Sashe 4
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
E mana son rai da gangan domin kowaye ya ji wannan batun ya san son zuciya ne. Sai kawai na rabu dashi dama sautari idan yana irin wannan fushin na bashi ha'kuri ya ki ji share shi nake yi domin daga zarar ya fahimci damuwata akan abinda yake yi sai ya sake tsanantawa daga na watsar dashi sai kuma ya fara neman shiri. Sabgarsa na fita saboda na tabbatar da cewa ban yi abinda ya kai ayi mini irin wannan wulakancin ba. Sati guda ban neme shi ba ranar litinin da misalin uku da rabi na rana ya kira waya lokacin ma tana hannun Yusura tana game ta kawo mini. Babu damuwar komai na gaishe shi cikin nutsuwa domin idan na nuna masa na ji ciwon abinda ya yi mini zai ji dad'i tunda haka yake so ashe daliline ya sanya shi kirana ba wai ya kira ni domin ya ji yaya nake ba. Kanin mahaifin Hauwa ne ya rasu shine za a yi ayari har da Hajja gobe zuwa can bauchi shine yake ba ni umarinin na shirya gobe da wuri direban gidan Hajja zai zo ya d'auke ni mu tafi tare tunda ni nan bai ajiye mini direba ba sai dai gidan cike yake da masu tsaro. Jin gaisuwar mutawa ce ya sanya ban yi jayayya ba na ce masa to kawai bai kuma jirayi komai daga gare ni ba ya datse wayarsa cikin raina na ce za ka yi ka gama. Ina zaune Ina zullumi yadda zan shiga cikin dangin Hauwa da wane irin Ido zan dube su domin dai Hauwa ce tasu ba ni ba, bai zama lallai su fahimci hakkina ba tunda itace 'yar uwarsu. Idan kuma na ce ba zan je ba zai iya zama gagarimin lefi ta yadda za a kama ni da hujja a ce ni ce ba ni son zaman lafiya da Hauwa. A daran na kira anti Yagana na gaya mata ta yi mini fatan alheri na sanar da Babarmu ma shima dai addu'ar zuwa lafiya da dawowa lafiya ya yi mana Da safe da wuri muka shirya don ba mu kai ga karyawa ba ma direban ya iso haka muka tafi da abin karin can gidan hajjan idan mun je sai mu karya kafin mu tafi. Ban samu wata tar'ba muhimmiya daga wurin Hajja ba, babu wannan k'aunar da nake ganinta a cikin idonta, babu dai k'yama kuma babu sakin fuska muka gaisa kadaran kadahan. B'angaran Hajiya Saratu babu wata matsala sai ma rashin jin dadin abinda Hajja ta yi ya bayyana a fuskarta. Ban nuna damuwata a sarari ba na danneta dama na riga nasan duk daran dadewa inna Uwani sai ta farraka tsakanina da Hajja tunda a zahiri ta fito ta nuna kishin hakan, amma ni a ganina abinda na yi bai kai ace kowa ya kasa yi mini uzuri ba sai dama idan da wata a kasa. Na ji dad'i da ban ajiye ba balle na yi fargabar wata matsala ta kutsu ta rabuwa na yi danasani zan kuma kiyaye faruwar hakan tunda dama da soyayyar Hajja nake gadara an shiga tsakani. Koda Hauwa ta fito a kintse cikin shiri har da yar k'aramar akwati ni kam ban yi guzurin komai ba sai a lokacin ma na tuna za mu iya kwana fa tunda gidansu ne bai zai yiwu ace mu je mu dawo a ranar ba. Babu yabo babu fallasa muka gaisa tana zauna kujerar da Hajja ta tashi tana duba wayarta na dinga nazarinta a fakaice ta kara haske ainun abinka dama da farar fata ya yi bul-bul irin na mace mai yaron ciki duk wannan ramar babu ita kirjinta ya ciko sosai kamar wadda take rayuwa a ketare. Na d'an janye idona a hankali na sauke ajiyar zuciya Ina nazarin yadda za ta kaya domin dai ni ba zan ce direba ya mayar da ni domin d'auko kaya ba idan kwanan ya zama dole na nemi shop na sayi koda abaya ce. Zaman mota ya sanya kafafun Hajja yin tsami da kyar ta fito daga motar tana kukan kafafunta na yi mata zugi. Ni na taimaka mata muka shiga gidan Hajiya Saratu da ita Hauwan suna bayanmu Yusura kuma tana gefena ri'ke da jakata a hannunta. To an ce duk inda mai kudi yake yana da wani irin kwarjini da haiba abinda ya faru kenan saukarmu a gidan rasuwar ke da wuya maza daga waje suka dinga shigowa suna gaishe da Hajja ni kaina wasu daga cikin dangin Hauwa sun mutuntani gaisuwa ta mutunci muka dinga yi da su. wad'anda na fahimci kuma ban ishe su kallo ba ni ma bana kallonsu amma na yi kokarin samun inna Uwani a gefe na gaisheta domin sai satar kallona take yi kuma ba ta ce mini komai ba. Ta amsa babu yabo babu fallasa sai na ja gefe guda na kame kaina Yusura na gefena don ma Allah Ya yi mini kwarjini da haiba da ban san abinda zai faru ba. Akwai wasu dana lura suna ta shige da fice a d'akin da aka sauke