← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 40

Sashe 31

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce." To kai ma sai ka kiyaye abinda zai 'bata mini rai, ai ka dauki alkawari ni ma na d'auka. Kuma da kake cewa wasiyyar auran Hajiya Maryam aka bar maka ai ka jima kana yi mini maganarta tare da sha'awar abinda take yi wa mijinta."
Sai ya zuba mini ido da yanayi na mamaki a fuskarsa ya furta." Kada shashanci ya sanya ki sauka daga kan abinda muke tattaunawa Amina, in banda rashin hankali daga kawai na tausaya musu ita da mijinta a lokacin da yake halin ciwo sai ki canza mini magana, wato idan na fahimceki kina so ki ce da ni tun abokina yana raye nake sha'awar auranta ko ba haka ba ne."
'Dauke kaina na yi tare da d'an zumbura baki na ce." Na ga ai itama bazawarar ce mai yasa ba ka wani shiga damuwa ba, tana fita daga takaba fa ka yi gaggawar auranta, ai ko ni ban fad'i ba haka duniya za ta sanya ayar tambaya a kanka."
Fashewa ya yi da dariya yana kallona yana yi ya ce." Mijinta da ya rasu shine ya rubuta hakan a wasiyyar da ya bari, cewa daga zarar ta fita daga takaba kada na ja lokaci a daura auren. Idan ba ki yarda ba zan nuna miki takardar idan mun je gida. Sai magana ta gaba kuma Amina ai ba ni na ga Hajiya Maryam na ce ina so ba, sannan me zai sanya ni na tsananta kishi a kanta bayan nasan abokina ne ya aureta shi kadai ya yi tarayya da ita. Ba ki son sai da so ake kishi ba ne."
"To ai duk da haka itama 'yar kasuwa ce har fita take yi kasashen waje ta yi kwana da kwanaki ta dawo mai yasa duk hakan bai dame ka ba, idan adalci ne itama sai ka hana ta fita waje sarin kaya."
Sai ya shiga girgiza kansa yana fad'in." A, a, akan me zai hana ta neman kudinta bayan a haka ta ginu, kin san yawan mutanan da suke ci da sha'a a 'karkashinta kuwa, maganar fita zuwa wata kasa wannan dama dole ta bari tunda girma ya fara hawa kanta yaranta sun fara tasawa sai ta wakiltasu, shi ma abokina yarda da cewa ba zata ci amanarsa ba ya sanya ya bata goyon bayan fad'ada sana'arta, kuma ke ma da ki ke yin wannan maganar ai ban hana ki kasuwancinki ba ko ba haka ba ne?"
"Ni kenan kana kokwanto a kaina shiyasa kake takura mini da zargi har da Hamusu ka dinga tuhuma har da su Allah Ya isa, ka dinga bin shafukana na intarnat kana yi mini binceka duk wani abu da na dora da zummar talla idan bai yi maka ba sai ka sanya a sauke mini, ta karfi sai da ka ruguza mini kasuwancina na media."
Numfasawa ya yi kafin ya ce." Neman rigima ne kawai irin naki Amina, abu ne a zahiri gashinan kasuwancinki dana Hajiya Maryam ya sha bam-bam, ita bata fitowa ta tallata kanta da sunan kasuwanci tunda na aureta nake bin abubuwan da take gudanarwa sannu a hankali ban hangi wani abin assha ba wanda zai janyo mana zubewar mutunci.
Ke kuma dake da kayan tallan ki ke tallatawa duniya ya ba zan d'auki mataki ba. Ko ba ni da ido da neman rahoto daga jaridu ai ina kishin kaina ba zan lamunci irin wannan business din ba, idan ba ki manta ba farko auranmu na gaya miki ki bi duk hanyoyi na halak da za su kawo miki kudi amma kada ki bi hanyar da zata janyo mini zubewar mutunci."
Shiru kawai na yi masa domin har yanzu ban gamsu da bayaninsa ba sai nake ganin kawai yana tsara ni ne saboda ban kai karfin matarsa ba. Ita ai babbar yar kasuwace babu buk'atar da ta bi irin hanyar da sauran k'ananun 'yan kasuwa ke bi domin su kafu da kiran kostoma ta riga ta kafu ta tsaya da kafafunta.
Ganin na yi shiru ban sake cewa komai ba sai ya ce." Ni da za ki bi shawarata ma ki ajiye komai ki kama ni ki ri'ke da kyau, ni kuma duk bayan shekara daya ko biyu idan Allah Ya tsawaita mana nisan kwana na dinga baki ajiya mai girma kina haife mini. Sai ni kuma na cigaba da nema muku dukiyar tare dake da abinda za mu haifa."
Kallonsa kawai nake yi na rasa ma abinda zan ce. Wai duk shekara daya sai kace wata kaza yanzu da shekaru suka fara tura mini ai Allah na tuba ko zan k'ara wata haihuwar bai fi uku zuwa hud'u ba idan ma Allah Ya 'kaddara. Shiru na yi masa ban iya cewa dashi komai ba saboda Ina yin fad'in wata maganar akan maganarsa ya canza mini tawa.
Ya kai hannunsa kirjina tare da fad'in." Wannan na ga ya k'ara girma, na shiga tsananin u'kuba na rashinsu Amina."
Maganar ta ba ni dariya amma ban yi ba kawai na zuba masa ido yana matsa mini kirji dake cikin riga. Cikin zuciyata na ce dama ai dole ka shiga ukuba tunda ka saba lugudarsu yadda ranka yake so, gashi amaryartaka ba ta dasu. Hauwa da nata suka bunkasa dalilin ciki tana can wata uwa duniya ashe abin maleji ne.
Ganin ban hana shi abinda yake yi ba ya sanya ya janyo kafafuna kusa da shi ya fara kicikicin kwantar da ni a kasan kafet din da muke zaune. Na cire hannunsa tare da saurin tashi tsaye. Sai shi ma ya tashi da wani irin yanayi na tsantsar fitina ya kashe hasken d'akin ya riko hannuna muka nufi katon gadon da yake girke a d'akin. Ban hana shi tattabani ba sai da lamarin ya yi nisa tukkuna na ce masa ba ni da tsarki. Nan na ga gigicewa har da su rawar murya wai ban yi masa adalci ba. Na yi shiru Ina kallonsa yana ta abubuwa kamar wanda ya rasa hankalinsa yana fad'in duk ma yadda zan yi sai na nemi hanyar da zan biya masa buk'ata lallai ba zai iya ha'kuri a wannan dare ba.
Na'ki rungumarsa na kyaleshi kawai amma sa'kon ya fara shigata daurewa kawai nake yi ina ta mutsu-mutsu! Tabbas na so na daure zuciyata da zummar ja masa rai, amma ina lamarin ya fi 'karfina ban ma san lokacin da na talfeshi a ki'dime har na so na fi shi za'kewa da kansa ya gane abinda na fad'a ba haka ba ne. Sai jakan ya k'ara sanya shi sakankancewa yana buga sambatu da nishin kamar wanda ransa yake daf da barin gangar jikinsa.
[9/28, 7:54 PM] Aunty B: 96
Yadda muka wayi gari cikin walwala da farinciki shine abinda ya kara tabbatar mini da cewa ba a shiga tsakanin mace da mijinta domin kuwa wanda ya shiga tabbas watarana shine zai ji kunya mussaman idan ya aikata abinda zai sanya jin kunyar gangan. Misali da ba dan Baban Saude ya yi amfani da ilimi da k'arewa wajan kawo sasanci da daidaito a tsakaninmu ba wata'kila da ya yi amfani da 'daya sigar to da ba wannan maganar ake yi ba. To shi ma sai a ka ci sa'a ya yi amfani da hikima wajan ganin ya isar da sa'kon da yake ya isar din wanda shi ma daga 'bangaran Yallabai din na fahimci abin ya yi masa ciwo sosai, kuma kamar yadda ya fad'a din na tabbatar da baya sona da buk'atar cigaba da zama da ni ba zai ta'ba bibiyata da nufin kome da sulhu ba, duk da Baban Saude bai yi amfani da tsautsauran kalamai ba, amma yadda na fahimta ya ji haushi kawai ya danne ne domin samun a zauna lafiya.Tabbas idan hakane kuwa Ina da ya'kinin zai gyara anan gaba tunda na lura ya tsani a kai shi k'ara don ko lokacin da na ta'ba Kai shi 'kararsa wurin Hajja akan lamarin Hamusu fushi ya yi da ni mai tsanani idan ban manta ba ya dinga gaba da ni sai da kyar ya sauko.

