← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 40

Sashe 7

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Kwanaki biyar da dawowarmu na fara mantawa da abinda ya faru amma dai duk da haka sai dana sanar da anti Yagana irin wulakancin da nasha na kuma tabbatar mata cewa ni da kara shiga danginsu har abada duk abinda zai yi sai dai ya yi amma ba ni ba kusantar abinda ya shafi Hauwa.
Ban kira shi ba kamar yadda bai kira ni ba kuma nasan yana da tabbacin mun dawo indai gaba ce ya yi ga fili nan ga mai maidoki sai mu zuba.
Sosai na mayar da hankalina wurin addu'a tunda na fahimci kamar zama da auransa ba mai karewa ba ne, ina addu'a sosai tare da kula da kaina na kuma yi kokarin cire damuwarsa a raina hankalina ya karkata wajan cigaba da hurdodina a cikin gidan dai tunda ba na fita amma Hamusu yakan zo sa'i da lokaci mu yi lissafi haka zalika ma Usaini yana zuwa don shi kusan kullum ma muna tare. Yanzu har kaya nake bawa Sahura cikin sau'kin farashi tana tafiya dasu wurin aiki itama ta d'ora nata akai ta samu. Haka zalika ma Usaini yana turawa Maman bokola kaya can garinsu akan sari yadda zata samu nata
A cikin wannan yanayin lokacin zuwa ziyara makarantarsu Kamalu ya yi.
A wancan karon ban samu zuwa ba sai Hamusu ne ya je tare da Baba Inuwa kanin mahaifinsu da yake can wani kauye da iyalinsa a k'aramar hukumar Sumaila can ya je ya d'aukeshi suka je na dai tura masa kudi a lokacin da za su tafi na ce ya yi masa sayayya sosai sannan ya bashi wasu ya rike a hannunsa ko zai bukaci wani abu.
Wannan karon kam tare za mu tafi domin yaron yana raina sosai kawai ina dannewa ne don ganin yadda Allah ya canza masa rayuwa a duk lokacin dana kalli hotonsa ina jin dadin ganinsa cikin nutsuwa don hotonsa ne akan fuskar wayata yana ri'ke da al'kur'ani mai 'kirar warshu yana ta karatu wata'kila ma bai san lokacin da aka yi hoton ba. Wani malami ne daga cikin malaman makarantar ya turowa Hamusu hoton ta whasap a tun farkon kaishi makarantar yanzu kuwa nasan ya k'ara girma sosai tunda abincin da suke ci hatsi ne (datsa) kuma suna noma suna aikin karfi ana koya musu sana'oin da koda an sallamesu zasu dogara da kansu.
[9/17, 9:38 AM] Aunty B: 84
Cikin rashin sanin yadda zan yi na sanar dashi maganar zuwa ziyarar Kamalu na kira Hamusu a waya na ce ya kira shi ya gaya masa tafiyar tunda dama farkon zuwanmu ya ce da Hamusu duk lokacin da za a je duba yaron a sanar da shi. Da wannan na samu mafaka Hamusu ya ce mini ai tun shekaran jiya suka yi waya ya sanar dashi ya kuma tura masa kudi har dubu dari wai ya yi kudin mota alheri kuma dama sa'i da lokaci yana taimakawa makarantar.
Babu yadda zanyi dole na ajiye nawa girman kan na nemi izini muddin kuwa Ina son zaman lafiya ba zai yiwu ace na je ba tare da saninsa ba.
Ga mamakina kiran farko ya daga kamar dama yana tsammanin kiran nawa.
Na dan yi shiru Ina dawurwura kafin daga bisani na daure na fara gaishe ya amsa a nutse kafin ya furta." Ya aka yi?"
Na ji wani iri da tambayar da ya yi mini ta ya akayi kawai sai na danne na ce." Lokacin ziyarar Kamalu ne ya yi kasan wancan karon ban samu damar zuwa ba to shine na ce yanzu bari na sanar da kai Hamusu ma ya ce kun yi waya shekaran jiya ko."
"E, ya gaya mini zasu tafi tare da kanin mahaifinsu wanda suka je tare dashi a wancan lokacin don haka zuwanki bashi da wani amfani tunda za su je so ban baki izini ba gaskiya.''
Ya fadi maganar cike da kwarin gwiwa da kuma nuna isa da bada umarni.
Na ce." To shikkenan." Kawai na kashe wayar na nemi waje na zauna kan kujera da mamaki a tare da ni, gabad'aya ma rasa wane irin tunani zan yi akan wannan zaman da muke yi ni da shi shikkenan saboda wani dalili sai ya 'kullace ni akan son rai.
Rigima ce dai yake so mu yi domin ba yadda za a yi a ce ya dinga take mini hakki da gangan! na tabbata da shi ya haifi yaron ai ba zai hana ni zuwa ganinsa ba, dama yana nema hanyar da zai 'bata mini rai sai gashi ya samu dama.
Yini na yi cikin takaici da b'akinciki ga Yusura bata nan ta je gida suna da biki can dangin babanta sai kad'aicin ya yi mini yawa sai da na yi kuka tukkuna na samu sasaauci kuncin da zuciyata take ciki. Na kira anti Yagana na gaya mata irin yankar k'aunar da mutumin nan yake yi mini a zahirance kowa ya ji abinda ya yi ya san bai kyauta mini ba. Ha'kuri dai ta bani ta ce mini na kyaleshi duk abinda zai yi akan yaran domin Ina iya yin magana ya juyata tunda kiris yake jira ya ce don bashi ya haifesu ba ne zan nuna masa iko kiri kiri ya raba ni da Yusi duk sha'kuwar da take tsakanina da yaron nan ko nema na baya yi a waya haka ina ji Ina gani na ha'kuri babu damar da zan yi magana. Kuma Bai zama lallai na gayawa Hajja ta goyi da bayana ba tunda yanzu bata yayina dole na ha'kura don babu yadda zan yi Hamusu sukaje suka dawo lafiya lau da albishirin Kamalu ya sauke al'kur'ani maigirma yanzu yana kan yin hadda ya kuma fara rubuta shi.
Farincikin hakan ya matar da ni takaicin da nake ciki domin yadda Hamusu yake yi mini bayani Kamalu ya zama gwani sosai domin suna zaune a wurinsa ba tare da ya d'auki al'kur'ani ba ya karance musu izifi ashirin daga sama.
Muka yi waya da Gwaggo a washe garin ranar wadda itama take cike da farinciki na ce mata ranar juma'a jibi kenan a yi abinci mai kyau a yi sadaka dashi duk abinda ake bukata na umarci Hamusu da ya fitar da kudin da za su wadata Allah Ya amsa mana addu'a ya kuma shiryi yaranmu.

