Sashe 23
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
D'aki guda ya sanya a ka gyara mini tsaf har da katifa da sabon mashinfid'i da labuleye masu kyau d'akin yana ta k'amshin turaran wuta. Mama uwarginshi da kanta ta shigo ta kawo mini abinci a jere a tire na silba muka sake gaisawa bayan wadda muka yi tunda kafin na shiga masaukina sai da na shiga duka d'akunansu muka gaisa. Ta dinga tambayata mutanan gidanmu da yaran na ce mata duk kowa lafiya lau.
Sai da nayi wanka tukkuna na d'an warware na ji 'kwarin jikina na zauna a nutse na ci abinci na 'koshi na fita da tiran ina sake yi musu godiya na koma d'akin na zauna tare da fito da wayata daga cikin jaka domin tun a cikin mota ban sake dubata ba. A mace take ban san dalilin da ya kasheta ba.
Minti biyar da kunna wayar kiran anti Yagana ya shigo. Cike da fad'uwar gaba da fargaba na d'aga nasa a kunnena cikin wani irin yanayi na yi sallama bata amsa mini ba na ji tana ce wa." Ya aka yi ki ka kashe wayarki Amina tun wajan la'asar nake kiranki sai a ce mini a kashe take."
A hankali na ce." Bacci na yini ina yi kuma tunda na sanyata a caji ban sake waiwayenta ba sai yanzu ina fatan kuna lafiya ina Fadila."
A takaice ta furta." Lafiya lau, mijinki ne ya kira ni yake tambayata wai kin zo gidana na ce a a wani abun ne ya faru a tsakaninku ne?"
Cike da takaici na ce." Babu abinda ya faru anti Yagana don girman Allah idan ya sake kiranki kada ki daga wayarsa."
"Akan wane dalili zai kira ni na'ki dagawa Amina, ki gaya mini menene yake faruwa domin yanayin da ya kira ni a d'azu ya tabbatar mini da cewa akwai abinda kuke b'oyewa ke da shi."
"Saki na ya yi."
Na tsinci kaina da gaya mata hakan.
Cikin rud'u da tashin hankali ta furta." Saki akan wane dalili, kina ina yanzu domin ya tabbatar mini da cewa tun safe ki ka fito daga gidanki direbanki Ayuba ne ya kira shi a waya ya gaya masa shine ni kuma ya kira ni yake tambayata."
Cikin dauriya na ce." Anti Yagana abinda nake so dake a wannan ga'bar da muke ci da mutumin nan don girman Allah ki cire kanki idan zai kira ki sau dubu ya tambayeki abinda ya shafe ni ki ce masa ba ki da k'arfi akan lamarin ya nemi manyana su yi magana."
Ta ce." To na ji, ko zan iya sanin abinda ya faru, sannan kuma ki gaya yanzu kina ina domin hankalina ya kwanta Amina sha'aninki yana nema ya fi karfina, don girman Allah ki fahimci kin girma fa kina dai kallon abinda ya samu Hadiza ko, mune manya a gidanmu ba mu da namiji babba dole mu zamu tallafi 'kannanmu da suke tasowa don Allah ki yi hakuri ki jure kamar yadda kowace mace take ha'kuri a d'akin mijinta ki zauna wannan ya zama mutuwa ce zata raba tsakaninku ki yi mana wannan alfarmar." Ta kare maganar cikin rawar murya.
Ina kuka na ce." Anti Yagana ya zan yi ne da rayuwata gabad'aya duniyar ta yi mini zafi a yanzu bana jin dad'inta. Duk yadda zan yi na yi kokarin ganin na zauna d'akina amma abin ya gagara, Allah Ya had'a ni da wani irin (Ba'aboren namiji) sunan littafin Binta Umar Abbale ku nema ku karanta ya yi mutukar dadi.
Tana kuka irin mai tafe da tsananin damuwa da takaici ta cigaba da cewa." Abubuwan da suka faru tsakanina da shi suna da yawa anti Yagana na gaji da b'oye miki na kuma gaji da zama da mutumin nan so nake yi kawai ya sauwake mini na huta idan ba so yake yi zuciyata ta buga ba."
A sanyaye ta ce." Dalili dame bakincikinsa zai kashe ki Amina, ai taura biyu bata taunuwa a lokaci daya babu yadda za a yi ace a shari'ar ma'aurata an saurari b'angare daya ni ba zan yarda da maganarki ba har sai ya zo tukkuna an zauna an zube magana sai a fahimci wanene mafi rijayen lefi."