Dama tun asubahi ya ce na yi duk shirye-shiryen da zan yi jirgin karfe takwas za mu bi zuwa abuja kafin lokacin ma ya cika mun fito ni dashi a kintse Sukairaju dama tuntuni ya sanya mana kayanmu a mota.
Kafin mu isa airport din Anti Yagana ta kira ni a waya kamar yadda ta fada na ce mata ai mun riga ma mun fito muna mota zuwa filin jirgi. Sai ta ce na had'ata da shi. Ba tare da na ce komai ba na mik'a wayar tare da gaya masa anti Yagana ce take so ta yi magana dashi.
Ya kar'ba a nutse suka gaisa sai kawai ta fara yi masa godiya har ina jin yadda muryarta take rawa godiya sosai na abin alherin da ya yi wa su Dada da Baban Saude. Sai kuma alkawarin kyautar motar da ya yi wa maigidanta. Da kulawa sosai ya nuna mata cewa ta daina yi masa godiya akan abinda ya yi, ai duka an riga an zama daya don haka ba abin mamaki da godiya ba ne akan duk irin abinda zai yi mana. Ta cigaba dai da godiya dai har tana cewa dashi ya kara da hakuri dangane da zamantakewa ta dashi in sha Allahu wani abu ba zai sake faruwa ba. Ya ce mata babu komai shi ma a b'angaransa magana ta wuce hakan ba zata sake faruwa ba.
Chapter 31 · 0% Book details