Sashe 5
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
mana ni da Yusura na had'o da hijabai biyu da takalmi flat ko rabin awa ba mu yi ba muka koma gidan Hajiya Saratu tana kara ta tausata don gaskiya yanayinta gabad'aya ya nuna takaicin abinda aka yi mini tana gaya mini ita kanta ta rasa abinda yake damun Hajja a tsukin nan don ta fahimci kamar tana shakkar Inna Uwani dalilin ma da ya sanya ta fara dora zarginta akanta Na nuna mata babu komai kawai amma can kasan zuciyata abin yayi mini ciwo kawai da gaske, zan yi kokarin ganin na taushi zuciyata har mu tafi wani abu bai faru ta b'angarena ba. Mussaman aka kunna genareto saboda mu. Gidansu Hauwa sai na ce da kadan ya dara namu gidan kwaryar sama ce take dukan ta kasa. Gidan kuma na had'aka ne mutum uku ne amma kowa da nasa bangaran wanda ya rasu ne kawai gidansa a waje. Mahaifinsu ya rasu kuma shine babbansu sai dai gabad'ayansu 'yan boko ne babu wani dan kasuwa a ciki suna ci da biro da takarda rufin asiri na abinci ne kawai kuma a cikin sa'aninta dai Ina ganin ita kad'ai ce take auran mawadaci sauran duk sai a hankali suna kula da kansu ne dalilin aikin gwamnati da suke yi sai dai yadda na lura suna da hadin kai da k'aunar junansu ba kamar na mu gidan ba. Wajan goma da rabi har mun kwanta ni da Hajiya Saratu da Yusura muna d'aki daya ita Hajja da 'yar uwarta suna tare Hauwa kuwa ba na ce ga inda take ba tunda ko lokacin da muka dawo ban ganta a falon ba. Muna d'an ta'ba hira kad'an kad'an Hauwa ta shigo da wayarta a hannunta tana fad'in." Har kun kwanta ne?" A tsanake na dubeta na ce." E wallahi." Sai ta miko mini waya tana cewa." Maigidanki ne yake so ya yi magana." Na yi sakare Ina kallonta yana so ya yi magana da ni bashi da lambata ne?" Abinda zuciyata take tambayata kenan. Ta sake maimaita maganarta tana cewa'' Wata'kila ya kira layinki bata shiga ba kin san matsalar network, ni dai yanzu ya kira ni ya ce na hada shi dake." Ban ce komai ba na amshi wayar sai ta juya ta fita ni da Hajiya Saratu muka bi ta da kallo. Ita dai girgiza kanta ta yi a hankali ta koma ta kwanta ni kuwa na tashi zaune da wayar a hannuna ina tsammanin kiran nasa. Minti biyar da fitarta ya kira. Na daga a nutse na ji yana cewa." Kin kai mata wayar?" "Eh ta kawo mini barka da dare?" Na fad'a tare da ko'karin danne damuwata." Ya d'an diririce ban san dalili ba can kuma na ji ya amsa yana cewa." Dazu na kira Hauwa a waya ta ce mini kun fita ke da Hajiya Saratu ina kuka je?" Babu mamaki a tare da ni saboda nasan zai iya yin abinda yafi haka na furta." Ta yi mini rakiya ne na sayo abu a shop saboda ban yi guzurin kaya ba don ban yi zaton zamu kwana ba." Ajiyar zuciyarsa na ji kafin ya ce." Kada ki kara shiga wani shago da zummar sayan kaya Amina hakan yana nufin abubuwa da yawa, kin san dai ba zai yiwu ace ku je Bauchi ko dawo a ranar daya ba, me yasa ba ki bawa maganata muhimmanci ba a lokacin dana kira ki na gaya miki ki shirya ki bi su." Na hasala da jin yadda yake ko'karin d'ora mini lefi shekkenan ni ba zan yi kuskure ba, kuma ai da ya gaya mini bai ce mini na hada kayana kwana za mu yi ba." Na ce." Shine me? ai lefin ba na kowa ba ne naka ne ko ka gaya mini na hada kaya zamu kwana? da ka kira ni ka sanar da ni na bijire maka ne, na ce to shikkenan ban yi maka jayayya ba saboda kuskure karami sai kuma a gaza fahimtata." "Ban kira ki don ki gaya mini magana ba Amina, na ce kada ki sake shiga shago ki ce za ki sayi abu ina da dalilina." Shiru na yi ban ce masa komai ba sakamakon yadda na ga Hajiya Saratu ta tashi zaune tana kallona da yanayi na damuwa. Sai kawai na datse kiran ban tsaya na saurari sauran maganarsa ba, wane irin dalili ne dashi wanda ya wuce na tozarci shikkenan don ina a matsayin na matarsa ba zan shiga shago na sayi abu ba ni din wacece. Itama Hauwa ta so faruwar hakan hakan ne amma menene na gaya masa ga inda muka tafi bai kira ni a waya don ya nuna ya ji dadin karar da na yi musu ba ya kira ni yana tuhumata akan wane dalili. Ban iya daure kukan da yake ta yun'kuro mini ba na fara share hawayen da yake gudana a kumatuna Yusura ta yi lamo akan katifa tana kallona kamar ta taya ni kuka. Hajiya Saratu ta dafa kafadata tana rarrashina a yanzu ita kadai ce take nuna damuwarta a kaina Hajja kam sai a hankali 'yar uwarta ta samu galaba akanta. Hauwa ta shigo domin ta kar'bi wayarta ta same ni Ina kuka muna tattauna abinda yake faruwa da Hajiya Saratu sai ta yi kasa'ke tana kallonmu a lokacin Hajiya Saratu ta rufe ta da fad'a tana cewa." Ki ji tsoron Allah Hauwa yadda ki ke ko'karin gyara auranki to na hore ki ki gyara na 'yar uwarki wadda ki ka zo ki ka sameta da mijinta, bayan abinda ku ke yi na karkashin kasa har sai kin yi mata bita da kulli kin san fa duk abinda ya faru me zai sanya don ya kira ki a waya sai ki gaya masa shikkenan mutum baya kuskure.. Babu wata damuwa a tare da ita ta ce." Sai na yi karya kenan ko anti Saratu na ce masa gata nan a kusa da ni ko me? Ya tambayeni ina take na ce masa kun fita tare zata sayo kaya ko ba haka na ji kuna maganar ba. A lokacin da na yi masa karya ya ce na bashi ita kuma na yi yaya kenan, kuma na ji kina cewa muna yin abu ta k'arkashin kasa, ita din da kike shedarta kina da tabbacin ba ta yi ne? ai alhaki koikoyone wata'kila abinda ta yi ne ya waiwaiyo mata, ni wannan ai sai dai na kalleta kawai 'kiri-'kiri tana nuna mini 'kyama ta kuma fito da hassada da kishinta muraran a kaina ciki dai da izinin Allah sai na haifehe ko ana so ko ba a so gwara ma mutum ya ha'kura ya barwa Allah ikonsa