← Book details Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata biyu da dawowo ta ina lissafin watannin cikin dake jikina wata uku da kwanaki kenan wannan karon laulayi nake yi sosai domin kuwa ba komai nake iya ci ba na fi kauri dai a b'angaran manja da yaji wainar fulawa ko d'anwake da manja ko d'anmalele. Sai ko kayan gona wannan kuma Hamusu nake sanyawa ya sayo mini duk bayan kwana uku ya kawo mini hidimar soya waina da danmalele kuwa Yusura ce ke yi mini. Duk cika da kasaitata a ko'ina sai da na rairaye saboda azabar laulayi ban fita na je ko'ina ba balle a gane halin da nake ciki itama Sahura tun zuwan da ta yi bata sake zuwa ba sai dai mu yi waya. Anti Yagana ma waya muke yi kuma ban gaya mata komai ba. Ta ce mini dai karshen shekaran nan za ta zo amma ita kad'ai ba tare da yaran ba saboda makaranta. Muka tsaya akan zuwanta a karshen shekaran nan da muke ciki to sai dai kana taka Allah Ya na tasa domin kuwa rikicin da ya ritsa da Hadiza shine abinda ya tilasta mata zuwa ba tare da shiri ba. Hadiza garin neman duniya da son lallai sai ta yi kudi bayan tafiye-tafiyen da take yi zuwa dubai sarin kaya ashe ta had'a kai da wata mata da suka hadu a can dubai din itama 'yar kasuwa ce mazauniyar Na'ibawa anan gidanta yake kuma bazawara ce babba da yaranta ta ribaci Hadiza tare da kwaid'ata mata kudin da zata samu idan ta shiga 'kungiyarsu ta shan jini. Ba tare da dogon nazari da tunani ba tunda dama babu wani sanin addini a tare da ita ta fantasma kanta a harkar da babu fita muddin an shigeta kuma sharad'in shine dole sai mutum ya bada jinin dan adam mutum guda. Suka had'a baki da ita Hajiya Alili suka saci wani almajiri suka mika shi ga kungiyar kamar yadda suka buk'ata da da farko cewa suka yi da ita sai ta bada d'anta na cikinta ta ce musu ai bata taba haihuwa ba shine suka buk'ace ta cikin kwanaki biyu kacal ta kawo musu matashin yaro wanda bai balaga ba. Matsanancin tashin hankali muka shiga gabad'ayanmu domin lamarin da ya faru sai yake nema ya shafi zuri'armu gabad'aya mutane suna ta ririta maganar tare da 'kir'kiro k'arya da gaskiya har da masu cewa dama sun jima suna zargin alhalinmu ko maita ko karuwanci ashe 'yan mafiya ne, wasu kuma na cewa gidan namu dama ai ya yi 'kaurin suna yara tun suna k'ananu suke sace sace. Hadiza ta zama kamar zautacciya domin kuwa ita da mahaukaciya marabarsu kalilan ne zafin addu'a da irin saukar karatun al'kur'ani da ake yi akan 'batan yaron ya sanya da bakinta ta fad'i ta yi kisan kai domin kuwa yaron tuntuni an shanye jininsa hakkin rai da rashin sabo ya sanya nutsuwa ta yi kaura daga jikinta. Yadda bincike ya nuna ita Hajiya Alili tunda ta ji maganar ta fasu a gari ta yi 'batan dabo aka nemata a ka rasa a garin. 'Yan unguwa suka cinnawa gidanta wuta ita kuma Hadiza muna ji muna gani mota guda da 'yansanda suka tafi da ita. Tashin hankalin da ya assasawa Babanmu fad'uwa kenan ranga ranga rai a hannun Allah muka kai shi asibitin nuna koke-koke don wallahi ni tsananin damuwa da fargaba ya sanya na manta halin da nake ciki duk wasu lalure laluran da nake yi a tsaitsaye nemansu na yi ba rasa muka dinga zurga da kai kawo daga gidanmu zuwa asibiti zuwa ofishin 'yansanda. Ni da anti Yagana mune manya kuma mune masu rufin asiri a ciki. Itama Ummansu Hadiza sun ri'ke dukiya a da can domin mahafinsu tsohon mai kudi to amma yanzu babu domin duk rabinsu sun karye babu abin sukan rasa ma abinda za su sarrafa a cikinsu. Ga masifar da take ciki bata fita ba wata ta kara kutsowa Alajiji d'anta na fari da ta haifa a wani gidan ya je ya damfari wani makudan kudi asirinsa ya tuno yana hannun hukuma suna bincike akansa domin dama tsohon mai lefi ne ya jima yana harkar yahoo 419 shine kiran da ta yi Alhaji Tajo a kwanakin baya ta ke gaya masa ya taimaka musu. Son zuciya ɓacinta kuma duk wanda ya sayi rariya tabbas ya san sai ta zubda ruwa idan da godiyar Allah iya jarin da Alhaji Tajo ya bata ya isheta ta juya ta kuma ri'ke kanta har ta kula da wasu to amma ta sanya son zuciya da son dole sai ta yi kudi ta kowace hanya ga abinda ya janyo mata nan. Anti Yagana a gidana ta sauka wannan dalilin ya sanya muke zurga zurgar tare domin ba zan ta'ba bari ta yi ita kadai ba. Hankalinmu bai kwanta ba har sai da muka ga jikin Babanmu ya dawo yadda yake tukkuna muka samu nutsuwar tattauna yadda za a kamo bakin zaran matsalar da Hadiza ta rikitowa kanta. Lamari ne gagarimi wanda duk wanda ya ji abinda ta aikata ya jajanta mata don gaskiya da wahala