**
Bayan sati daya Yusura ta dawo amma tare suke da wata dattijiwar mata wadda na sanya Sahura ta nemo mini domin taya ni aiki dukda aikin gidan bashi da yawa ni kadai ma zan iya yin abina to amma nasan zaman matar tare da ni zai d'ebe mini kewa dalili ko ma'kota bai ba ni damar hurd'a dasu ba yadda ya sanya masu tsaro a gidan na tabbatar da cewa ya yi hakane domin su sanya masa Ido akan duk wani motsina shiyasa tun bayan dawowarmu daga Bauchi babu inda na je gashi yau kwanaki arba'in da biyu kenan da tarewata a gidan ina kuma lissafi kwanakin ya yi daidai da lokacin da ya k'ulla gaba da ni. Watanni uku kacal na d'iba masa idan bai ajiye gabar ba sai dai ya ji labarin na bar gidan domin ba yadda za a yi ace zama ya yi kyau ta irin wannan sigar manya za su shiga maganar a bawa mai lefi lefinsa mai gaskiya a bashi gaskiyarsa.
Baba Tabawa sunan mai aikin da Sahura ta samo bata ta'ba haihuwa ba har ta fara manyanta mijinta ya rasu ya bar mata gadon gidan da take ciki a yanzu. Yadda Sahura take yi mini bayani tun bayan rasuwar mijinta take fadi tashi don wataran ma takan kwana da yunwa saboda rashin abinda zata ci da rashin haihuwa don da ta haihu ko daya ne zata samu mai tallafarta wataran har gefe titi take bi ta yi bara da daddare ankara da hakan ya sanyan a unguwar aka samu wani mutum ya sanya mata kwano yana bata abinci

Baba tabawa ta kwanta mini a rai dalili kuwa shine macace mai nutsuwa addini da sanin ya kamata a d'an zaman da nayi da ita na 'yan kwanaki na karanceta tsaf tana da gudun duniya kuma tana da zuciyar neman na kanta dalilin ma da ya sanya kenan lokaci guda ta amince da bukatar Sahura a lokacin da ta je gidanta ta sameta da maganar.
Sai zamanta ya rage mini kad'aici mussaman idan Yusura ta tafi islamiyyar dana sanyata anan bakin titi domin ta cigaba da dora haddarta kasancewar dama ta yi saukar al'kur'ani wattanin shida da suka wuce wanda ya yi daidai da lokacin da ta zana jarrabawar fita daga secondary da kaina na yi tunanin sanyata a makarantar saboda zaman a haka bashi da amfani zata sake d'aukar darrusa masu muhimmanci kafin lokacin auranta tunda makarantar ba wai al'kur'ani kawai suke koyarwa ba har da sauran littafain na addini za ta kara sanin tsarki da hukunce-hukuncensu.

Ranar da Sahura ta zo yini muka yi muna magana daya har dai na gaji na yi mata shiru domin kuwa ba zan ta'ba yin abinda take so ba don ban ga abinda na yi ba ai na d'auka sai mutum ya yi lefi tukkuna zai ta bibiyar wanda ya yi wa domin ya yafe masa.
Ita kanta tasan maganata akan daidai take ba zai yiwu ace sun mori juna sun jiyar da kansu dadi ciki ya samu ace ni kuma dake gefe na je na yi musu wahala ba, ai ba yarinya ba ce balle ace kuma ita din menene bata sani ba tunda malamar asibiti ce duk wanda zai zage ni ya dad'e bai yi ba abu ne mai mutukar wahala wata mace ta aminta da hakan.
Ita Sahura wai kada mutane su yi mini wata fassara ko a juya maganar ace ina yi mata b'akinciki don ta samu cikin haihuwa wanda ni kuma wallahi babu wannan a cikin raina komawa ne kawai ba zan yi ba, ni ma a lokacin da na samu nawa haka nayi ta fama dalilin ma da ya sanya kenan nake d'agawa Hadiza kafa saboda wahalar da ta yi mini.
Chapter 7 · 0% Book details