Sashe 9
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali suke tafiya lokacin da suka fito wurin awun.
A nitse suka miƙe ɗan corridor'n har cikin Office ɗin shi.
Bisa tattausar kujerar dake gefe ta zauna tare da sauƙe numfashi tace.
"Gsky Yah Sheykh yanzu kam fa na fara jin nauyin cikin nan, in zan É—aga kafata sai inji ya tokareni".
Goron ruwan faro mara sanyin daya ɗauko ya miƙa mata, tare da cewa.
"Eh dole kiji haka yanzu tunda cikin yayi ƙasa. Alamun haihuwa yau ko gobe ake cewa ko?".
Rufe goran tayi bayan tasha mai yawa kana a hankali tace.
"Uhummm ni naƙuda kawai nake tsoro in badon shiba ni Ko yauma in haihu mana kawai in huta".
Sunkuyowa ya É—anyi yayi kissing goshinta a hankali yace.
"La, la, la kada ki damu ke kam Aish na ƙudarma ni zan miki kinji"
Yayi mgnar cikin wasa da kwantar mata da hankali.
Da sauri tace.
"Allah yasa haka".
Amin Amin yace cikin murmushin.
Sai kuma ya fara tattare Æ´an abubuwa shi dan zasu wuce gida.
Yana gamawa suka fita suka tafi.
Yau asabar Sheykh ne zaune gaban Malam Abubakar da LamiÉ—o da Galadima dan Malam Abubakar É—in ne yazo har gida a nitse Sheykh yace.
"Toh Alhamdulillah Malam in Allah ya kaimu gobe.
Ƙannen maman Sulaiman Ya Adam da Ashiru su shirya suje. Abuja su kai kuɗin beli kamar yadda suka faɗa. Naso inje to kuma abubuwa sun min yawa."
Cikin gamsuwa ya gyaÉ—a kai kana a hankali yace.
"Sai dai kuÉ—in belin ne wuyar 3 million da sukace".
Kai Sheykh ya É—an É—ago tare da cewa.
"Eh ba damuwa na turawa Ashiru kuÉ—in a accutan É—insa in suje su cire suje musu da kash".
Cikin jin daÉ—i Malam Abubakar yace.
"Kai Alhamdulillah Muhammad Allah yayi maka al'barka Ngd matuƙa".
Amin Amin sukace kana sukaci gaba da wata hirarsun.
Alhamdulillah kuwa su Ashirun sunje lfya ranar Monday sun bada belin Sulaiman sun dawo lfy yan uwan shi mata kamar zasu mutu dan farin ciki.
Cikin Shatu kuwa gaba ɗaya ya sauƙo yayi ƙasa a hasashen likitoci sauran kwana takwas ta haihu.
Yau ta kasance ranar jumma'a ne.
Tunda safe Sheykh yayi shirin jumma'a'arsa.
Da sauri ya fito falonshi sai baza ƙamshi yakeyi.
Wani tattausan yadine a jikinsa lemon green mai masifar kyau yasha aiki da farin surfani.
Gariyar tayi cas da jikinsa.
farin hula mai ratsin lemon green ya kafa bisa tattausan gashin kansa.
sai takalminsa sau ciki shima lemon green.
Da sauri ya ɗan ja da baya ganin ya kusa yayi karo da Aish ɗinsa da cikinta da ya fito sosai yayi kuma ƙasa sosai in ka ganta har kamar ta ɗan rame.
Cikin kula tace.
"Hamma Jabeer fita zakayi ne?".
Motsota yayi a hankali ya É—an ruggumota kana yasa hannunshi ya É—an shafi cikin a hankali yace.
"Eh fita zanyi Aish ina son inje gidan Malam Abubakar dan mu gana da Sulaiman tunda ya dawo shekaran jiya ban samu mun naje na masa jajeba".
Cikin fidda sassanyan numfashi tace.
"To zaka dawone kafin azahar".
Kai ya jujjuya alamar a a.
Manna kanta tayi da ƙirjinsa kana a hankali tace.
"Toh kuma zanje makaranta fa, zan shiga aji daga ƙarfe sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya zamu gama takardun da suka rage mana".
ÆŠan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Wannan makaranta ni dai tana cimin rai".
Cikin sanyi tace.
"Toh ai ma mun kusa samun hutu yau last page É—in ezam É—in zamuyi".
Kai ya É—an sunkuyar ya manna hancinsa a wuyanta a hankali yace.
"Toh yanzu muje in kaiki da kaina in na sauƙeki sai in wuce gidan malam kuna tashi inzo in ɗaukiki in dawo dake, nasan kafin nan kuma lokacin salla yayi."
To tace kana taje ta shirya.
Ta zurma ƙaton hijabi.
Haka kuwa akayi yana sauƙeta saida ya tabbatar ta shiga aji lfy kana, ya juya ya nufi gidan.
Malam Abubakar.
A falonshi ya sameshi zaune shida Sulaiman.
Da sauri Sulaiman ya tasa ya nufi inda yake.
Cikin yanayi sabo da shaƙuwa suka ruggume juna.
Murya na rawa Sulaiman yace.
"Sheykh ngd ngd Ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya rufa asiri duniya da ƙiyama ya ceceka da wahalar siraɗi kamar yadda ka zama sanadin cetoni daga azabar hukumar ƴan sanda da na faɗa ciki".
Amin Amin yace cike da tausayin ganin yadda Sulaiman ya rame yayi duhu farin shin nan duk ya tafi.