mu kuma na fahimci sa'anin Hauwa ne irin 'yan uwan nan da aka tashi tare daya dai daga cikinsu da ta gaza ha'kuri ta dube ni da dan murmushi irin na munafurci sai ta kalli Hauwa dake kwance lakadan tana lasar lemon tsami saboda yawun da yake cika mata baki tana tambayarta wai Yusura 'yata ce dan an ce dama ina da yara biyu. Sai ta bata amsa da cewa itama bata sani ba. Hajiya Saratu da ta fahimci kamar da cin fuska ta yi tambayar ta ce." Sadiya idan 'yarta sai me, ina ce kema kina da 'yan matan yaran nan don Allah ku dinga yin shiru dangane da abinda bai shafeku ba." Ta na dariya ta ce." Anti Saratu daga tambaya sai a yi mini fassara ayi ha'kuri to." Ta d'auki wani fulas da yake cike da funkaso ta fice daga dakin. Hajja ta dan dube ni a nutse ta ce." Wai ni Amina yarinyar wacece ne wannan?" Na ce." Yarinyar Sahura ce Hajja ai ta jima a hannuna tun tana kan'kanuwa." Ta ce." Ayya, ai shi Yusi ya'ki zaman nan fafur da Baban nasa zai tafi har da kuka sai ya bishi Shima ya daure masa gindi wai saboda makaranta." Murmushi na yi a hankali na ce." Ni kaina Hajja na manta yaushe rabon da naga Yusi ko gidan da na tare fa bai zo ba." Ta ce." Ai duk lefinku ne kun yi abu a 'kunshe waye zai san halin da kuke ciki, ina sane ni ma ban zo ba, da ya yi mini jagora na duba Gwaggo na yi dawowata gida.." Da mamaki a tare da ni na ce." Hajja Yusi ne ya yi mini jagora har gidan Gwaggo." '"Kwarai kuwa shi da direbana kafin su tafi shima baban nasa sai labari ya ji mun je mun dawo." Na yi kasa da kaina cikin jin nauyi na ce." Ki yi hakuri Hajja hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allahu rabbi. Shiru ta yi ba tace komai ba. Hajiya Saratu kuwa sai murmushi take yi ta ji dadin yadda Hajjan ta saki fuska har muna hira wannan yana nuna mini ko da asirin har yanzu akwai sauran kaunta a cikin zuciyarta. [9/16, 10:20 AM] Aunty B: 83 Sai bayan Ishai tukkuna muka tafi gidan inna Uwani dalili gidan da akayi rasuwar a cike yake da jama'a kasancewar gobe ne za a yi addu'ar sadakar uku. Babu nisa a tsakanin gidan mutuwar da gidansu Hauwa gabad'aya muka nufi can din har da ita. Hajja ta ce gobe da wuri idan an yi addu'a sai mu kama hanya mu tafi gida sosai na ji dadin hakan don haka inna Uwani tana shigowa tana gaya mata abinda ta yanke ta nuna rashin jin dadinta akan hakan har dai ta gaza yin shiru tana gaya mata ita me yasa idan ta je mata take wata da watanni ina lefin ma mu yi sati daya sai mu tafi. Jin abinda ta ce ya sanya mini fargaba don gaskiya bana so ko kwana daya mu kara a garin bayan wanda Hajjan ta yanke. Yanayin yadda inna Uwani ta nuna b'acin ranta ya sanya hajjan ta ce idan an yi addu'ar gobe jibi sai mu tafi lokacin dai duk wanda ya kamata a gaisa dashi an gaisa. Dukda hakan dai inna uwani ba ta ji dad'i ba ta so a ce mun zauna mun yi sati guda kamar yadda ta buk'ata. Jin shawarar da suka yanke ya sanya na fara tunanin nemawa kaina mafita dole gobe ma mu shiga cikin mutane kuma ba zai yiwu na sake komawa da kayan jikina ba ba don komai ba sai don na siyawa kaina mutunci. Na gayawa hajiya Saratu abinda yake da akwai da buk'atar son ta yi mini jagora mu fita a daran tunda da sauran lokaci dare bai yi ba. Hajja ta kama fad'a sosai irin wanda bata taba yi mini ba gabad'aya taki kar'bar uzurina tana fad'in ai nasan ba yadda za a yi mu yi tafiya irin wannan mu je mu dawo a ranar na ce mata mantawa na yi sai da muka fito daga gidan tukkuna Allah ya tunasar da ni. Ina jin inna Uwani da tunda muke maganar ba ta ce komai sai da ta ji hajjan tana yi mini fada tukkuna ta sanyo bakinta wai ko dai ba na son zuwa aka tursasani. Takaici da b'acin rai bai barni na sake wata magana ba, na yi shiru kawai da bakina Ina mamakin yadda yanzu gabad'aya Hajja ta daina fahimtata ta kuma daina tausaya mini. Haka dai muka fita ni da Hajiya Saratu ran mu duka a b'ace domin ita kad'ai ce ta dubi uzurina ta kuma fahimce ni ita Hauwa ma bata iya cewa komai ba har aka yi maganar aka gama kuma tana kwance a wajan amma uffan ba ta ce ba. Direban da muka zo dashi ne ya fita da mu. Garin ba bak'on Hajiya Saratu ba ne ta san wurare da yawa don haka ma ba mu yi nisa da hawa titi ba muka ci karo da wani shop a d'aya hannun na cewa magaji direba ya shiga damu ciki. Dogwayen riguna na sayo