Sashe 14
Garkuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Alhamdulillah Bappa duk suna lfy cikin farin ciki".
Ya bashi amsa yana murmushi.
Shi kuwa Bappa cikin kula yace.
"Yah Shatu na?".
Murmushi Sosai yayi kana yace.
"Alhamdulillah Bappa Shatunka ta girma yau É—azu da yamma gabanin magriba ta zama uwa".
Cike da tsananin farin ciki Bappa yace.
"Masha Allah! Alhamdulillah yaushe ta haifu mata na samu ko aboki mai tayani kiwo?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"A a Bappa wannan Gimbiya ce amrya ka samu".
Cike da farin ciki Bappa yace.
"Alhamdulillah Allah ya raya mana bisa imani".
"Amin Amin".
Yace yana mai jin muryar Junainah tana cewa.
"Ayyah Bappa bani shi Adda Shatu ce ta haihu?".
Cikin kula yace.
"Bappa a bawa Junainah waya".
To yace kana ya miƙa mata wayar, tare da juyowa ya kalli Ummey cikin murmushin yace.
"Alhamdulillah Shatu ta sauƙa lfy an samu ƴa mace yanzu da yamman nan".
Wani irin ajiyan zuciya mai sanyi Ummey ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah yau kam zanyi bacci hankali na konce Shatuna ta haihu lfy".
Murmushi Inna Amarya tayi tare da cewa.
"Wlh kuwa kai Alhamdulillah Metai fi haka daÉ—i kaji kawai É—an ka ya haihu lfy".
"Wlh kuwa fa". Cewar Bappa.
Sai kuma suka juyo suna kallon Junainah dake tsalle tana cewa.
"Alhamdulillah Hamma Jabeer kace dani takeyin kama?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Junainah".
Cikin dariya tace.
"Allah shi ƙara dama kullum Addana sai tace wai ta fini kyau wai inada dogon bakin kwaɗayi, ni kuma kullum ince Allah yasa ta haifi irina ai zata dena cemin mummunan".
Dariya yayi sosai kana yace.
"Toh gobe dai zaki zo mana ko?".
Da sauri tace.
"Eh zanzo Bappa na da Ummey ma zasu zo".
Katse kiran tayi kana ta miƙawa Bappa wayar.
Shi kuwa kiran Abboi yayi ya kara wayar a kunne tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
"Wa alaikassalam".
"Barka da dare Abboi".
"Barka dai Bappa Shatu." Abboi yace yana murmushi tare da kallon Dedde dake gefensa.
Cikin jin daÉ—i Bappa yace.
"Alhamdulillah yau Shatu na ta hau matakin uwa ta sauƙa lfy mun samu ɗiya mace".
Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da jin daÉ—i Abboi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kai yau naji labari mai daÉ—i masha Allah. Kace lallai zuwa Nigeria ya kamani".
Da sauri Bappa yace.
"Sosai ma kuwa, yanzu dai su waye zasu fara zuwa".
Da sauri yace.
"Khadijah da Amina ƙanwar Deddena Shatun, dama nayi mgnar da mijinta tun kwanaki to yanzu kuwa zan kirashi in sanar mishi anfa yi haihuwar ba mamaki gobe ko jibi su taho da safe zuwa gidan naka.
Kaga da azahar sai su wuce masarautar da iyalin taka".
Cikin gamsuwa Bappa yace eh hakan yayi.
Yana katse kiran yayiwa Ummey bayani cikin gamsuwa tace.
"Eh hakan yayi amman in Amina da Khadijah sun zo suje da Junainah ni sai bayan suna sai inje ko".
Cikin gamsuwa yace.
"Eh amman bayan suna da kwana É—aya zakije in anyi suna kamar yau sai gebe kije ko".
"Eh hakanma yayi". Tace cikin jin daÉ—i.
Shi kuwa Abboi a ya juyo ya kalli Dedde ya mata bayani.
Sosai ta shiga cikin farin ciki a take ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Nan ta gaya Khadijah ta fara shiri Addanta ta haifu.
A masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya a daren labarin haihuwar Shatu ya karaɗe ko ina lungu da saƙo na masarautar.
Riskar wannan lbrin a kumnunwan Magauta yayi masifar tada musu hankali.
