Sashe 6
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Maganganun Hauwa sun yi mini nuni da cewa tabbas ta ji ciwon abinda na yi wanda har hakan ya sanya suka hade mini kai ita da mijinta. Amma kuma sun yi tsauri ga hajiya Saratu wata'kila ko ta manta da cewa ita din yayar mijinta ce fa ba kanwarsa ba, a tunanina ko kanwarsa girma da shekarunta bai kai ace ta tsaya a kanta da fitsara.
Ni idan ta yi mini kishiyarta ce ba abin damuwa ba ne tunda da kishi a tsakaninmu amma ni da ban had'a jini dasu ba ba zan ta'ba yi wa mai shekaru irin na Hajiya Saratu rashin kunya ba.
Abinda ya haddasa musu rikici kenan a tsakaninsu sai ya zamana ni na shiga tsakiya kuma a ta dalilina komai ya faru Hajiya Saratu fadi take yi "Ba za ta je ta zauna miki ba din, ko ita ce ta yi miki cikin, ai ni Amina ta yi mini daidai duk abinda za ku ce akanta kun dade baku fad'a shegiya mara kunya ki dubi tsabar idona ki dinga nema ki zage ni saboda kin samu kanki ko, idan kin manta bari na tuna miki ni Yaya nake ga Tajo ba k'anwa ba balle ki ce za ki gaya mini magana son ranki Ubanki zan ci domin ba na ciki da iskancinki shashasha mara wayo kawai, ai iliminki bai amfana miki komai ba sai rashin dubara."
Tana kuka sosai take fad'in." Ai ba sai kin zage ni kin aibata ni zai tabbatar mini da cewa' Ba kya kaunata ba, duk dai abinda za ki yi a kaina ba yadda za a yi ki ce ni ba jininki ba ce, aure kuma dole dake da wad'anda ba su k'auna ku yi hakuri gashinan har da rabo a tsakani, idan ba aikin asiri ba menene wannan an ce ta na yin surukulle irin nasu ba barebari kin k'aryata ni, duk yadda ki ke kaunarta ni ce dai taki ba kuma yadda za ki yi da ni."
Hajiya Saratu ta fusata ainun ta fitar da hannu ta tsinka mata mari tana cewa." Babu ruwana da wai kina da ciki Hauwa ni ba Hajja ba ce ba kuma zan yarda da cin kashi ba, sau dubu wallahi a yanzu gwara Amina dake tunda ita tana ganin girma da mutuncina, ke kam kin yi asara ba kuma ki ji dadin halinki ba.
Hauwa ta dinga kuka daga tsaye Hajiya Saratu na fesa mata kausasan maganganun har Hajja da inna Uwani suka shigo d'akin suna tambayar abinda yake faruwa.
Ni dai sunkuyar da kaina kasa na yi domin ban san abinda zai kuma biyo baya ba, abinda dai na yanke a cikin raina shine ko kasa da sama za ta hade ba zan kara zuwa sabgarsu ba har abada sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Hajja tana gama jin abinda ya assasa rigimar ta juya ta fita amma fuskarta kadai zaka duba ka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake. Shirun nata kuma sai ya yi ma'ana domin idan ta yi magana za a ga kamar ta goyi da bangare daya amma a zahiri kowa ya san Hauwa ita ce mai lefi
Haka muka wayi gari rayukan kowa a b'ace da da kyar ma inna Uwani ta amshi gaisuwata haushina take ji sosai a ganinta ba kowane ya haddasa rigimar nan ba sai ni tunda ni ce bare a cikinsu kuma hajiya Saratu ta zabe ni akan 'yar uwarta.
Da sassafe washe garin sadakar uku muka d'auko hanya amma banda Hauwa wai sai ta dan kwana biyu tukkuna kodai ba ta zauna ta haihu ba sai cikin ya yi k'wari tunda duk dambarwar da ake yi duka cikin bai fi wata uku ba.
A gidan Hajja muka ya da zango ban kuma tafi a ranar ba tunda dare ya yi sai da gari ya waye tukkuna na shirya tafiya har yanzu da damuwar abinda ya faru a tare da ni dalilin ma da ya sanya kenan ban bar gidan ba sai da na tabbatar da cewa na wanke kaina a wurin Hajja na kuma kar'bi gyara da kuskuran da na yi, amma na nuna mata har abada Hauwa ba a matsayin kishiya na d'auketa ba 'yar uwarta ce kuma ni ma ban ji dadin rikicin da ya faru duk ta dalilina ba.
Muka rabu ba k'ullatar juna yayin da muke ta bawa juna ha'kuri ni da Hajiya Saratu tana ganin ni akayi wa lefi ai ni ya kamata a tausa acewarta tijarar da Hauwa ta yi mata kuwa ai kanta ta tonawa asiri ba wani ba har yau har gobe kuma tana goyon bayana ko mata dari Tajo zai ajiye a gidansa ni ce dai wadda ta aure shi a lokacin da mata suke gudunsa.