Sashe 19
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Sannu a hankali kwanaki suka cigaba da tafiya wattani ma suka 'kara nisa babu jituwa a tsakaninmu domin kuwa ya'ki ha'kura da abinda ya faru ya k'ullace ni da gasken gasken yau wata biyar kenan ina lissafi ganin mun kusa rabin shekara ba ma magana babu wata kyakyatawar kulawa ta aure sai na fara tunanin nemawa kaina mafita domin kuwa yana da kyau na san matsayin idan auran ne to idan kuma ba ya yi sai ya sauwake mini akan dai ya shareni ban san a wace makoma nake ba.
Wata ranar litinin tun wajejen tara na safe na fita na je gidanmu akan lamarin Hadiza domin hukuncin rataya aka yanke mata amma sai nan da shekaru uku tukkuna a cewar alkalin za ta zauna a gidan prison ta kar'bi horo mai tsanani kafin a zartar da hukuncin.
Tun bayan yanke hukuncin aka rasa gane kan Ummantasu abinda take yi kamar na mai tabin kwakwalwa shine Babanmu ya ce na taimaka a kaita asibitin dawanau domin su binciki lafiyarta domin kuwa baya yi mata kallon mai hankalina.
Bincike ya nuna bata da wata matsala sai damuwa da tunani shine ya haddasa mata zaucewa depression yake nema ya kamata. Suka bata magunguña amma ba irin na mahaukata ba muka dawo gidan na dinga tausarta da bata ha'kuri tare da kawo mata misalai na rayuwa. Ta dinga kuka tana ba ni ha'kuri wai hakkin abinda ta yi mana ne da Mamanmu yake bibiyarta don Allah mu yafe mata. Na ce mata babu hakki kawai ta d'auki hakan a matsayin jarabawarta.
Sai bayan isha'i na koma gida. Na tarar Baba Tabawa da Yusura suna kallon tarihi Annabi Yusuf a Mbc drama a tsaitsaye na tsaya a falon muka dan yi magana kafin na shiga na yi wanka tare da sauri alwala na yi Ishai a d'akin na ce Yusura ta kawo mini abinci don tashin hankali bai barni na ci wani abincin arziki ba duk kuwa da cewa Ummansu Saminu ta ciko mini kwano da shinkafa da miya har da salak da nama. Amma halin da Ummansu Hadiza take ciki ya sanya mini fargaba da nadamar rayuwa ashe dai da gaske ne karin maganar nan da ake cewa alhaki koikoyone ne gashi dai da bakinta tana fad'in abinda ta aikata.
Abinci na ci sosai na koshi Yusura ta zo ta kwashe kayan ta fita da su. Sai a lokacin na samu sukunin duba wayata cikin nutsuwa nake bin komai a hankali Ina dubawa na shiga Whatsapp bangaran status ina d'an dubawa a nutse can sai na ga ya yi status hannuna na rawa na shiga ina mamaki domin sai na ce tunda mukayi serving din lambar juna dashi ban ta'ba ganin ya d'ora status ba.
Katin d'aure aure ne mai d'auke da sunansa. Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Dambatta da Hajiya Maryam Abubakar Sabi'u Jos wanda za a d'aura ranar juma'a mai zuwa a babban massalacin Juma'a na garin jos din bayan saukowa daga sallar Juma'a.
[9/23, 8:02 PM] Aunty B: 91
Wani irin yanayi na shiga na tsantsar tashin hankali da fargaba wanda ba zan iya misalta irinsa ba. Idan hasashena daidai ne Hajiya Maryam ce wadda na sani matar abokinsa Alhaji Amadu da ya rasu wattanin baya.
Amma fa zahirin gaskiya al'marin ya ba ni mamaki ba kad'an ba. Katin d'aurin auran dai nake sake dubawa da tu'ajibi a tattare da ni wato yana hasashen samun abinda abokinsa yake samu daga wurinta kafin rasuwarsa kenan.
To hakane mana tunda ai ya sha fad'a mini abokinsa ya yi sa'ar mace tana da gayu da kula da kuma tarairayar miji shine dalilin da ya sanya tana fita daga takaba ya yi wuf da ita.
Sai wannan ya sake tabbatar mini da cewa wato shi dai namiji har mace ta mutu ba zata daina d'aukar darasi akansa ba.
