← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 40

Sashe 25

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Murmushi na yi mara armashi na ce." Sahura hakan da na yi shine kwanciyar hankalina da kuma samun nutsuwata don Allah kada ki ka ga lefina kada ki 'kullace ni, addu'a kawai nake so ki taya ni da ita, sannan maganar anti Yagana kuma ni na fi kowa sanin halinta kwata-kwata ba ta kar'bar uzurina in dai akan mutumin nan ne to bata ta'ba fahimtata kamar yadda ke ma ba kya gane nufina. Wannan dalilin ya sanya ban gaya mata ba domin lefinsa za ta take da k'afarta ta rufe gabad'aya ta d'auka ta d'ora a kaina, to shiyasa ko da na yanke shawara ban nufe ta ba kai tsaye na yi tafiyata a gidan Baban Saude."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." To ke yanzu me ki ka yanke a zuciyarki rabuwar ki ke ganin itace mafita a gare ki ko kuwa?"
"Ban yanke komai ba Sahura sai abinda Allah Ya zaba mini, idan har rabuwar itace alheri ina farinciki da hakan, idan kuma akwai sauran zama a tsakaninmu to gaskiya ba zan koma ba lallai sai ya fahimci cewa abin fa da yake aikatawa kuskure ne, sai ya dauki matakin gyara da alkawari tare da sharad'in hakan ba zata sake faruwa ba.

Murmushi ta yi irin na takaici kafin ta ce." Amina wani lokacin ina mamakin tsaurin idonki wallahi to wai Baban Sauden ki ka wakilita da ya kira Yallabai din ya titsiye shi akan kuskuran da mafi rinye ke ce mai shi. Idan fa an bi ta 'barawo to a bi ta mabi sawu na gaya miki tun ranar da na zo gidanki wallahi ke ce mai lefi mai yasa za ki zubar masa da ciki saboda wani banzan dalili da bashi da tushe. Son zuciya ne fa wannan tsagwaronsa ki ka nuna masa a zahiri saboda ke ai kina da yaran shi kuwa fa. Ki bari ki haihu mana ki ga abinda za ki haifa da lafiya ko babu kawai sai ki yankewa Allah hukunci, ba zan gaji da gaya miki ba, baki da gaskiya."
Cike da tsantsar takaici na ce." Ban kyauta ba din Sahura duk abinda za ku yi ku yi din, haba na gaji da magana daya wai ana aure dole ne ko kuma tilas aka ce sai na zauna da mutumin nan da za ku bi ku tsangwameni. uwata ce ke da za ki kira ni a waya kina gaya mini maganar da ranki ya so, ko kuma ke ce ki ke zaune da mutumin nan ne, kwata-kwata kun kasa fahimatata, na yi kuskure na nemi afuwar Allah amma gabad'aya kuna juya mini magana saboda kawai wani dalili naku. Shi din sahabi ko kuma Annabi ne da ba za a 'bata masa rai ba. Ko annabawan Allah suna kuskure balle wani bawa kuma Allah Ya yafe musu saboda haka a yanzu daga ke har anti Yaganar ba na buk'atar ku fahimce ni, duk abinda za ku yi akan lamarin kun jima ba ku yi ba." Ina gama maganata na kashe wayar raina a mafisar b'ace. Tunda muke da Sahura ba mu ta'ba musayar yawu mai zafi irin wannan ba. Haba na gaji da jan magana d'aya muddin ba za su gane hujjata ba to sai mu yi ta tafiya a haka ba zan sake yarda wata ta kira ni a waya ta 'bata mini rai ba.

Da takaicin abinda yà faru tsakanina da Sahura na yini duk yadda na kai ga ko'karin ganin sun fahimceni ita da anti Yagana abin ya gagara har sai da sa'bani ya gifta a tsakanimu, to kuwa ta yaya za a yi kuwa na manta da mutumin nan tunda ta dalilinsa anti Yagana take furta maganar da ban ta'ba tsammanin fitowarta daga bakinta ba, wai za ta rabu da ni har abada saboda shi yau ga Sahura tana gaggaya mini ba'kaken maganganu. Ban ta'ba nadamar saninsa ba a rayuwata sai a wannan lokacin.
Da daddare muna zaune a babban tsakar gidan gabad'aya har da maigidan Baban Saude an shimfida masa dadduma mu kuma muna zaune a 'katuwar tabarma ana ta hira cikin nisha'di cikin raina ina ta mamakin hakan wato duk wanda zai k'alubalanci Baban Saude akan wani lamari tabbas ba zai zauna dashi ba ne, sannan kuma bai gama karantar hali da d'abi'arsa ba.
Chapter 25 · 0% Book details