Sashe 21
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
To kamar yadda yake a rubuce a katin d'aurin auran da ya d'ora a status d'insa ranar juma'ar dai aka daura auran bayan an yi sallah. Hajiya Maryam Abubakar Sabi'u jos tsohuwar matar amininshi Alhaji Amadu yau ta zama matarsa.
Cikin kunci na 'karasa yinina cikin damuwa da ciwon kai wanda ya dabaibayeni a ranar na dinga k'okarin ganin na hana kaina kuka amma na kasa jimirin yin haka rufe kaina na yi a d'aki na ci kuka na 'koshi haka kawai nake jin wani irin mugun haushi da kishin matar a cikin zuciyata na tabbatar da cewa yana sonta yana kuma tausayinta tunda har ya iya auranta ba tare da kai da kawo ba. Itama kuma tana sonsa domin auransa zai zame mata rufin asiri domin cigaba da hurd'odinta kuma ina da tabbacin cewa babu abinda zai hanata aiwatarwa na abinda ya shafi abinda take yi tun kafin rasuwar tsohon mijinta. Hankalinsa zai fi kwanciya da ita tunda ai ita ya san wanda ta aura abokinsa ne kuma shi kad'ai ya yi tarayya da ita, ni kuwa fa maza biyu na aura a baya na haihu da d'aya.
'Dayan ban haihu dashi ba, ina ganin wannan dalilin shi ya sanya shi cire shakku a kanta har ya yi gaggawar auranta jim kad'an bayan fitarta daga takaba.
Daddare status din ya k'ara d'orawa a karo na biyu na wannan lokacin hutonan d'aurin auran ne ya d'ora yana cike da walwala da annashuwa tare da manyan mutane abokanshi da suka samu damar halarta domin taya shi murna. Hotonan na dinga bi daya bayan daya ina dubawa sun kai kusan arba'in kowane kuma yana cike da annushuwa kamar wanda ya yi auren fari. Wasu hawaye masu zafi suka k'wace daga idanuwana duk ko'karin dannarsu da nake yi. Zuciyata ta dinga harbawa da k'arfi azababben kishin da nake yi a kansa ya motsa mini na dinga jin kirjiina yana toyewa. hawayen idanuwana na sake tsananta ai da farko na d'auka zan iya jurewa ashe ba haka ba ne soyayyarsa ta riga ta gama mamayata na tabbatar da duk wani yun'kuri da zan yi akan kwatar 'yancina idan lamarinsa ya bijiro mini sai na koka da hawaye domin kuwa abinda nake ji a can kasan zuciyata a halin yanzu Allah ne kadai ya san shi. Na ji radad'i da kishi ainun a lokacin da zai auri Hauwa haka zalika ma ina jin ciwo da b'akinciki a duk lokacin da ya furta Marigayiya Samira matarshi ta farko ita ce first love dinshi. A wasu lukutan na kwana na yini ban kula shi ba saboda haushi. Amma a yanzu sai na ganin abinda na ji na bakincikin auransa da Maryam ya shallake na baya. Gabad'aya ma na shiga dana sanin duba status din wanda na tabbatar da gayya ya d'ora domin ya cusa mini b'akinciki. Zamewa na yi na kwanta ina shar'bar kuka na tausayin kaina gefe guda kuma ina ta tunano irin muguwar soyayyar da yake gwada mini a baya kamar zautacce ashe akwai ranar da za ta zo da zan zama banza mara galihu a wurinsa.
[9/24, 7:43 PM] Aunty B: 92
Wannan kukan da nake yi ya zama me mini dole ne na yi shi domin yinsa kad'ai zai sanya mini jin sasaauci a zuciyata. Amma kuma tilas ne fa na yi wani abu akan wannan lamarin namu domin sanin matsayin da nake.
Haka dai na yi hakuri na danni zuciyata da 'karfin addu'ar da na dimanta na d'an ji sa'ida a cikin raina, amma dai duk da haka idan lamarin ya fado mini a raina na kan shiga wani yanayi mara dad'i.
Na cigaba da kasancewa cikin tunani da nazarin yadda zan b'ullowa alm'arin. Kai tsaye shawarar da na yanke a raina itace zan nufi maiduguri gidan Baban Saude nasan shi kad'ai ne zai dube ni ya kuma fahimci halin da nake ciki. Nasan kuma zai ri'ke ni kamar 'yar cikinsa a wannan karon ba zan ce zan yi zaman kaina ba balle a canza mini manufa a iya tunanin da na yi shine gidan Baban Sauden dai shine marufar asirina babu wanda zai zarge ni da wata niyya na ke ko'karin kashe auran. Ba zan gayawa anti Yagana komai ba itama sai dai kawai ta ji labarin ina garin. Kuma na tabbatar da cewa babu wanda zai zo ya ce zai tursasani akan abinda ba na so muddin na ci sa'a Baban Saude ya kar'bi kukana ina da ya'kinin zai iya yin gaba da gaba da Alhaji Tajon sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Ina ta shirye-shiryen tafiya ban gayawa kowa ba shawarar da na yanke shine Yusura za ta koma hannun mamanta itama baba Tabawa zan sallameta da alheri mai yawa, masu gadin gidan da Ayuba dama ba ni na ajiyesu ba. Ina shakkar Babanmu ya samu labari abinda na tabbatar da cewa ranshi zai b'aci matu'ka da gaske. Hakan ba zai sanya ni na janye ba domin kuwa Babanmu zuciyarsa ba irin ta kowa ba ce ba zai iya ta'buka komai ba ko da kuwa an zube magana an tabbatar da cewa ni ma ina da gaskiya ta wani gefan ana cutar da ni.
