Sashe 33
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zama na yi da hijabin a jikina. Shiru ya ratsa wajan yana ta dube-dubensa bai ce komai ba. Sai da ya gama tsaf sannan ya rufe computer ya dube ni tare da cewa." Za mu je gidan Momi ki dubata ko?"
A sakarce na ce." Wacece Momi?" Duk kuwa da cewar na gane wadda yake kira da sunan irin yadda na ji yaran na kiranta da shi.
Ya ce." 'Yar uwarki mana, da gaske ba ta jin dad'i kin san zafin zazzabi da mura dai."
A nutse na ce." Mai zai hana ni zuwa na dubata, to Allah Ya sawwa'ke."
Ya amsa da "Amin."
Shiru ya sake biyo baya kafin na ce." Ya Hauwa kuna waya ko?
Da sauri ya ce." Sosai ma kuwa, d'azu nan kafin na shigo sai da na kira ta, wannan watan da ya mutu shine na haihuwar wani ya kama sakamakon scanning ya nuna bakwai ga wannan watan da muka shiga shine daidai lokacin haihuwar."
Na ce." Idan hakane ana sa rai nan da kwana uku kenan?'
'' 'Kwarai kuwa, to amma kin san irin wannan ai ba a yankewa Allah hukunci."
Na ce." Hakane wata'kila ma ka ga gobe ta haihu don ba abin mamaki ba ne a wajan Allah."
Ya ce." Allah Ya sauketa lafiya dan Annabi."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Sai da muka ci abinci tukkuna muka fita zuwa gidan nata.
Adam da Yusi muka samu a falon suna kallo . Na tsaya muna magana yayin da shi kuma maigidan ya nufi sama ban bi shi ba saboda bai nemi hakan ba. Ina nan a tsaye ban kai ga zama ba ya sauko yana cewa ya ki ka tsaya anan Amina.
Ban ce masa komai ba illah Ido da na zuba masa. Akan wanene dalili zan bi shi ai yana da kyau a ce ya fara shiga ya sanar mata tunda ba a san a halin da take ciki ba. Idan shi mijinta ne ni kuma fa, wata'kila hakan bai zai yi mata dad'i ba.
Bayansa na bi muna hawa benan yana sake tisa maganar wai na tsaya Ina ta d'ari-d'ari na'ki sakin jikina. Na yi masa shiru ban tanka masa ba. Da dai naga ya'ki ya bar maganar daf da zamu shiga d'akin na tsaya Ina dubansa babu fara'a a tare da ni na ce ." Don Allah maganar nan ta isa haka fa, ina dalili sai maimaitawa ka ke yi, ai ba daidai ba ne kai tsaye kawai mu kutsa mata d'aki idan kai babu lefi hakan ni kuma fa, ai ba mu san halin da zamu same ta ba."
Yadda na nuna 'bacin raina akan hakan ya sanya bai sake wata magana ba muka shiga d'akin. Na yi kokari sosai wajan ganin na daidaita yanayin da nake ciki.
Tana zaune gefan gado sanya da kayan bacci a jikinta. Wata kujera dake can gefe ya nufa ya je ya zauna shi kadai nasan ya yi hakan ne domin mafitarsa yana tsoron ya zauna kusa da wata daga cikin hakan ya zama lefi shiyasa ya ke'be kansa waje daya.
Sosai muka gaisa cikin sakewa tunda dama ita din macace mai fuska da iya hurd'a da mutane. Babu wani abu na kishi da ganin kyashi da na karanta a tattare da ita. Sai dai na hangi tsantsar soyayya a cikin idanunta. Domin kuwa motsi kad'an za ta juya ta kalleshi ta dinga kokarin janyo shi cikin maganar da muke yi a tsakaninmu ni da ita amma ya'ki ya sake ya dai 'kyalemu muna hirarmu. Daga karshe ma sai ya sauka kasa ya bar ni tare da ita. Anan na dinga nazarinta duk da dare ne na fahimci tana jin jiki kuma murar ta kama ta da k'arfi. A lokacin sai kawai zuciyata ta dinga raya mini wani abu wai ko ciki ta samu domin sai nake ganin yanayinta kamar na mai karamin ciki. Kirjinta ya ciko ita kanta ma gabad'aya ta murmure ta yi ki'ba amma ba sosai ba. Jikina ya k'ara yin sanyi da al'marin Ubangiji. Lallai ciki ne da ita kuma shine dalilin da ya sanya duk ya gigice tunda abinda yake nema ne ya samu.
