Sashe 20
Gudun Aure Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki babu kuzari ta furta." To shikkenan in sha Allahu rabbi ki jiraye ni daga zarar na taso daga aikin zan shigo, Allah Ya rufa asiri." A takaice na amsa da 'Amin Ya Allah." Na kashe wayar na ajiye a kusa da ni.
Wajen sha biyu na fita falon sai Yusra kadai a zaune tana duba Wani littafin.
Na tambayeta baba Tabawa ta ce mini ta shiga kicin yanzu. Kai tsaye hanyar kicin din na nufa na sameta tana hidimar dora abincin rana na ce ta had'a kayan waina masa saboda zuwan Sahura tunda favorite dinta ne. Store din ta nufa da sauri tana fad'in." To bari na duba buhun shinkafar don ta d'auko hanyar k'arewa."
Store din na bita tana daga buhun farar shinkafar bata fi sauka gwangwani shida ba. Na dubi kayan abincin da suke store din lallai bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa
zara bata barin dami. Ko da yake ai saura kad'an na shekara da tarewa a gidan kuma tun lokacin kayan abincin suke ake diba tunda har da masu gadin gidan ake yin abincin da Ayuba direba sun yi kasa sosai kayan abincin kuma ba na tsammanin zan kira shi domin na gaya masa ga halin da ake ciki.
D'aki na koma na d'auko kudi na fito na ce Yusura ta kira mini Ayuba. Ina tsaye a bakin kicin Baba Tabawa tana ciki tana goge-goge muna d'an ta'ba hira ya shigo na bashi dubu goma na ce ya sayo mana farar shinkafa ta towo na sake bashi dubu biyar daban na ce ya yi cefane da ita. Da sauri ya kar'ba ya fita ya kama hanya ya tafi. Ni kuma na koma cikin d'aki na zauna ina cigaba da karanta wasi'kar jaki.
Sai bayan da na tabbatar ta ci abinci ta samu nutsuwa tukkuna na fara gaya mata abubuwan da suka faru da kuma hukuncin da na yanke akan matakin da ya d'auka a kaina.
Ta jima tana jimantawa kafin ta dube ni a sanyaye ta furta." Na rantse da Allah Amina kaina ya kulle gabad'aya ma na rasa yadda zan yi na auna lamarin nan, to wai shawarar me ki ke so na ba ki tunda lokacin da za ki aikata ba ki neme ni ba. Ya fa fi ki gaskiya wallahi sai dai idan ki take hakan dagangan! Amma yanzu ke kanki kin san fasuwar maganar ba karamin gagarimin abu ba ne a wurinki."
Na zuba mata Ido da yanayi na 'bacin rai na ce." Sahura na lura ba za ki taba ganin kusuran mutumin nan ba, ban sani ba ko don kina aiki a 'karkashinsa ne oho, sau nawa ina gaya miki irin abubuwan da yake yi mini na rashin kyautawa amma ba ki taba goya mini baya ba, duk lamari idan ya faru sai ki ce lefina ne, shi kenan bayan kuskure duk abinda ya yi daidai ne saboda yana da kudi ko kina jin tsoron ki goyi da bayana ki samu matsala a wajen aiki ne."
Ta dinga galla mini harara kafin ta ja tsaki ta furta." Tare muka tashi yarinta da girma na tabbatar da cewa ko anti Yagana ba za ta fi ni sanin halinki ba Amina, nasan abinda za ki yi da kuma wanda ba za ki yi ba. Abinda fa ki ka aikata kuskure ne babba wallahi domin kuwa hukuncin rayawa da kashewa ba a hannunki yake ba to me zai sanya ki shiga cikin lamarin Ubangiji."
Shiru na yi ina kallonta jikina duk ya mutu da maganganunta. Sai ta cigaba da cewa." Dole ne na gaya miki gaskiya domin ni dake zama ne muke yin sa na gaskiya da amana babu yadda za a yi ki yi kuskure na biye miki zahirin gaskiya ba ki kyauta ba, kuma ni babu yawuna akan abinda ki ka kudirta abinda nake ganin shine alheri a tare dake ki cigaba da bibiyarsa kina bashi ha'kuri domin wallahi kin yi masa lefi mai ciwo amma da yake dan halak ne ya rufa miki asiri bai gayawa kowa ba. Duk irin shariyar da zai miki ki d'auka hakan hukunci ne yana sonki irin Wanda ke kanki ba ki yi tsammani ba na tabbata duk ranar da takaicin hakan ya sake shi zai neme ki ku sasanta, amma ba zan ta'ba baki shawarar cewa ki nuna masa daidai ki ke dashi ba alhalin ya yi miki zarra ta kowace siga kuma har yanzu dai tunda bai aiko miki da takardar saki ba kina nan a matsayin matarsa."
Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama sauraranta na ce." Na ji bayaninki sis, na amshi lefina kuma tun kafin ya bar garin nan na nemi afuwarsa na gaya masa na yi kuskure ba zan k'ara ba. Amma ina so ki sani cewa shi d'abiarsa ce haka muguwar gaba da ri'ko sannan kuma a lokacin da ake bashi ha'kuri a sa'in yake 'kara tunzura sai ya tsananta abinda yake yi. Watsar da shi tare da fita daga cikin sha'aninsa shine yake dawo dashi daidai. Na yi iyakacin abinda nake ganin zan yi, ai ba zina ya kama ni ina yi da wani ba, ba sata na yi masa ba, na uku ba madigo ya kama ni ina yi da wata mace ba. Abu ne ya faru wanda da ni dashi duka mun san haka, kuma mun shede a haihuwarmu ta farko. To me zai sanya haka kawai saboda kuskuran da na yi wanda nake da ya'kini Ubangiji ya gafarta mini sai shi a matsayinsa na adam ya ri'ke ni a cikin ransa da mummunan nufi. Wallahi na bashi ha'kuri Sahura na kwantar da kai na yi kuka da kalamai na gazawa da nadama ya'ki kula ni ya ki ke so na yi masa. Na gaji na yi rantsuwa da Allah da Annabi ba zan sake nemansa ba, kuma muddin ya k'ara wata d'aya akan watannin da ya d'auka bai zo inda nake ba zan bar masa gidansa idan ya so sai ya aiko mini da takarda ta inda nake a shirye nake da faruwar haka tunda ai ba wannan ne na farko ba."
Ta yi shiru ranta duk babu dad'i da kyar ta ce." Yanzu dai kin barwa wasu shi kenan, ke girman kanki ba zai bari ki kwaci mijinki ba ko sisi."
"Idan dole ta wannan sigar ya kamata ace na k'wace shi a hannuna wallahi na bar musu shi dama wahala yake ba ni a zamantakewar auran namu gabad'aya ya fi ni moriya domin irin galabaitar da ni da yake a shimfida ba kowace macace za ta jure ba. Ki bar maganar kawai Sahura za mu ga zuwan da dawowar kawai ki taya ni da addu'a."
"Shikkenan ai tunda haka ki ke ganin ya yi miki amma ina so ki sa ni cewa wata k'addarar fa bawa ne yake janyowa kansa ita da kansa. Kada ki ce Allah ne a wannan ga'bar domin kuwa kin so a lissafa miki aure abinda kowa yake gudar mike kenan."
"Ai da na haihu dashi ne zan damu ko na turasa zuciyata zama dashi saboda gudun kada a ce kowane d'a da ubansa Sahura to ban ajiye masa komai ba, kin ga kuwa lissafi aure ai ba komai ba ne tunda ba akaina a ka fara ba, idan har 'kaddara ta sanya ya sake ni to Ina mai tabbatar miki da cewa ni da aure har abada domin kuwa kin fi kowa sanin irin kalubalen da na fuskanta a rayuwata ta kowane fanni. Ai addinin musulunci addini ne mai sau'ki kuma auran nan ba fa farilla ba ne balle a ce dole kowane bawa sai ya yi shi. Idan na ce zan kare rayuwata a haka babu dalilin da zai sanya jama'a su zarge ni saboda na yi auran nan har biyu na ji dadinsa da rashin dadinsa wanda shi ya fi rinjaye muddin zan ri'ke kaina na iya sarrafa sha'awata a duk lokacin da ta motsa mini to yin hakan ba zunubi ba ne a wurin Allah."
Shiru ta yi mini tana kallona har na kammala maganata ba ta ce komai ba, yanayinta dai ya nuna sam abinda nake shirin aiwatarwa bai kwanta mata a rai ba sai don babu yadda za ta yi ne ta ha'kura ta yi mini shiru.
Sai daf da magriba ta tafi babu karsashi da sukuni a tare da ita cikin raina na ce ba zan ta'ba biyewa son zuciyarki ba Sahura saboda na riga nasan wanene Alhaji Tajo ciki da wajensa.
Bayan Isha'i muna falo gabad'aya domin ni ma fitowa na yi na zauna muna kallon tare domin na fahimci zaman takurar da nake yi zai iya haifar mini da wata matsalar wanda kuma nake yi dominsa hakan ba damuwarsa ba ce....Ayuba Ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yana cewa." Hajiya za a shigo da kayan abinci."
A nutse na dube shi." Kayan abinci daga ina?"
Ya ce." Maigidan ne ya sanya a kawo."
Da mamaki mai yawa na ce." Gaya masa ka yi cewa na aike ka sayo shinkafa d'azu."
Shiru ya yi tare da yin k'asa da kansa. Raina a 'bace na ce." Ashe duk abinda nake yi a gidan nan Ido ka sanya mini Ayuba ni ba ni da bakin gaya masa kenan sai kai ko?"
A nutse ya ce." Ki yi hakuri Hajiya umarninsa yin hakan domin ya ce duk halin da ake ciki a gidan a dinga sanar dashi."
Shiru na yi ina nazari wato duk shige da fice da zurga-zurgar da na dinga yi lokacin rikicin Hadiza sai da ya gaya masa kenan.
Na dube shi babu fara'a a fuskata na ce." Shikkenan a shigo dasu." Ya juya ya fita da sauri. Baba Tabawa ta tashi ta nufi kicin din da sauri domin gyara store din.