kamata na je a tsakankanin kwanakin da ya ba ni mun je ne tare da Hauwa domin duk inda na ajiye kafata itama nan take ajiye tata. Baba Tabawa na goye da Hassana ni ina goye da Usaina ita kuma Hauwa tana ri'ke da Khalil a hannuna.
Ayuba ne ke jan mu a mota rana ta farko a gidan Gwaggo na yini sai yamma muka yi mata sallama muka nufi gidanmu anan muka yi magariba. Sannan muka nufi gidansu Sahura dake kusa damu muka gaisa sosai da mamansu ta d'auki yara ta sanya musu albarka.

Washe gari a gidan Hamusu muka yini amarya ta zama 'yar gari Hamusu kuwa ya rasa Ina zai tsoma ransa ya kai ya kawo ya siyo wannan ya ajiye ya siyo wannan ya ajiye bayan uban girkin da ya sanya aka yi mana. Sai da na ga abin ya yi yawa tukkuna na yi masa magana sannan fa ya dan samu nutsuwa.
Dubu ashirin na bawa amaryarsa na ce ta sayi janbaki ta kar'ba tana godiya ta rako mu har bakin gate.
Da muka fito tare da shi nake tambayarsa ya ake ciki da karatun Turmizi tunda shine ya shige gaba wajan kai shi makaranta kamar yadda maigidanmu ya yi alkawari nan yake ba ni tabbacin alhamdulillahi an samu cigaba kwarai da gaske domin hankalin yaron ya fara dawowa jikinsa domin lokacin da aka kai shi makarantar ma baya hayyacinsa dalilin irin shaye shayen da ya fara yi ya hadu da wad'anda suka fi shi wayo suka bashi kwayoyi har hankalinsa ya gushe garkuwar jikinsa ta raunana. A Tasha aka je aka d'auko shi yana zagari da kai kawo tare da sururai. Ya ce ko wancan watan da ya je dubasu ya same shi garau kuma ya kama karatu ka'in da na'in domin malaman a tsaye suke a kansa kuma makarantar cike take da tsaro babu ta inda yaro zai haura ya gudu.
Kamalu kuwa farkon watan da zamu shiga zasu sallameshi da izinin Allah dama kuma shi mun gama magana dashi zai zauna a hannunsa domin taimaka masa da cigaba da gudanar da harkokin da muke yi na kasuwanci.
Chapter 38 · 0% Book details