← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 40

Sashe 37

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ganin yadda muka k'ulle muka zama tsintsinya madaurinki d'aya ya sanya shi shiga hankalinsa ssosai. Tun ranar da muka yi zaman nan bai sake yin wata magana da ta danganci matarsa ba saboda ganin yadda muka nuna masa ba mu yarda ba a tun farkon fari. Dama neman magana ne kawai tunda na farko ai bai ga mun ware ta ba, sannan bai ga muna neman fitina da ita ba, maganace a ka zauna ana tattaunawa wadda kowa yake da hakki akai to babu dalilin da zai sanya shi ya budi baki ya yabe ta a gabanmu bayan alfarmar da muka yi mata. Macace mai nagarta kuma wadda take amfani da ilminta a inda ya dace. Duk irin kushe da kiyayyar da mutum zai yi a kanta wallahi kyawun halinta sai ya sanya wataran mai kushiya akanta ya yaba mata.
Ina jin kunya da nauyinta sosai, ba don komai ba sai don yadda take k'aunar abinda ya jib'anceni. Na jima ban ga mutum mai kara da kawaici irinta ba.

Daf da zamu tafi Legos muka yi waya da Sahura take gaya mini an kawo kudin Yusra an kuma sanya rana shekara daya mai zuwa. Na ce har saurayin ya gama ginin kenan ta ce mini saura kad'an. Daga sanda muka yi waya da ita na ce ta nemi mai wannan lambar 08089965176 wato garkuwar mata itace wadda nake sayan magunguñan Islamic a wajenta na ce su yi magana tunda tana nan kano akan ta hadawa yarinyar maganin sanyi da wanda zai sanya kirjinta ya ciko kafin zuwan lokacin bikin ta kara cika tunda har ga Allah yarinyar bata da wani jiki na arziki yanzu kuma tana matakin shekaru goma sha bakwai a duniya. Idan sun gama magana da mai maganin ni kuma zan tura mata kudin sai ta aika mata dashi.
Ta dinga godiya har sai da ta sanya ni na ji haushi na ce ta bari ba na so domin kuwa Yusura haihuwarta kawai ta yi amma na fi ta cin moriya kuma ban yafe mata ba muddin ta sayi ko cokali akan sha'aninta kawai ta bar mini hidimata ta ce. Ta dinga dariya tana fad'in Lallai abin har ya kai haka. Na ce ya wuce hakama a wajena domin kuwa abinda ya shafeni.
Kafin mu tafi sai da na kira Babanmu duka na yi masa bayanin abinda yake faruwa amma ban sanar dashi matsalar da ta kaini wajan Baban Saude ba, sosai ya yi mini addu'a da fatan alheri. Ya kuma tabbatar mini da cewa ana samun cigaba ta bangaran Ummansu Hadiza domin yanzu hankalinta ya fara daidaita ta dawo hayyacinta ta ha'kura da kaddara ta barwa Allah komai. Amma har yanzu Hadiza na can gidan yari a ajiye ba a kai ga yanke mata hukunci ba ana ta neman ita wadda suka had'a kai suka yi aika-aikar wato Hajiya Alili."
Mun yi waya da anti Yagana na gaya mata za mu wuce legos ban rufe mata komai ba duk na gaya mata irin yadda muka tsara zamantakewar gidan. Ta ce mini hakan da na yi shine daidai a matsayina na babba daga cikinsu dole ni zan dinga 'kokarin d'aukar girma saboda tabbatuwar zaman lafiya.

Sati uku da komawa legos na fara laulaye-laulaye. Ciki fa ya samu abinda ake nema ban gaya masa ba da kansa ya fahimta ya dinga murna kamar me ni dai dariya kawai nake yi masa amma can 'kasan zuciya cike nake da zullumi da fargabar abinda zai kasance bayan na haihu. Shi kuma maganarsa daya Allah Ya sa tagwayene. Kullum abinda yake cewa kenan sai dai kawai na yi murmushi gefe guda kuma na tsananta addu'a akan Allah Ya ba ni d'orarre.
Ban yi tsammanin zai gayawa kowa ba kawai watarana sai Hajja ta kira ni a waya muka gaisa dama kuma sa'i da lokaci takan kira ni, ko kuma ni na kira ta mu gaisa har ta tambayeni zamanmu na ce mata komai lafiya. Cike da farinciki take magana ai maigidan ya gaya mata na samu ciki. Ta dinga ba ni shawarwari akan na kula sosai kada a sake samun matsala irin ta baya. Idan ma ina so sai ta zo ta zauna mini irin na goyon cikin baby Nana.
Na ce mata in sha Allahu zan kula sosai amma ta yi zamanta tunda bata da wadataciyyar lafiya bayan haka kuma abun zai zama wani iri muddin Hauwa ta ji labari ba zata ji dad'i ba, abinda haihuwa ba ta farko ba ce, babu wata matsala da za ta faru.
Da wannan na rufe bakinta ta ce mini shikkenan amma dai za ta sanya a rubuce mini al'kur'ani maigirma. Godiya sosai na yi mata muka yi sallama. Hajja macace mai dattako kwarai da gaske tana k'aunata fiye da tunanina don ma an yi yun'kurin shiga tsakanina da ita a baya.