Ga alamun tashin hankali da firgicin da basu gama sakeshi ba.
A hankali suka zauna gaban Malam Abubakar da yaketa sanya musu al'baka a duniya bai taɓayin ɗaliban da yake so da ƙauna sama dasu ba.
Cikin kula Sheykh ya É—an rusunar da kai tare da cewa.
"Barka da hantsi malam".
"Barka dai Muhammad, ya iyalin taka da Æ´an tagwaye da Jafar".
"Alhamdulillah duk suna lfy sai dai Yah Jafar yanzu kusan wata uku kenan, yake yawan yin bacci dare da rana safe da yamma, salla da cin abinci kaÉ—ai ke tada shi.
Ni kaina wasu lokutan sai inyi kusan kwana biyar ban ganshi ba, sai in nine naje Side É—insa".
Murmushi mai sanyi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
"Uhummm Alhamdulillah waraka na bisa hanya, ai bacci ga irin mai larurarsa alamun sauƙi ne".
Cikin jin daÉ—i yace
"Allah yasa haka".
Amin Amin sukace.
Kana ya kalli Sulaiman cikin kula yace.
"Sannu Sulaiman Allah ya kiyaye gaba ya taƙaita, ya sauƙaƙa mana ƙadda rorinmu, dani da kai dama sauran al'ummar musulmi baki ɗaya."
Cikin rauni murya na rawa hawaye na kwaranya, Sulaiman ya ɗago kanshi tare da son danne shessheƙan kukan da yake taso masa yace.
"Tabbas wannan yana ɗaya daga cikin manyan ƙaddarorina masu zafi a rayuwata, na kuma samu tsira da kuɓuta cikin sauƙi, kasan cewar inda masu damar yin mgn aji.
Amman tunda na dawo Jabeer ban bar yin kukan bayin Allah'n da na bari a tsare a can magarƙamar.
Ina kuka har inji numfarfashi na yana fizga, tunda na fito na barsu ban sake samun nayi bacciba.
Inajin tausayin kaina, inji tausayinsu, nayi ta kuka dana dawo da naga halin ƙunci da iyayena da yan uwana suka shiga.
Ina tuno su kuma wanne hali iyayensu da Æ´an uwansu suke ciki."
Sosai kukansa ya tsananta cikin tsananin kukan da yasa.
Malam Abubakar zubda hawaye Sheykh kuwa sai taune lip ɗinsa na ƙasa yayi cikin tausayin waɗanda Sulaiman yake mgn a kansu koda bai sansuba.
Shi kuwa Sulaiman murya na rawa yace.
"Yara ƙanana sun sadaukar da rayuwarsu domin tawa sun amsa laifin da ba nasuba domin ni in tsira.
Ko wani hali iyayensu ke ciki, kuma dukansu uwarsu É—aya ubansu É—aya".
Cikin rauni Sheykh yace.
"Me sukayi ne Sulaiman?".
Cikin wani irin shessheƙan kuka mai ciwo da rauni da tausayawa yace.
"Wanna itace tambayar da kullum sukeyiwa haukumar dake tsare damu kullum in sun shigo suna dukansu suna azabtar dasu tammaya É—aya sukeyi mushi nee.
"Wai me mukayi ne aka kawowu nan kuke ta dukanmu ku gaya mana laifinmu".
Zuwa yanzu hawaye sosai Malam Abubakar yake zubdawa.
Sheykh kuwa tausayi da rauni sun adaddabi zuciyarshi hawaye musu masifar zafi ke tsastsafo mishi.
Cikin rauni yace.
"To Sulaiman sun gaya maka ya kayi aka kaisu can ne?".
Kai ya fara jujjuyawa yana kuka murya a disashe kamar mace yace.
"Sunce suma basu san me sukayi ba, kawai suna kiwo sun shiga suyi al'wala akazo akayi ta kamasu ɗaya bayan ɗaya, daga nan aka rufe musu ido, su dai sunji an kwana tafiya dasu a wannan ranar da asuba aka iso dasu wannan magarƙamar. Ƙaramin cikinsu kullum yakanyi ta kuka yana kiran iyayensu".
Da sauri Sheykh yace.
"To amman meyasa aka tsaresu kuma su kansu basu san laifinsu ba anya ba karya sukeyi ba ko dai criminals ne, kasan suna da taurin zuciya".
Da sauri Sulaiman yace.
"Wlh wlh su ba criminals bane, tunda na gani a gaban idona akayi musu sharri kuma akasa suka yarda dashi dole, amman sun yarda dashi ne dan su tseretar dani".
Da sauri Sheykh yace.
"Kamar yaya akayi musu sharri?".
Hannu yasa ya share hawayensa murya na rawa yaci gaba da cewa.
"Tun randa aka kaini wannan magarƙamar nayi matuƙar mamkin ganin waɗannan yaran, yarane ƴaƴan Fulani masu tarin kyau da farin fata, saidai yanayin wahalar da ake gana musu kullum tasa sun rame sunyi baƙi.
Mafi akasarin kwanaki sai an daukesu hotuna ana tirsasu amsa laifinsu.
Ni da yake ko muntsilina ba'ayi wlh ana dukan yaran nan ina kuka, da fari na fahimci ko isasshiyar Hausa basaji tabbacin fulanine kamar dai yadda duniya takewa Fulani kuÉ—in goro ga duk wanda aka ji ya iya fillanci ko yana kiwo to ya zama ba fulatani, so nima kai tsaye nai zaton fulanine kuma sai akayi dace hakan ne.