Sati uku da d'aurin auransa inda wa'adin rantsuwar da na yi akan rashin zuwansa ya kusa cika saura sati daya kenan wattanin bakwai da barinsa garin.
Hajiya Saratu ta kira ni a waya tana gaya mini Hajja babu lafiya har sun je da ita Egypt sun yi sati daya sun dawo gida amma jikin da sau'ki yanzu. Na ce mata wallahi ban sani ba da tun wuri na zo na dubata. Mamaki ta dinga yi wai saboda na ce mata ban sani ba, ganin kamar tana so ta fahimci wani abu ya sanya na yi mata sallama tare da bata tabbacin in sha Allahu Ayuba zai kawo ni gobe na dubata.
Kwana biyu a tsakani Ayuba ya kai ni gidan Hajja na dubata jiki da sauki alhamdulillahi ta warware don tana zaune ma ana ta hira, ni ma na saki jikina sosai domin ko da wasa ban nuna akwai wata matsala ba. Cikin hirar da muke yi ne na d'an fahimci wani abu ashe maigidan ya zo garin har ya yi kwanaki ya koma a cikin tsakankanin wannan lokacin bayan sun dawo daga Egypt .
Shiru na yi da suna maganarsa ban iya cewa komai ba domin kuwa ni ban san ma ya zo har ya tafi ba, amma can 'kasan zuciyata abin ya tsorata ni sosai ya kuma sanya mini shakku anya maganar Sahura bata tabbata ba kuwa ko dai da gaske ne matar nan Maryam da ya aura tana asiri tunda mijinta har ya mutu da ita kadai ya rayu.
Tunanina ne ya katse a lokacin da na ji Hajja tana maganar ai ya je can bauchi wurin Hauwa wadda take daf da haihuwa ko yau ko gobe domin kuwa sun yi waya da inna Uwani ta ce mata kwanansa biyu a can kafin ya tafi.
Jikina ya 'kara yin sanyi kwarai da aniya tabbas mutumin nan ya sake ni furta mini ne kawai bai yi ba saboda mugunta ya jingine ni a gefe d'aya.
Ina jin su suna ta hirar abinda ya shafe su, idan ta had'o da ni na sanya musu baki amma kuma zuciyata cike take da mamaki lamarin to sunce ya zo ya kwana amma me yasa basu fahimci cewar ba ma tare ba. Idan har ya zo din ai a gidana ya kamata ya sauka bayan ya duba mahaifiyartasa. Wani sashe na zuciyata ya ce mini tunda ki ka ga basu fahimci komai ba to wata'kila bai gaya musu wata matsala ba kuma ai yana da gidajen a garin da guesthouse bai zama lallai ya kwana a gidanki ba, idan ya yi musu sallama da zummar tafiya wurinki ai ba zasu fahimci komai ba."
Wannan hasashen na zuciyata shi ya zauna daram a k'wa'kwalwata. Wato abinda ya yi kenan har ya yi kwanakinsa anan din ya tafi bauci wurin matarsa ba su gane komai ba. Ganin haka ya sanya ni ma na cigaba da nuna fara'a da annashuwata ban yarda yanayina yayi sauyarwar da za su gane akwai matsala ba. Da suna hirar Hajiya Maryam amaryarsa ni ma na sanya bakina Ina biye musu domin kuwa ga dukkanin alamu ta samu karbuwa a wurin Hajja tana sonta don sai fad'in alherinta take yi. Tabbas matar ta san takan zama tare da duniyanci domin kuwa koda bata asiri zai wahala duk wanda ya kusanceta ya ga laifinta domin ta iya mu'amula da kyautatawa. Gashi dai 'kiri-'kiri sun mayar da ni sauna ita da shi sun kar'be mini yarona duk tsananin sha'kuwar da take tsakanina da Yusi idan mun had'u sai na zama bak'uwa a wurinsa. Yadda ma za a yi ya dawo hannuna a yanzu shine abinda ya fi daga mini hankali da sanya mini fargaba domin kuwa yadda ya d'aukaki mutumin nan kamar shine wanda ya haife shi. Haka zalika ma ta b'angaransa shi Yallabai din ya sanya yaron a cikin ransa wanda yake nuna kamar ya ma fi ni iko da shi.
Yini na yi sai yamma na yi shirin tafiya Allah sarki Hajja ta had'a mini Turaruka masu tsada da k'amshi na jiki da kuma na wuta dana tsinke.
Zuciyata ta tsinke k'warai da gaske domin kuwa na tabbatar da cewa ta ji labarin bada'kalar da take faruwa hankalinta zai tashi wanda hakan ka iya yin barazana da lafiyarta. Na kuma gane dalilin da ya sanya shi kansa yake 'boyewa saboda tabbatuwar kwanciyar hankalinta tunda ni din ta gaban goshinta ce in banda yanzu da magauta suka yi yawa amma zahiri Hajja tana sona k'warai, kuma tana son zamana da d'anta.