Hajia Mama kuwa a dare cikin masifar tashin hankali ta wuce gidan bokanta.
Tana shiga tace.
"Meyasa ne wai ku bokaye babu wasu maƙaryata a duniya sama daku, ya mukayi da kai da shaiɗanun makaranka maƙaryata. Shin ba cewa sukayi randa aka haifi yarinyar a wurin yanke cibiya zasu kashe min itaba".
Cikin wani irin masifeffen razana ta daka tsalle tayi baya, sabida wani irin razanenne tsawa da bokan ya daka mata da ƙarfi.
Cikin É—aga amo yace.
"Ke tafi daga can waya isa ya cutar da wanda Allah ya kare, dama ai na gaya miki babu abinda da zai samu cikin nan sai al'khairi.
Amma da yake ke tinkiyace ƙidahuma kikazo kina min ihu a kai in zaki iya cutar da itan ke kije ki gwada mana".
Cikin tashin hankali gano tayi asarar kuÉ—aÉ—enta a banza ta juya ta fita tana cewa.
"Tabbas sai na kashe yar nan babu shakka bazata rayuba".
Shi dai boka tsaki yaja.
Ita kuma ta juyo ta dawo hankali a masifar tashe.
Shi kuwa Sheykh yana gama mgn da Bappa DSS É—insu ya kira.
Cikin hikima da iya sarrafa harshe yace.
"Sir naga wasu yaran da akayi nasarar kamasu da laifin kinnafin ko?".
Jim kaÉ—an yayi tare da cewa.
"Eh yaran fulani masu kiwo ko?".
Da sauri yace.
"Eh su waÉ—anda akasa suka amsa laifin da ba nasuba akan dole."
Da sauri yace.
"A a kamar yaya laifin da ba nasuba?".
Cikin nutsawa ya gyara zamanshi kana yayi mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi É—azu.
Cike da al'hini irin yanayin nan na ba'a mugun sarki sai mugun bafade ogan nashi yace.
"Kai Malam ni bansan da zancen nanba, kawai nasan kotu ta bada beli babu batun a nemo wasu a basu laifin da ba nasuba".
Da sauri Sheykh yace.
"Ni nasan baka saniba dan na yarda da adalci ka yanzu me abun yi a kan lamarin yaran nan?".
Cikin takaicin yadda wasu jami'an tsaron kasar nan suka zama azzalumai yace.
"Dole zamu kai zancen kotu ayi bayani a gaban al'ƙali a kawo Sulaiman ya bada shaida, da kuma sauran ma zauna magarƙamar".
Cikin wani irin jin daÉ—i sanin muddin mgnar taje kotu.
Komai zai iya dai-dai yace.
"To ka taimaka musu a meda case É—in yaran zuwa kotu".
Cikin nitsuwa yace.
"Toh ba matsala".
Suna gama wayar kuwa ya fara bincikan lmrin a afaren ya turawa wani al'ƙali rahoton.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin Shatu.
Tuni tayi wani baccin gajiya.
Ummi na kwance gefenta.
A hankali yace.
"Ummi bakuyi bacci bako?".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To ita dai mai jego tayi sai nida ƙawar tawane muke hira".
Murmushi yayi kana ya matso.
Miƙawa mishi yar tayi, amsa yayi, ya zauna a bakin gado gefen Shatu.
Addu'o'in ya farayi yana tofa mata.
Kana a hankali ya kalli Shatu data buÉ—e ido a hankali tana kallonsu.
fuskar yarinyar ya kalla yadda taketa wawure-wawuren hannunta.
Cikin nitsuwa yace.
"Ummi yunwa nefa ya hanata bacci".
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Ita kuwa Ummi da sauri tace.
"Yauwa tunda ta tashi ta bata maman ta tsotsa".
Kai ya gyaÉ—a kana yasa hannunshi ya kamo na Shatu ta tashi zaune.
ÆŠaura mata yar yayi bisa cinyarta, kana yace.
"Bata Baloon É—in tasha".
Cikin É—an yamutsa fuska tace.
"Daga yanzu?".
Da sauri yace.
"Eh".
Ya ƙare mgnar yana tattaro rigarta yayi sama dashi, tare da ɗan ɗago kan Baby ya saita bakinta da nimple ɗin ya manna mata.