Duk da ban tabbatar da hasashena ba amma tun a lokacin na ji na fara tausayin kaina. Zuciyata ta dinga yi mini munanan tunane-tunane. Idan ma har na samu cikin na haihu yarana ne za su tashi daban a gidan masu d'auke da wata lalura idan da k'arar kwana kuma d'aya bayan daya duk su mutu.
Da wannan tunanin na kasance har muka bar gidanta daurewa kawai nake yi amma gabad'aya zuciyata ta kasa juriya sai da na buya a toilet na ci kuka na 'koshi na dinga yin istigifari da rokon Allah ya sassauta mini abinda nake ji a cikin zuciyata.
Washe gari da safe sukuku na tashi babu karsashi a tare da ni. Hakan kawai abinda ba ni da tabbas akai ya ke nema ya daga mini hankali. To menene ribar auran ne haihuwa ce, mai yasa nake jin b'akinciki dan matar ta samu ciki. A ganina ai abin murna da farinciki ne a gare mu bakidaya..
Shirun da ya yi mini bai gaya mini matarsa tana da juna biyu ba shine abinda ya yi mini ciwo a ganina menene abin boye mini, idan ba yana nufin wani abu ba. Ko yana gudun ya gaya mini na ji haushi ko na nuna b'akincikina. Duk da bai zama dole a ce ya gaya mini abinda ya shafe shi da matarsa ba, amma ai idan da fahimtar juna da zama na amana ba lefi ba ne don ya gaya mini sai mu had'u mu yi farincikin tare gabad'aya.
Na yi ta ko'karin ganin na danne damuwar da nake ciki amma ina sai da ya fahimci wani abu yana damuna.
Ya dinga bibiyata duk domin son ya ji abinda yake damuna kawai na ce masa babu komai. To ne zance masa ni ban iya 'karya ba balle na yi masa, babu kuma dad'i na fito fili na nuna jin haushina dan matarsa tana da ciki.
Kwana biyu a tsakani ya gaji da tambayata ya kyaleni kawai ya zuba mini ido tunda ya lura da cewar ba na son doguwar hira sai ya daina nema da ita. Amma baya fashin kwanciya da ni duk ranar girki na. A haka ya yi kwana biyu a wajena ya koma gidanta a washe garin ranar ya shigo da safe lokacin ma ban ma tashi ba tunda na yi sallar asubahi bacci ya d'auke ni mai nauyi. Shine ya tashe ni da farinciki yana gaya mini yanzu nan Hauwa ta haihu.
Ganin yadda yake cikin annashuwa da murna ya sanya ni dole ni ma na ara na yafa ina tambayarsa abinda aka samu namiji ne kuma gabad'aya suna cikin koshin lafiya.
Fatan alheri na yi musu gabad'aya tare da addu'ar Allah ya raya abinda aka samu. Ya kuma bada lafiyar shayarwa. Ya ji dad'i kuwa ya dinga amsawa cikin jin nishadi.
A ranar ya shirya tafiya bauchi da nufin zuwa ya je ya dawo duk a ranar tunda tafiyar jirgice. Ban damu ba tunda ba kwanana ba ne, na yi masa addu'a da fatan alheri ya tashi ya fita domin zuwa ya kintsa.
Sai bayan ya tafi tukkuna na shiga tunanin da na sani na kar'bi lambar wayarta a wurinsa sai na kira ta na yi mata barka tunda rantsuwar nan da na yi tana nan ba zan sake taka kafata garin ba sai dai duk abinda za a ce an jima ba a fad'a ba, wannan duniyar idan har mutum ya ce sai ya farantawa wani rai yana tare da wahala domin kuwa wasu lukutan ma Wanda kake kokarin ganin ka bashi farinciki shine na gaba gaba wajan ganin ya jefaka a masifa. Baban Saude ba irin nasihar da bai yi mini ba akan zama lafiya da abokanan zamana, na kuma d'auki nasiha da shawararsa duk wadda ta shirya zaman lafiya da ni, to ni ma a shirye nake dana zauna lafiya da ita, amma wadda take ganin ta fi karfin ta ba ni girmana na babba a cikinsu sai ta yi rayuwarta ni ma na yi tawa.
Wannan shawarar na yanke a zuciyata wani sashe yana gaya mini cewa da duniya zata zageni hakan zai sake tabbatarwa da masu zargina cewa Ina hassada da ciki da haihuwar. Tunda ai tun farkon samuwar cikin an sha rigima da ni akan wani dalili.
Ni ba zuwan ne matsala ba a wajena ba, Ina gudun kallon banza da habaici shine kawai abinda nake tunani, ba na so a yi mini abinda sai hasalani na kasa jurewa na aikata abinda bai da ce ba.