Cikin kukan na ce." Anti Yagana ke fa macace ya kamata a ce kin dubi halin da nake ciki, ki fahimce ni wallahi ina da matsala ba wai da gangan nake so auran nan ya mutu ba ina da hujja mai karfi."
"Hujjarki ai bata wuce kina gudun haihuwar yara masu cutar sikila ba dalili kuwa shine rashin had'uwar jini. Wannan ce kad'ai hujjarki wadda na sani Amina, sai kuma kishin da yake damunki tunda na ji labarin an ce ya sake yin wani auran, in bayan hakan ban san wani abu da ki ka taka ba. Sannan kuma ai kai tsaye ban ce miki baki da gaskiya ba, cewa na yi a bari a ji ta bakinsa tukkuna kafin a yanke hukunci wannan shine adalci, ai duk yadda zan so shi bayanki ne, matsalar namiji kuwa muddin ki ka ce ba za ki iya d'aukarta ba to Amina kina tare da damuwa domin kuwa kusan gabad'ayansu haka suke.
Na ce." Wallahi anti Yagana ban da Babansu Fadila a ciki, ai ya yadda ki ka kasa fahimtar damuwata tuntuni na tabbatar da cewa ba ki kai ajin da nake ba dangane da karatun namiji, maza uku fa na aura kuma kowa da halinshi wallahi ban ta'ba shan wahala a hannun Yaya Aminu da Alhaji Muntari irin wadda nake sha a hannun mutumin nan ba. Ku ne kawai kuke yi mini kallo hutu da jin dadin amma ni kadai nasan irin takaicin da nake 'kunsa."
Murmushi ta yi har sai da na ji sautinsa ta furta." Ha'kuri dai kawai na fi ki shiyasa ki ke ganin kamar ba ni da wata matsala da mijina. Amma kai tsaye ba zan musanta miki ba domin kuwa mai-d'aki shi yasan inda yake yi masa yoyo abinda nake so dake anan shine ki gaya mini kina ina yanzu hankalina zai fi kwanciya."
Kai tsaye na ce." Ina nan gidan Baban Saude yanzu haka."
Cike da zullumi ta furta." Gidan Baban Saude fa ki ka ce Amina?"
[9/25, 8:18 PM] Aunty B: 93
"Kina da hankali kuwa Amina, shin ko kin manta halin Baban Saude da d'aukar jidali akan abu 'kalilan zai mayar dashi babba. Mai yasa ba ki yi shawara da ni ba tukkuna kafin ki yanke wannan hukuncin sanin kanki ne Alhaji Tajudden ya yi nisan da wani mahalu'ki zai kai ya ta'ba mutuncinsa ko da babu dukiya kuwa to dattijanka da girma da mutuncinsa ya wuce a ce kina yawon kai shi a k'ara, kuma duk ki tsallake 'yan uwan Babanmu saboda raini ki taho wurin Baban Saude saboda dama kin tabbatar da cewa shi din ba mutum ne mai nisan tunani da tsinkaye akan lamari ba. Yanzu me ki ke tunanin zai faru idan har ya kashe miki aure wallahil-azim ba ni babu ke Amina." Ta kàrasa maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa.
Sosai kaina ya d'aure da jin maganarta. Wai yau anti Yagana itace take kiran Baban Saude da mutum mara tsinkaye saboda wani na daban, ta manta cewa Baban Saude ciki daya suka zauna da Mamanmu. uwa daya uba daya ba wasa ba ne, kuma wallahi duk tsayayyar da yake yi akan gaskiyarsa yake mutane ne suke ganinsa masifafe. Ba na shakka ko fargabar had'uwarsu da Alhaji Tajon ai mutunci da sanin ciwon kai ya fi komai a rayuwar wanda yasan kansa. Baban Saude ba makwadaici ba ne ballantana yana ganin gaskiya ya take da gangan. Ai da Babanmu zai d'auki wani mataki da tuni ya d'auka tun kafin lamarin ya yi tsanani irin haka to ballantana kuma baba Sule da yake da son abin duniya. Ni gabad'aya ma na rasa gane inda anti Yagana ta dosa wallahi da ban san halinta ba da sai nace itama kudinsa take kwad'ayi. To na san halinta da kawar da kai da kawaici akan abin mutum sam bata da wannan zulamar. Abin mamaki wai yau anti Yagana ce take cewa idan na rabu da wani namiji ita da ni har abada. Sai kawai na ji wasu zafafan hawaye sun k'wace mini suka fara kasa tsere a kumatuna. A hankali na ajiye wayar na silale na kwanta saman ledar dake tsakar d'akin Ina wani irin kuka mai ciwo lallai mutumin nan ya yi wa rayuwata illa ta kowane 'bangare.