Ai kuwa da ƙarfinta ta damƙi nimple ɗin.
Wani irin zillo Shatu tai tare da yarfa hannun cikin sakin ƴar ƙara tace.
"Wayyo Allah na Yah Sheykh zafi".
Da sauri ya saki dariyar mugunta.
Hakama Ummi dariyar suke mata.
Ita kuwa cikin kunya ta ɗan sunkuyo tana kallon yadda ƴar taketa zuƙam nonon da har yanzu bai tsastsafo da ruwaba.
Haka nan taji wani irin son yarinyar yana shiga ta.
Tsawon 5 minute tana tsotsar bakin nimple É—in ta,
wanda saida yayi ja yayi tsami a hankali tace.
"Zafi wlh zata cinye min nimple".
Murmushi yayi tare da lakace hancinta kana ya janye kan yarinyar.
Ya kwantar da ita, ai kuwa gajiya da tsotson yasa tayi bacci.
Ita kuma Shatu meda breast É—inta cikin riga tayi kana ta koma ta konta.
Sunkuyowa yayi kansu yayi musu addu'a.
Kana ya juya ya fita yana cewa Ummi.
"Sai da safe".
Allah ya bamu al'khairi tace.
Amin yace yana fita.
Yana komawa É—auki shi yayi shirin bacci kana ya kira Haroon da ibrahima sukayi hira sosai cikin farin cikin.
Daga nan ya kwanta.
Washe gari da safe.
Gimbiya Saudatu ce zaune a falon Shatu.
A hankali ta fito ruggume da yar a hannunta sunyi kyau sosai cikin shigar tasu.
Especially Babyn da aka shiryata cikin wasu kayan sanyi masu taushi red color and white masu masifar kyau da taushi, tayi lib a ciki.
A hankali ta kalli Shatu dake miƙo mata ƴar amsa tayi tare da cewa.
"Masha Allah, Æ´arinya kam kekkyawan sai dai Allah yasa kada ta gaji Rashin kunyar uwarta da ubanta".
Sheykh dake shigowa ne yace.
"Ai kuwa zata gada dan kyan É—an ya gaji iyayensa".
Cikin watsa mishi harara tace.
"Kai matarka ta haihu ka girmama bazaka bar yiwa manya rashin kunya bane wai?".
Da sauri ta juyo ta kalli Shatu dake cewa.
"Toh ai kema baki bar rashin kunyarba bare mu".
Cikin ta kaici tace.
"To uwar fitsara ke kiji da jegon ma mana tukun".
Murmushi tayi tare dasa hannun ta amshi babyn da take miƙo mata tare da cewa.
"Allah ya raya".
Karo na forko a rayuwar Sheykh da yaji Gimbiya Saudatu ta mishi addu'a ko mgn mai kyau.
Cikin jin daÉ—i yace.
"Amin ngd".
Tsaki taja tare da watsa musu harara ta fita.
Murmushi yayi mai sauti ƙana ya iso gareta.
Ya ruggumeta ita da Babyn cikin raÉ—a yace.
"Ana Uhubbuk ya habibi Da'iman".
Murmushi tayi dan bata gane da ita yakeba, a zatonta da yar tasu yakeyi.
Shi kuwa ganin bata gane bane sai ya share tare da cewa.
"ÆŠazu nazo kuna bacci".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Ummi ta gaya min".
Da sauri ya janye jikinsa gareta, jin Muryar Mom Maman Imran wacce itace matar Abbansu ta uku.
A daƙile ya amsa sallamar tata, sai ya kuma saki fuskarsa ganin harda Abbanshi da cingam ɗinsa amaryarsa kenan.
Bayan su zauna ne Shatu ta miƙa musu ƴar ɗaya bayan ɗaya, cikin murmushin Mom tace.
"Masha Allah, tana kama da kakarta".
Amaryar Abban ta miƙawa amsa tayi tare da cewa.
"Kekkyawar Baby Allah ya raya amaryar Habibullah".
Da sauri Abba yace.
"Uwar gida dai, ai kece amarya kam".
Kauda fuska Sheykh yayi kamar baya wurin.
Haka dai sukayi musu Barka suka tafi.
Haka kuma mata da maza bayi da hadimai keta yiwa Sheykh Barka a duk sanda ya gilma cikin masarautar.