***
Watanni shida ciki ya bayyana ya fito sosai duk wasu gwaje-gwaje da scanning an yi mini tagwayene duk mata. Ya rasa ina zai sanya rayuwarsa duk fitina irin tasa ha'kura ya yi a sati bai fi ya kwanta da ni sau biyu ba wai kada yaran dake cikina suga kamar an takura musu. Acewarsa yawan motsa ni da yake yi zai sanya su dinga shan wahala. Abin sai ya ba ni dariya da mamaki. Tun suna ciki basu fito ba yana nuna musu k'auna irin haka, ai ni ma 'yar wani ce mai yasa bai duba hakan ba, a lokacin da ban samu cikin ba yake galabaitar da ni, wato kenan kowa nasa ya sani.
A haka na yi wata shida a tare dashi a legos babu wanda bai san ina da ciki ba domin kuwa duk ya sanar da iyalinsa Hauwa har bidiyon call muke yi da ita musha hira Khalil ya yi wayo sosai yana koyar zama. Wasu lukutan ma idan na tambayeta yana Ina sai ta ce yana can wajansu Yusi idan ba nono ya buk'ata ba a can yake yini idan ba makaranta. Idan kuma da akwai idan za su tafi sai su mayar mata dashi. Da kanta ba tambayarta na yi ba take gaya mini yadda suke zaune lafiya domin a wasu lukutan ma takan shiga wajanta su hira itama kuma takan shigo. Na ji dadin hakan sosai da sosai, yanzu dai hankalinmu ya kwanta babu wani kishi na jahilici bayan haka kuma dukanninmu ba yara ba ne iyayene masu yi wa na kasa dasu nasiha.

Tare muka koma da shi abujan sai da ya yi sati biyu tukkuna suka juya shi da Hauwa da yaronta. Duk dauriyar da ya dinga nunawa sai da na gane hankalinsa gabad'aya yana kan abinda yake cikina kawai don ba yadda zai yi ne ya dawo da ni, ya d'auki Hauwa domin babu irin rarrashin da bai yi mini ba akan na zauna na haihu a can a gabansa a cewarsa sai hankalinsa ya fi kwanciya na ce masa a a, mun riga ai mun gama magana tuntuni babu dalilin da zai sanya yanzu a warware idan har za a yi mini adalci a lamarin wattani uku kacal za su yi a can shi da ita ta dawo a lokacin ma na haihu in sha Allahu rabbi ko da ban haihu ba to kad'an ya rage. Da haka ya ha'kura smma ba don ransa ya so ba.

Bikin Hamusu ne ya tashi gadan-gadan domin kuwa yarinyar da ya jima yana nema burin mahafinta ya cika ta kammala karatunta wannan dalilin ya sanya uban ya ce a d'auki wata biyu kacal a yi a gama komai
Ya kira ni yana gaya mini duk abinda yake faruwa. Na ce masa duk abinda yake bukata ya nemi Usaini domin shi yake kula mini da shagunana ya had'a lefe abinda babu ya fitar da kudi ya saya amma ya yi mata akwatina shida ya kuma sanya mata kaya masu quality. Godiya ya dinga yi mini sosai na ce babu buk'atar hakan domin kuwa duk abinda na yi masa babu fad'uwa hakkinsa ne tunda dukiyar tare muke nema. Gini kuwa dama ya kammala abinsa can unguwar maidile ya sayi fili ya gina irin na zamani tuntuni gidan ya kammalu har bidiyo ya yi ya turo mini. Na ce masa idan sun tare ya nemi solar mai girma ya saya sai a sanya masa a gidan tunda na lura unguwar kamar sabuwa ce bata gama cika ba babu wutar nepa.

***
Bikin ya matso sosai daga can suna ta shirye-shiryen a lokacin cikina watanshi bakwai da satika. Da kyar nake gudanar da abubuwan da suka zame mini dole saboda nauyin da cikin ya yi mini ya yi girma sosai ya kara sanya ni na d'unkule. Amma ina da burin so na ga na samu halartar bikin Hamusu dalili kuwa anan shine yaron ya wuce komai a wurina ni ce uwa kuma uwar dakinsa.
Daga tambayarsa akan ya barni na je tunda ai tafiyar jirgi ce ba mota ba kuma zan motsa jikina na shiga cikin jama'a. Sai abin ya zama rigima saboda ya san ma ba bari na zai yi ba ya mayar da abin tashin hankali ya dinga sakin maganganu har sai da ya fusata ni dama haka yake so na ji haushi mu yi fad'a na kashe wayar raina a b'ace cikin zuciyata Ina fad'in idan ba zaka bari na je ba menene kuma na yin tijara kawai a ce ba zan je ba shikkenan sai magana ta mutu.
[10/1, 9:47 AM] Aunty B: 99
Haka aka ci aka cinye bikin Hamusu babu ni uwar biki, sai hotona da ya turo mini nan naga ashe har da su Dada da anti Yagana sun samu damar zuwa bikin. Na ji takaici sosai amma haka nan na ha'kura na yi masa addu'ar samu zaman lafiya madawwami. Amma na yi masa alkawari idan na haihu lafiya takanas zan zayarci kano saboda shi.

***
Duk abinda Ubangiji Allah Ya hukunta walau mai dad'i ko mara dad'i yana da iyaka. Kuma cikar mumini kenan yarda da kaddara kowace iri ce wannan shine yake tabbatar da cewa Allah yana sane dakai kuma duk jarabtar da ya yi maka idan ka cinye ba ba tare da ka bi wata hanyar ka sa'ba masa ba to zai maka tagomashin wanda kai kanka ba ka yi tsammanin irinsa ba.
Chapter 37 · 0% Book details