A hankali na jingina bayana jikin gado ina cigaba da nazarin yadda al'amura suke tafiya a wannan duniyar. Ai babu mamaki don ya manta da sha'anina tunda akwai babban lamarin da ya sha kansa wànda yake hasashen samun nutsuwa a cikinsa. Na dinga danne hawayen dake ko'karin k'wace mini amma sai da suka fara gudana kuma da 'karfinsu suke zuba a kumatuna. Wato duk irin juriya da ha'kuri da kulawar da nake yi da mutumin nan bai ga ni ba ta wannan hanyar zai saka mini. Hanci na ja tare da girgiza kaina domin duk yadda na so ganin na yi dauriya akan lamarin naka sa yi kukan ne kawai zai sanya mini jin sasaauci a cikin zuciyata. Yana da kyau a wannan ga'bar da muke ciki ni dashi na san menene matsayina domin kuwa a shari'a ma aure yana dab da 'baci idan muka cigaba da tafiya haka. Zai auri Hajiya Maryam babu wanda ya ji ya gani, cikin rufin asiri alhalin itama bazawara ce kamar ni kuma 'yar kasuwar da take 'ketarawa 'kasashe sarin kaya. Ya lullube sirrinta ya kuma rufe idonsa ga ganin aibunta tunda dama ai tun kafin aure yana 'kwarzanta nagartatta. Ni kuwa motsi kad'an zai kira ni da gagararriya fitinanniya mara kamun kai saboda kawai na dogara da kaina, ina sana'a ban nema a wurin wani ba. Kullum cikin zargi nake a wurinsa saboda wad'annan dalilai ita kuwa duk da ta girme ni kuma ta jima tana harkokinta ya aureta a haka saboda dama hausawa suna fad'in kowace kwarya da abokin burminta matar abokinsa ce, kuma macace mai dukiya da duniya ta shaida hakan. Bayan haka kuma 'yar gayu ce kuma 'yar boko domin kuwa gabad'aya ta yi mana zarra ta ko'ina da ni da Hauwa sai da mu take bayanta.
Wad'annan zantukan zuciyata take ta zayyano mini tare da nuna mini lallai na tashi na kare mutuncina muddin na bari ya zube to don kowa ya hau ya taka ba wani abu ba ne.
Cike da faduwar gaba da tunani nake nazarin ta Ina zan fara domin yanzu ina yin wani motsi daga 'bangaransa za su ga kamar kishi ne don ya yi aure ko da na fadi halin da nake ciki babu wanda zai fahimce ni tunda shi bai fito ya fadawa kowa ba. Idan na nufi Hajja da maganar dole za ta bukaci sanin dalilin da asassa mana rigima wanda fad'insa zai janyo mini zubewar 'kima da mutunci da mummunan zargi.
Amma babu shakka Hajiya Maryam sai ta ba ni yarona domin babu yadda za a yi na zuba ido a dinga juya ni alhalin ni ma Allah Ya rufa mini asiri. Daf ake da sallamo su Kamalu daga makaranta ni ma zan hada kan yarana waje daya kamar yadda ta had'a kan yaranta waje guda.
Kuka na ci na 'koshi na hak'urk'urtar da kaina tare da barin abin ya tura kad'an kafin na nemawa kaina mafita don na yi rantsuwa da Allah da annabi wata d'aya kawai na kara akan wad'anda suka gabata idan bai neme ni ba zan tattara na bar masa gidansa sai dai ya aiko mini da shedar saki domin kuwa ban amfanin zaman da nake yi ba.
Da kyar na iya rintsawa a daran saboda tsananin damuwa na tashi da ciwon kai irin na gefe d'aya da kyar nayi wanka na karya kummalo Yusura ta kawo mini abin kari d'aki don ban iya fita falon ba saboda yanayin da nake ciki na rashin sukuni. Sahura ta kira ni a waya a lokacin da nake karyawa muka gaisa kad'an domin na gagara daurewa muryarta har rawa take yi ta fara fad'in." Amina da gaske ne oga zai auri Hajiya Maryam jos matar amininshi da ya rasu watannin baya, a wajan aiki ne na ji ana ta maganar wallahi shine na ce bari na kira ki na ji."
Na ce." Eh da gaske ne ranar juma'a za a d'aura auran." Sai ta shiga jimami da zullumi kafin daga bisani ta furta." Ban yi maraba da auran nan ba 'kawata ina jin tsoron matar nan ta shigo ta tarwatsawa Yallabai gida domin kuwa muguwar 'yar duniya ce ga bin malamai na tsiya a wurinta."
Na ajiye kofin hannuna a nutse na ce." Ke a Ina ki ka samu wannan labarin Sahura babu kyau fa zargi da zato akan abinda ba ki da tabbas a kai."
"Amina da gaske ne wallahi muna tare da wata 'yar garinsu anan wurin aiki itama aure ne ya kawota nan garin itace take ba ni labarin gidansu da ita kanta Hajiya Maryam din sannan anan wajan aiki ma na ji ana ta maganarta wai bata da hali."
Na ce." Ni dai ba zan gazgata maganarki ba Sahura tunda na zauna da ita na 'yan kwanaki ban hango wani aibu mai muni a tare da ita ba. Idan ma tana asiri da jefe-jefe ni dai na yi mata nisa wallahi Inna Uwani da Hauwa sun buga sun bari Sahura kin san duk wanda ya rike Allah Ya kama dahir don haka ki bar maganar nan kawai domin ni a halin yanzu ma ba itace a gabana ba wallahi.
A sanyaye ta ce." To shikkenan na bari tunda kin ce haka amma fa kema ba zama za ki yi ba kawai ki zuba ido domin wallahi tallahi matar nan za ta iya raba ki da mijinki."
Dariya na yi wadda babu nishadi na ce." Tun kafin ma maganar aure ta ratsa tsakaninta dashi ai ya sa waigi mai girma a tsakaninmu don haka ni ba zan zargeta ba Sahura."
Shiru ta yi nasan tana nazarin maganata ne. Na ce." Kin ga idan kin taso daga aiki ki zo za mu yi magana akwai abubuwan da suke faruwa wanda dole sai kin ji amma ina so ya zama sirri a tsakaninmu."