idan hukuncin kisa bai rataya a wuyanta ba gashi an yi an yi da ita ta fad'i wurin da mutanan da suka sanyata suke ta'ki fad'a duk kuwa da azabar wahalar da take sha a hannun hukuma. Ranar da muka je da dubata alfarma kawai suka yi mana dalilin ina auran Babban mutum amma da babu wani uzuri da zai sanya su bar mu shiga wajenta. Kuka wiwi na dinga yi ganinta a jigace ta dimauce jikinta duk shacin duka abinka da farar fata ta ki'dime sosai tana ta zantuka marasa tushe anti Yagana ce mai dauriya bata koka ba amma idonta kadai ya tabbatar mini da cewa kukan zucci take yi. Fati Kam fad'uwa ta yi a wurin aljanu suka bugeta Hassana da Usaina suka fita da ita can waje domin wurin da muke babu iska. Da muka fito anti Yagana ta gargadi su Hassana akan kada wadda ta kuskura ta gayawa Ummansu halin da muka tsinci Hadiza su nemi hanyar da zasu kwantar mata da hankali koda kuwa ta 'karya ce don za ta iya shiga mummunan yanayi muddin ta ji halin da Hadizan take ciki. A daran aka sallami Babanmu daga asibiti a waya na kira Ayuba sabon direba na ce dashi ya zo ya d'auke mu a mota gabad'aya domin a galabaice nake kwarai da gaske gajiya da jiri da ciwon mara da kafafu ban kuma kawo komai a raina face wahala da fargaba tare da kai da kawon da na yi. Muna komawa gida ni da anti Yagana na zube a tsakiyar d'akina domin wani mashahurin ciwon mara ne ya turnike na dinga murkususu ina ri'ke cikina anti Yagana hankalinta ya tashi sosai ta kira Baba Tabawa tana cewa mu je asibiti na girgiza mata cikin halin da nake ciki na fara yun'kurin amai amma bai fito ba kakari na ke yi ban amayar da komai ba sai can na ji kamar an fasa ruwan pure water a zanina jini mai yawa ya fara gudana har ya fara naso a kafet din daidai inda anti Yagana ta ajiye kafarta. Cikin fitar hayyaci na furta." Anti Yagana 'bari zan yi jini ne yake zuba." A ki'dime ta tsuguna gabana ta daga cinyata jini sharkaf ya jika mini zani sai ta fashe da kuka tana fad'in." Ciki ne dake dama Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Ta kwalawa Yusura kira tare da ce mata ta gayawa Ayuba ya fito da mota za mu je asibiti. dishi dishi na fara gani domin kuwa kafin faruwar hakan na yi masifar tsorata da irin mahaukacin jinin da nake zubarwa wannan shine ya assasa d'aukewar ji da ganina na wucin gadi. [9/22, 9:50 AM] Aunty B: 89 To cikin dai ya zube a lokacin da ban yi tsammanin fitarsa ba. Wahala kuma na ci ba 'yar karama ba domin kuwa biyu ne ashe na farkon ya fita ba mu jima da zuwa asibitin ba. Na biyu sai da aka kai ga yin wankin ciki tukkuna aka yo waje dashi. Jini kam na zubar ba kad'an ba aka dibi na anti Yagana aka sanya mini aka nemo leda daya a waje a kara. Tun a daran anti Yagana suka yi waya da maigidan ta sanar dashi halin da ake ciki. Ina jinshi lokacin da yake gaya mata ai ban ta'ba sanar dashi ina da juna biyu ba har wata uku da sati uku. Ya ce mata in sha Allahu gobe mu tsammaci zuwansa. Da safe Baba Tabawa da Yusura suka tafi gida domin yin abinci. Anti Yagana tana tare da ni a asibitin motsi kad'an sai ta dube ni ta share kwalla. Jikina ya yi sanyi na fara zargin ko likitan da yake tsaye a kaina ya yi mata bayanin wani abu ne. Ni babbar fargabata ma zuwansa asibitin nan domin kuwa gabad'aya na yi sanyi da lamarin dalili na riga na san likitocin asibitin Malam Aminu suna da gogewa ta fannin aikinsu dole zasu yi binciken abinda ya asassa fitar cikin nawa. Jiki babu wani kuzari na yi wanka da ruwan da ta had'a mini a bandakin dake cikin d'akin da nake kwance da yake waje na mussaman suka ajiye ni a asibitin dalili tun shigowarmu security suka shaida fuskata duk kuwa da yanayin da nake ciki na ciwo. Na shirya cikin doguwar riga na kintsa jikina sosai cikin rashin kuzari da k'warin gwiwa gabad'aya rashin walwala da sukuninta ya fi damuna sosai akan fitar cikin daga jikina. Likitan da yake duba ni ya sake shigowa muka gaisa ya yi mini tambayoyi na ce masa jiri ne ya fi damuna sai rashin jin dadin jikina. Magunguña ya had'a mini tare da ba ni shawarwari da yadda zan yi amfani da maganin ya ce mini sun yi waya da Yallabai din ya ce ya iso garin amma yana danbatta wurin mamanshi zai jira zuwansa asibitin kafin ya tafi gida tunda dama aikin dare yake da shi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba anti Yagana ta yi masa godiya kafin ya fita. Ina kallonta ta je ta yi wanka ta kimtsa jikinta ta sake zama a gefana ba ta da niyyar cin wani abu bayan gashinan Baba Tabawa ta yi abinci
Chapter 15 · 0% Book details